Labarai

Yanzu-yanzu: DSS ta baiwa NNPC da dillalan mai wa’adin sa’o’i 48 su kawo karshen karancin mai

Yanzu-yanzu: DSS ta baiwa NNPC da dillalan mai wa’adin sa’o’i 48 su kawo karshen karancin mai

 

 

 

Da yammacin Alhamis ɗin nan ne hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta baiwa kamfanin man fetur na kasa (NNPC) da dillalan mai wa’adin sa’o’i 48 su samar da man fetur a fadin kasar nan.

 

Kakakin Hukumar, Peter Afunanya, ne ya bayar da wannan sanarwar a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ofishin hukumar da ke Abuja bayan wata ganawar sirri da su ka yi da masu ruwa da tsaki a harkar man fetur a yau Alhamis.

 

Afunanya ya bayyana cewa kamfanin na NNPC ya tabbatar a yayin taron cewa ya na da isasshen man da za isa yi wa ‘yan Nijeriya hidima a lokacin kakar Yuletide da kuma bayanta.

 

Ya ce an sanya duk wasu umarnin DSS a kan gargadi kuma za su fara aiki don gano masu kunnen kashi tare da hukunta su.

 

Afunanya ya kuma koka da kalubalen karancin man fetur, inda ya ce lamarin ya dauki wata gaɓa da za ta iya kawo illa ga tsaron kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button