BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 36

Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

36

………Burin Mommy kawai ya kalleta amma yaƙiyin hakan. Tsahon minti guda baice komai ba yana satar kallon fuskokinsu ta gefen idanu. Tabbas ya hango tashin hankali kala-kala musamman a fuskar Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima da Fadwa, ya haɗiye busashen yawu da ƙyar tare da tattaro dukan ƙwarin gwiwarsa da jarumtarsa. Cikin dakewa ya ce, “Baba bani da ja akan hukuncinku”.
       “Kan ubanka Al-Mustapha!!”.
  Mommy ta faɗa cikin suɓutar baki, Murmushi Abba da Abie suka saki kusan a tare, hakama aunty Mimi da Mom da aunty Amarya sai da sukai kananun murmushi. Ɗayan yayanta da suke cema Yaya Kamil ya harareta, a kausashe yace, “Nafisa! Dama kina buƙatar ya bijirema iyayensa ne? A matsayinsu na mahaifa a garesa su zartar da hukunci ki nunama duniya k baki bama ɗanki tarbiyya ba saboda wani banzan tunaninki da hujjojinki? Karna sake jin bakinki a wajen nan, in ba hakaba ranki zaifi haka ɓaci billahillazi!!”.
        Dole tai shiru saboda a maganar Yaya Kamil ɗin babu wasa sam. Baba Ibrahim ya sake maida hankalinsa ga Shareff. “Ka bamu amsa ne a dunƙule Shareff, kana nufin ka amsa auren kenan?”.
       Sai da ya ɗan saci kallon Mommy ta gefen ido, tako zuba masa ido cikin matsanancin ɓacin rai, janye idanunsa yayi ya maida kan Daddy shima ya tsume kamar fuskar tasa zatai aman wuta.
     “Shareff kai muke saurare, in har a ranka kanajin auren nan cutuwane a gareku ka saki yarinyar nan tun yanzu anan karka saka ku a wani halin da zai wargaza zuminci”.
     A hankali ya girgiza kansa dake rissine a ƙasa. “Baba ku gafarceni bazan iya sakinta ba tunda an ɗaura….”
      Kukan da Anaam ta fashe da shi ya hana Gwaggo data ɗauki sallami tana tafa hannaye ƙarasawa, hakama Mommy da Gwaggo Halima da suka zaburo. Fadwa ma kuka ta saki mai ƙarfi yayin da Aunty Mimi da Mom da Abba suka saki wata nannauyar ajiyar zuciya, Abie ko murmushi ya saki, shi ko Daddy ya ɗan lumshe idanu. Mamie dai kanta a ƙasa yake babu mai iya gane yanayinta. Albarka su Baba Ibrahim suka shiga sanya masa da suma murmushin ya ziyarci fuskokin su, hakan ya ƙara tunzura kukan Anam da Fadwa….
      “Nidai bana Son sa baba, akwai wanda naima alƙawari zan aura nima, kuma shi nake so!!”. Furucin Anam cikin matsanancin kuka ya daki kunnuwan kowa dake a falon. Cikin sauri da zaburowa Mommy tace, “Shima ai ba son naki yake ba, shegiyar yarinya mai kama da ifiratan aljanu. Yaya ai kaga abinda nake gudun masa tun farko, mizaiyi da wannan mara tarbiyyar yarinyar har tana wani iƙirarin ba son sa take ba fitsararriya…..”
     Hayaniyace ta nema sake kaurewa a falon, yayinda Anam ke rusa uban kuka ita akwai wanda take so. Tsawar da Abie ya daka mata ce ta saka gaba ɗaya hayaniyar kukan Fadwa da Hargowar Mommy data Gwaggo yin tsitt. Anam ta maƙure jikin Aunty Mimi tana sake fashewa da kuka. Baba Ibrahim ne ya kalla Abie cikin murmushi, kansa ya girgiza masa cikin dattako. “Ayi haƙuri Usmanu abita a hankali sai a samu masalaha sahihiya. Tsanani baya kai kowa ga hanyar nasara. Juwairiyya zonan kinji”.
       Da taimakon aunty Mimi ta mike taje gabansa, kusa da ƙafafunsa ya nuna mata, ta zauna tana shashshekar kuka da sharɓar hawaye da gyalen data rufe har fuskarta. Cikin lallashi yace, “Kukan ya isa haka to, maza share hawayrnki”.  Da ƙyar ta iya danne kukan, sai dai hawayen basu bar zirara ba.
Cikin lallashi yace, “Faɗa min wa kike so?”.
Kai tsaye tace, “Muzaffar!”.
“Miyasa shi Shareffuddeen baƙya son shi?”.
Shiru tai ta kasa magana, ya ƙara maimaita mata tambayar.
“Kawai Baba”.
“Ai shi mutum ba’a ƙinsa kawai Juwairiyya. Amma zan baki wata dama da kuma alfarma kin yarda?”.
Cikin share hawaye ta jinjina masa kanta. Yay murmushi irin nasu na manya masu basira.
“Ina so kimin alfarmar yarda a kaiki gidan Shareffuddeen. Daga nan zuwa wata uku in har baki samu wani farin cikin zama da shi ba, kizo ki sanar min, ni kuma na miki alƙawarin da kaina zan saka shi ya sallama miki”.
Karon farko ta ɗago ta kallesa. Cike da tabbatarwa ya jinjina mata kansa yana murmushi. Ta kai dubanta ga Shareff, cikin sa’a kuwa suka haɗa ido. Wani shegen kallo da taima fassara dana tsana ta hango cikin idanun nasa, sai taji ƙwarin gwiwar cin nasarar shawarar baba ibrahim, dan kuwa ta tabbatar babu wani farin ciki da zata samu daga Shareff ɗin musamman idan ta auna irin tsanar da yay mata a rayuwa. Idan haka ne gara ta amince kodan goge laifinta da su Abie zasu iya gani, cikar wata uku kuma dai-dai da kammala Serves ɗinta kenan……
“Baki ce komai ba”.
Baba ibrahim ya katse mata tunani.
“Baba na amince”.
Murmushi ya saki mai ƙayatarwa, hakama abie da Abbah da Daddy duk sai da suka saki ajiyar zuciya. Yayinda Mommy tai ƙwafa sai dai babu damar cewa wani abu.. Baba Ibrahim ya sake ƙara musu nasiha baki ɗaya musamman Gwaggo dake a matsayin uwa garesu su duka a wajen. Hakama Mommy data hau dokin zuciya da yasan bazata taɓa tanƙwasuwa ta sauƙi ba. Itama dai Fadwa da Gwaggo Halima sun sami nasu rabon musamman ma Fadwa da yaketa lallashi dan yasan an mata laifi. Suma dai su Daddyn ya musu nasihar ya kuma ƙara bama kowa haƙuri da fatan komai ya wuce sannan yay addu’a taron ya tashi dan dare ya farayi…..

