Lu’u Lu’u 18
*18*
Saida ta fita ne Umad ya kula da yanda ya ga mahaifiyarshi, da sauri ya zagaya b’angaren ta ya rik’o hannunta yace “Mahaifiyata kin tashi lafiya?”
Zuba mata ido yayi amma kuma yana fahimtar amsar da take bashi ta tafukan hannayensu, shafa kan ta yayi da ya ga an gyara mata shi yau sannan yayi murmushi ya mik’e yace “Mah ina zuwa?”
Yana fad’a ya nufi fita a d’akin sai ya ji sarki Wudar ya rik’o hannunshi, juyowa yayi suka kalli juna, a tausashe sarkin yace “Kasan wacece ita da kake bata umarni haka?”
Wani malalacin murmushi yayi yace “Na sani Pa.”
Yana fad’a ya zage hannunshi a hankali ya fice a d’akin, kayan daya tanadar mata ya ba wa d’aya daga cikin hadiman gidan ta kai mata a d’akinta, inda shi kuma yana fitowa daga b’angaren sa ya ci karo da amininshi Haman ya zo gidan.
Had’e fuska Umad yayi sosai ya tako kamar mai tsorontaka k’asar ya tsaya gaban Haman d’in dake jingine a motarshi, Haman kam dake k’are masa kallo ya san akwai abinda had’e fuskar nan ke nufi, amma sai ya dake ya mik’o masa hannu yana murmushi yace “Barka aboki.”
Hannun Haman d’in ya bi da kallo kafin ya kalli fuskarshi, kawar da kai yayi sannan ya mik’a masa hannun yana d’an jinjina kai, gyara tsayuwa Haman yayi yace “Wai me yake damunka ne?”
A dak’ile yace “Me ka gani?”
Da yar raha yace “Na ga kayi wani iri ne ai, kamar ba kayi farin cikin gani na ba, da wata matsala ne?”
Tsakiyar k’wayar idon Haman d’in ya kalla fuskar nan a murtuke yace “Haman, bayan ni da kai bana jin akwai wani da yasan inda Zafeera take, ya akayi a sanda nake can kuma sai ga mutanen Baba na?”
Sunkuyar da kai yayi yana k’yakyabta ido da sauri kuma ya d’aga kai yace “Kamar ya? Zargi na kake Umad? Na d’auka kafi kowa sanin ba mu kad’ai muke nemanta a lokacin ba.”
Jinjina kai yayi yace “Hakane, amma kuma mu kad’ai muka san gakamaimai inda take a lokacin.”
Gyara tsayuwarshi yayi ya d’an sassauta had’ewar da ya ma fuskarshi yce “Haman, kasan aikinmu aikin sirri ne, kuma zamu kai ga gaci ne ta hanyar Zafeera, a duniya babu wanda ya san sirri na sama da kai, kar ka yarda na fara d’ora alamomin tambaya a kan ka, hakan zai ruguza maka yardar daka samu a wuri na.”
Juyawa yayi zai nufi babban b’angaren yace” Muje ka ci abinci, sarki zaiyi farin ciki da ganinka.”
Da kallo Haman ya rakashi har ya shige ciki ya dain ganinshi, wani sakaran murmushi ya saki akn labb’anshi ya furta” Zamu gani Umad, zamu gani.”
Da sauri ya shiga taka matakalar ya shiga b’angaren shi ma, sai kuma ya samu Umad da sarki Wudar da kuma Joy zaune wajen cin abinci ana zuba musu, k’arasawa yayi a ladabce ya gaishe da sarki sannan ya masa izinin zama kusa da shi, yana zama kuma sautin tkalmin Ayam suka sanar da su zuwanta.
Sarki Wudar da Haman da kuma Joy ne suka bi ta da kallo, rigar yadin dake jikinta mai santsi da kauri da k’yalli-k’yalli zai nuna maka yadin babba ne, saidai d’inki ne simple babu kwalliya, rigar har kasa ta sauka ta bak’in yadin sai hannayen da suka matseta sosai har zuwa gwiwar hannunta, daga k’irjinta ma zuwa ciki ya matseta sosai sai k’ugun da aka fito mata da tsarin surarshi sai tayi kyau sosai.
K’arasowa tayi ta ja kujera kusa da Umad ta zauna, tana neman cire takalmin k’afarta, dan gaskiya bata saba saka wannan takalmin ba ko can dama, wasu lokuta tana sakawa ne idan zata tafi wani shagali ko kuma wani shagalin makaranta, duk da shi ma kad’an ne a aikinta ta saka riga da wandonta mai yagewa a gwiwa ko cinya ta saka takalminta k’afa ciki ta d’auresu tamau da zariyarsu, shiyasa yanzun sai k’afafunta suka fara ciwo saboda sakawar da tayi jiya da kuma yanzu.
