AMANA TA CE Page 41 to 50

sai a lokacin taji muryan xarah na cewa munay kika bar wan nan mai kama da Aljanan, take miki rashin kunya, daga hannun munay ta kai mata mari, auta ko cikin zafin nama ta rike hannun, ido munay ta zaro sai a lokacin ma ta lura da kayan jikin ta, aiko take ranta ya kara baci tayi kam ta da niyar duka aiko auta ta damko ta, sai lokacin karfi ya zo mata nan ta shake munay, sai ga idonta ya fito alamar tafiya taji shaka, xahrah da kaltum suna ganin haka, sukayi kan auta zasu fara jibgarta sai ka ahyan ya shigo ko sallama babu, yana yar wakansa, ganin abunda ke faruwa, yayi kansu kai!! meye haka? Mts ya fisgo xahra da kaltum, kafin ya kwace munay, sai haki takeyi, auta ko jin wuyanta ya bushe ta wuce kitchen ta dauko faro mai sanyi, tana takun isa, ta zo falo ta taras yana fada wa munay, suna hada ido ta yi mata gwalo, nan munay takara harzuka sosai, kamar zata fasa ihu.
Auta bata gama gyara zama ba, taji tsayuwar motar Ammar da sauri tayi mike don bata son ahyan ya tafi ya barsu, zasu iya mata rashin mutunci, kitchen taje ta dibi rabin girki da tayi wa munay, duk da tasan ya masa yawa, amma don ta kularta, ta diba da yawa sosai, tazo ta wuce su tayi dakin ammar lokacin yana cire ta kalmi, da sallama ta shiga, kalonta ya tsaya yi don tayi kyau sosai, bai san har ta iso gefensa ba, sam ya shagala da kalonta sai da ta hada hannunta tana tafawa, kafin yayi firgit ya sauke wani ajiyar hrt, sannu da zuwa ta masa, ya amsa da sakin fuska, kalonta yayi, ya ce my sis gsky na iya zabe, don kayan nan ba karamin kyau suka miki ba, murmushi tayi tace na gode Allah ya kara budi, ameen ya ce barin watsa ruwa, tana zaune ya shiga dakinsa, sai da ya dau 10 minutes, kafin ya fito cikin kaya maras nauyi, abincin ta zuba masa, nan kamshi ya fara dukan hancinsa, aiko bai tsaya wata2ba ya fara diban abinci yana santi, sai da yaci yayi rabi sanna ya sha ruwa, yace Alhamdulilah.
Hira suka rinkayi yana bata dariya sai kyal2lewa takeyi, sai da aka kira sallah magriba kafin ta masa sai da safe, ta nufi cikin gd, sai da ta dan leka ta ga basa nan, ta nufi kitchen da hanzari ta ajiye cooler ta nufi dakinta, key ta saka tayi sallah haka har akayi isha’i ta kwanta.
Da safe ta hada breakfast ta dibi nata ta koma daki, bayan ta karya ta koma daki, bata fito ba sai karfe daya ta daura na rana lokacin munay na bacci, tana gamawa ta diba ta koma daki, bayan taci wanka tayi ta zauna tana duba littafin adu’ah. Sai kusan uku taji tashin mota tasan munay ce, tana tabbatar da ta bar gidan ta fito ta nufi kitchen ta gyara ta kama wasu ayukan.
Su mum sun isa sakoto lfy, tayi duk abunda ya kaita, da taso su kwana 2 amma sai aka mata kiran gagawa dole suka shirya don ta jirgi zasu dawo yau din nan 5 jirginsu zai sauka.
Auta ko han kali kwance take aikin ta, har da yar waka ta, ahyan ne ya shigo gd ya leka daki munay yaga bata nan, murna fal ransa ya nufi dakinsa ruwa ya watsa kafin ya canza kaya zuwa boxer da singlet ya nufi dakin auta, nan yaga fata dawo dakin ba, buya yayi a toilet.
Auta na gama aikinta ta shigo dakinta, bata rufe kofa ba turawa tayi don zata koma jimawa kadan ta dauko zobon da taha kafin yayi sanyi, kan gado ta fada, bata wani dade ba ta fara gyan2di, a hankali ahyan ya bude kofar, lokacin bacci barawo ya dauketa, kusa da ita yazo nan ya fara mata wani irin salon, “(ido na zaro ina rokon Allah ya kubutar da wannan baiwa daga hannun wan nan maras tausayin)”.