          ★★Washe gari an tashi ne mafi yawan rayuwuka a ɓace, ga amaryar Maheer ta iso tun daren jiya, tana a sashen Mom kamar yanda Daddy ya sharɗanta. Aunty Halima dai tun daren jiya tabar gidan tare da Fadwa, acewarta dai su Daddy basa ƙaunarta babu ita babu su, Fadwa ma tabar gidan Shareff kenan sai dai ya biyota da takardarta. Komai babu wanda yace mata a cikinsu, sai Gwaggo dake faman matsar ƙwalla tana faɗar maganganu. A haka dai babu daɗin rai akai walima washe gari dan dama ango Maheer shi bai yarda da wani event ko ɗaya ba, butsutsunsa yasa Mommy haƙura duk da taso a sha shagali tamkar bikin Shareff da Fadwa.
       Shareff ma dai tun a daren ya koma can gidansa tare da Khaleel da Maheer ɗin da suka kwana da shi a can saboda yanayin jikinsa daba gama daidaita yay ba. Itama dai Anam bata kwana da lafiya ba dan tunda sassafe ma sai da Abie ya kaita asibiti da kansa aka bata gado. Dan haka har yamma tana can tare da Aunty Mimi da Abie ɗin, sai su Mom da su Daddy da sukaje daga baya dubata. Wannan ya kawo ƙaracin armashin buɗar kai da akai na amaryar Maheer, bayan sallar la’asar danginta da wasu a dangin Mom sukai mata rakkiya gidan mijinta. Gida yayi ƙyau dan Maheer ma yayi ƙoƙari sai sambarka. Sannan iyayen amarya ma sunyi nasu ƙoƙarin dan kun san dai Mom dama duk inda take na masu manda ne. (Tana bala’in son huɗɗa da masu kuɗi a gidan sanyi????).
         Tun a ranar mafi yawan baƙi suka kauce dan uwar bikin a birkice take. Tako’ina Mommy ɗin ta birkicema kowa. Gida yayi lafiya, baƙin da suka rage kalilanne, Hakan yasa koda aka sallamo su Anam daga asibiti sanda suka shigo gidan tsitt yake.

      Washe garin data kasance lahadi sai ga mahaifin Fadwa har gida ya maido Fadwa, babu ragi yay mata tatas a gaban su Daddy ita da Mommy. Fafir kuma yaƙi sauraren zantukan Gwaggo duk da uwa take a garesa. Wannan dattako daya nuna ya matuƙar faranta ran kowa a gidan ciki harda Shareff da aka sashi zuwa gidan. Daga ƙarshe kuma ya bisu da nasihar zaman haƙuri dana riƙe junansu domin samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Bayan wucewarsa su Daddy suka sake zama da Shareff, sun basa umarnin ƙarasa abinda ya rage masa dan nan da sati ɗaya amarya zata tare ɗakinta. Yaso yace suɗan ƙara masa amma baiga wannan damar a fuskokinsu ba dan umarni suka bashi ba shawara ba. Daddy kuma ya turkesa a wajen yace ya biyasa kuɗin sadaki dan shine ya ranta aka biya a waccan ranar. Dole yayma Daddy transfer ɗin kuɗinsa take a wajen sannan ya barsa ya tafi.
       Ƙin shiga wajen Mommy yayi dan wasan ɓuya yake da ita tun ranar, ya aika Aysha ta kira masa Fadwa tazo su wuce. Amma sai Mommy tace a faɗa masa Fadwan ta ƙarfi ce idan yanada ƙarfin yazo ya ƙwata. Murmushi kawai yayi sanda Aysha ta zo masa da amsa, batare da yace komaiba ya shiga motarsa ya fice a gidan dan gwara wannan wasan ɓera da magen da yake da Mommy ɗin akan tunkararta face to face a yanzun.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button