Lu’u Lu’u 17

A dak’ile fuska a had’e Ayam tace “Ai cewa na yi ki d’auko min, ba wai ki fad’a min inda suke ba.”
Da sauri ta juya ta fita ta shiga d’akin da aka sauke Ayam d’in, ita kuma abincin ta d’auka ta fara ba wa Kossam wacce k’arara zaka fahimci fuskarta bata cikin yanayin nan na dumkum data saba.
Duk da ta ji an bud’e k’ofar bai sa ta juyo ba dan tunanin ta hadimar ce, amma sai ji tayi an ce “Uban wa ya baki damar bata abinci?”
A gadarance kamar wacce ta tashi da ciwon wuya haka ta juyo ta kalli Joyran wacce tashin hankali ya bayyana a gareta k’arara, d’auke kan ta tayi ka rantse bata san da mutum a wurin ba tace “Kin ci sa’a d’aya an ce yar uwar madam ce ke, ba dan haka ba da na ce *uban ki*.”
Kossam kan ta saida mamaki ya bayyana a fuskarta, uwa uba kuma hadimar nan data shigo d’auke da kayan da Ayam d’in ta buk’ata, haka ma Joyran kusan jiri ta ji zai d’ebeta, yanda ta zazzaro ido ta k’ura mata su kamar wacce ke kallon gawa na motsi, sam mantawa tayi da a inda take me kuma take yi saida ta tsinkayi muryar Ayam a kunnenta tana fad’in “Ki daure ki k’ara kad’an madam, please.”
Da sauri ta zabura kamar wacce aka mara ta k’arasa shigowa d’akin, cikin tashin hankali da neman bala’i ta bige farantin abincin tana fad’in “Ke har kin isa? Wacece ke da zak…”
D’aga mata hannu Ayam tayi ta d’ora yatsa a labb’anta tace “Shiiiii!”
Kallon fuskar Joyran d’in tayi tace “Haka kawai na tsani tsawa, na tsani a d’aga min murya musamman a k’ok’on kai na, na rlk’oki kar ki jawowa kan ki mummunar safiya ta hanyar tak’alata rikici, ina so na kafa kyakyawan tarihi a gidan nan kafin na barshi.”
Juyawa tayi ta kalli hadimar tace “Kawo kayan ki taimaka min a saka mata.”
A tsorace cikeda girmama lamarinta hadimar ta k’araso jikinta har rawa yake ta aje kayan kan gado, a tsawace Joy ta kalli hadimar tace “Ke! Idan baki bar nan ba sai na tozartaki.”
Da kallo Ayam ta bi hadimar data fita a rikice ta rasa me zatayi, zagayawa tayi ta d’auki kayan ta warware ta tako zata koma inda take, cikin jin haushi Joy ta fizge kayan ta jefar a k’asa tace “Fita a nan malama, sannan ki ji da kyau.”
Tayi maganar tana nuna Ayam da yatsa, d’orawa tayi da “Daga yau sai yau karko sake shigowa d’akin nan bare ki k’araso gareta, babu ruwanki da abinda ya shafeta, idan kuma kika sake to ki sani ki ma zaki tsinci kanki a mugun hali.”
A take, a bazata, kamar saukar aradu Ayam ta rulgume hannaye tana fad’in “Kamar yanda kika jefata kenan?”
Wani mummunan fad’uwa ne gabanta yayi ta rarako ido ta kalleta, take wani gumi ya shiga tsatsafo mata a goshinta zuwa wuya, tsatsareta tayi da ido ta sake gyara tsyuwarta tace “Ko kuma zaki jefani fiye da halin da kika sakata ne duk tsawon shekarun nan?”
Kame kame ta fara tana jujjuya kai tace “Ke ke..me kike…fad’a ne wai haka ? Baki da hankali da alama.”
Tana fad’a ta rab’ata zata fita a d’akin, ta kai daf da k’ofa kuma sarki Musail ya shigo daidai da Ayam tace “Ina da hankali, amma ki sani a cikin haukana zan bankad’o sirrin da kika jima kina b’oyewa ta hanyar wasar kura da rayuwar mutuniyar kirki.”
Rud’ewa Joy tayi ta kalli sarki Musail dake binsu da kallon tuhuma yana son sanin me ke faruwa, fashewa tayi da kukan makirci tana fad’in” Wannan ma ai tozartani kike yi, yar uwata ce fa, ya kike tunanin da hannu na a cikin rashin lafiyarta?”
Shigowa yayi yana kallon Ayam yace” Gimbiya Zafeera, me yake faruwa ne? Tana neman b’ata miki rai ne?”
Kallonshi Joy tayi da mamaki wato bai ma damu da damuwarta ba bare kukan da take, figaggiyar ma yake tambayar ko ana neman b’ata mata rai ne?
Ayam kam murmushin yak’e tayi tace” A’a ranka shi dad’e, ba komai muna magana ne.”
Kallon Joy yayi yace” Ki koma b’angaren ki, sannan ki kiyaye b’acin ranta, dan zan iya yin komai a kan ta.”
Kallon shi Joy tayi ta k’ara kallonshi sau ba adadi, sai kawai ta juya ta fita dan bata san me zata fad’a ba, tana fita kuma Umad na shigowa har ma yana gaisheta amma sai ya fahimci bata cikin hayyacinta, yana shigowa ciki ya zuba idonshi akan ta, duk da rigar bata fito da jikinta ba face k’afafunta da kuma fuska sai tafukan hannu, amma sai ya ji ya tsani tsayuwarta haka kuma a gaban mahaifinshi.
Bai kula da sarki Wudar dake tsaye ba haka mahaifiyarshi da idonta ke kan shi, fuskarsa a had’e ya kalleta yace “Malama ki je d’akinki ana kai miki kaya yanzu.”
Abun al’ajabi da mamaki daya kusan saka sarki Wudar suman tsaye shi ne yanda Ayam ta jinjina kai alamar to ta kuma kama hanya ta fice, sai ya ji ya fara kokonto ko dai ba ita bace, dan wacce aka fad’a fa komai matsayinka ita ce zata baka umarni kuma kayi jikinka na b’ari, hasalima ita waccen idonta kawai sun isa su saka mai aurenta durk’usawa kan gwiwoyinshi ya tambayi me take da buk’ata.
To amma kuma wannan ya d’anshi ya bata umarni haka ta bi? Duk da dai yasan waye Umad wajen tsare gida shi ma akwai izza da shan k’amshi inda a msarauta yake, to amma ai ta ta izzar ta dame ta shi ta shanye dan ita harda baiwa a lamarinta, uwa uba kuma sarautarta ta fi tashi k’arfi. (Idan har ta zama yanda kuke fad’a ai bata dace da zama matar kowa ba kenan, dole ta auri kan ta)
*Alhamdulillah*
The post Lu’u Lu’u 17 first appeared on 2gNovels.com.ng.
[ad_2]