Da kallo ita ma ta bisu d’aya bayan d’aya kafin ta dire a kan sarki Wudar tace “Barkanku.”
Da wani irin alfaharin jin kasancewa gashi ga Zafeera ya jinjina kai ya saki murmushi yace “Barka gimbiya ta.”
D’an yak’e kawai ta masa ta maida hankalinta kan farantin ta, a hankali ta saci kallon Umad da shi ma lokacin yake kallonta, amma suna had’a ido yayi gaggawar d’auke na sa ya wani yatsina fuska irin ko menene d’in nan? D’auke kan ta tayi ita ma ta kalli Haman, da fara’a a fuskarta tace “Amma kai balarabe ne?”
Da sauri ya aje kofin daya d’auka mai ruwa zai sha ya tsura mata ido, cikin zaro ido yace “Wacece ke kuma? Me yasa kika ce haka?”
Murmushi tayi tace “Alamunka ne ya nuna, kuma da alama larabcin parsi kake, idan ba parsi ba to Ourdu.”
D’ora yatsanshi yayi a goshi yana rarraba ido, zufa zufa yake jin tana neman wankeshi daga zaune, to ta ya ma ta sani lokaci d’aya haka? Ko fa Umad bai san asalin waye shi ba, ya ita take neman saka shi a uku haka? Sarki Wudar kam wani farin ciki ne ya lullub’eshi har ya kalli Haman yace “Ita ce fa, Zafeera.”
Tsoron da Umad ya gani a tare da Haman d’in a lokacin sai ya sake jefa masa shakku a kan shi, tar tar yake kallonsa yana kuma karantarsa, cikin i’ina ya kalli Ayam yace “Ke ce dama? Sannu ko, ai mun jima muna nemanki.”
Murmushi kawai ta masa ta d’ibi abincin ta kai bakinta, sam ta k’i yarda ta kalli inda Joy take, saidai tar take kallonta ta k’asan ido, tana kuma ji a jikinta irin mugun kallon da take bin ta da shi, gyara zamanta tayi ta kyab’e fuska kamar yarinya ta kalli sarki Wudar tace “Am yallab’ai, zan iya tambayar wani abu?”
Da fara’a yace “Zaki iya mana gimbiya, ai ki saki ranki kiyi duk abinda kike so, nan gidanki ne kuma masarautarki.”
Gyara zamanta tayi tace “Yallab’ai dama ina so ne nasan dalilin zama na a nan? Ina so na koma gida saboda ina karatu a can.”
‘Yar dariya yayi yace “Karki damu gimbiya, ki d’an bani lokaci kad’an, zaki san me yasa kike zaune a nan.”
Bud’a baki tayi a hankali tace “Amma…”
Sai kuma ta jinjina kai kawai tace “Shikenan.”
Sake kallonshi tayi tace “Yallab’ai me yasa madam take gida kwance madadin asibiti?”
Muskutawa yayi hana ci gaba da cin abincinshi yace “Bana jin akwai asibitin da ban fita da Kossam ba, amma magana d’aya ce ba’a san dalilin ciwonta ba, da fari tana magana, amma a k’arshe sai ta zo ta daina, boka ya fad’a mana sammu ne kawai aka mata, amma kuma shi ma ya kasa karya wannan sihirin.”
Tarrr! Ta sauke idonta cikin na Joy da ita ma take kallonta kamar zata fasa ihu, girgiza kai kawai tayi tace” Zata samu sauk’i ita ma, amma da taimakonka.”
“Kamar ya?” Ya tambaya yana tsare ta da ido haka ma Umad dake neman gasgata mafarkinshi da kuma abinda malamin nan ya fad’a masa cewa _”Ban san gaibu ba, amma a d’an ilimin da Allah ya bani zan iya karambanin fassara mafarkinka Umad, a ganina kar ka cutar da ita saboda kana jin haushin mahaifinta kuma kana son d’aukar fansa a kan sa, a gani na zai fi kyau idan ka sameta ka kyauta ta mata, alamu sun nuna zata iya zama silar warkewar mahaifiyarki, dan ni kai na abinda na fahimta a ciwon mahaifiyarka da sihiri a ciki, kuma ko shakka babu a kullum ana sake sabinta mata wani mugun k’ulli, saidai Allah ya barwa kansa sani, shin wanda ta had’a jini da shi ne ko kuma daga nesa, abu d’aya da zan fad’a maka shi ne, da na kusanta ne ake samun nasarar cutar da ita.”_