Auta kamar daga sama taji ana mata wasu abun da ya basa tunaninta, a hankali ta soma bude ido ganin ahyan yasa tasoma kokawan kwace kanta, amma ina yafi karfinta, sai kokarin rabata da kayanta yakeyi, da kyar ya samu ya yaga rigan jikinta, ganin daga ita sai bra yasa ta ja da baya ga hawaye da ke zuba, shiko sai wani dariyan mugunta yakeyi, haka har suka iso bangon dakin, ya nufota gadan2 tasaki wani razanane kara,
Wanda yayi dai2da shiigowan Ammar gidan, bai karasa parking ba sai ga su hajia mamu sun iso, auta ganin ba wanda ya jita yasa takara takarkarwa iya karfinta tasaki ihu ta fadi kasa sumamiya, shiko hakan baisa ya ci gaba da abunda yayi niyar yi ba.
aiko dukansu da ammar da su hajiya bansan wanda yafi wani gudun shiga ba, nima ina ganin haka na bisu da mugun dugu har sai da wayata ta fadi.
Mai karatu ban samu daman daukar wayata ba, nabisu don inji gurmin da za a toya, kar ya wuce ni, in na dauko zakujini a next page….lol…
Taku a kulum mai kaunarku Yar Mutan Kardam
®WISDOM
HAUSA WRITER’S
Rash Kardam
[7:56PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Da gudu suka nufi cikin gidan, duk a rude suke, ammar garin hawa stairs ya fuge kafarsa, nan take sai ga jini ya soma fita, amma ko ta kansa bai bi ba, yana isa yaga kofar arufe yayi zaton da key ne ajiki, komawa yayi da baya yayi wani duka ma dakin, sai yaga ko motsi baiyi ba kafin yasake naushin, H Mamu ta zo da sauri ta murda kofar sai gashi ya budu, duka suka shiga dakin, abunda suka gani ne yasa su suman tsaye, ammar da gudu ya kaima ahyan damka wanda shi gaba daya baya cikin hayyacinsa yana kokarin kire ma auta skirt yakeyi, ammar ya shake wiyarsa ya makasa da garu take kansa yasoma zubda jini, ran hajiya mamu ya baci idonta ya rufe, ga hawaye zai zuba yakeyi dai2 nan munay ta shigo ganin abunda ammar yake ma bros dinta yasa tafara dukansa wani naushin da ya mata sai da ta fadi gebe dan azaba kasa kuka tayi, hajiya mamu tazo tafara taya ammar dukan ahyan, sai da suka ga baya ko motsin, suka kulyalesa, kausar kam kuka take kamar ranta zai fita, ammar da gudu ya dauki auta yayi waje da ita wanda marabanta da gawa kadanne, kausar da H Mamu suka rufa masa baya, akabar munay da bros sai kuka take tayi.
Ni’IMA CLINIC, ya nufa gudu yakei kamar zai tashi sama har sai da yan hanjin cikin kausar suka kama disko, suna isa emergency suka nufa, da sauri nurses suka karfe ta suka shiga da ita, ba a dade ba na hango Mrs Adul cikin shigan kayan likita, tayi emergency, ammar ko kasa zaune yayi sai zagaya wa yakeyi, yana hawaye nan wani bakin ciki ya tokaresa, bai san lokacin da ya buga hannunsa a garu. Har sai da hannu tayi kass, kausar duk ta tsure da lamarinsa daman haka yake da zuciya, (ni rash nace hmm).
Can Mrs Abdul ta fito fiskan nan baya bo ba fallasa da sauri Ammar yayi gunta, Dr ya jikintan? Ta tashi kuwa? Atare ya jero mata wayan nan tambayan, ajiyar zuciya tayi kafin tace Alhamdulilah, bata tashiba amma zamu ce da sauki, amma meye ya razana ta haka don tayi dogon suma, amma muna sa ran farfadowanta a kowani lokaci, aziyar hrt ammar yayi, Mrs Abdul taci gaba da cewa, zamu kaita dakin hutu ba kuma mai zuwa kusa da ita don bata son hayaniya, suna tsaye akazo aka wuce da ita special room, hajiya mamu kam duk takasa cewa komai wai ace ahyan ne ya aikata haka, ina tarbiyan da tabasa duk yasa kafa yayi watsi da shi, in sonta yakeyi, mai yasa bazai fada mata, sai ayi musu aure ba? Dole in gwada wa ahyan bacin raina dole nasan abin yi, kausar kam kasa hada ido tayi da ammar don tana jin tsanar ahyan amma sun gode ma Allah da Allah yasa bai kita mata haddi ba.