Hausa Novels

Lu’u Lu’u 18

Gaba d’aya ya tattara hankalinshi kan ta yana so ya ji me zata fad’a, a tsanake cikin ladabi tace” Ina nufin ka canza mata masu kula da ita, sannan ka kafa dokar hana shiga d’akinta idan ba kai ko d’anta ba, sannan duk abinda za’a mata anfani da shi misali ruwa ko abinci, to a tabbatar an duba lafiyar abinda zata ci sannan wanda aka yarda da shi ne zai bata.”

K’uri sarki ya mata yace” Gimbiya Zafeera, kina magana kamar kina so ki nuna kin gano wani abu ko kuma kina son fad’an wani abu ko?”

Sanyayyan murmushi tayi ta girgza kai tace” Babu abinda na sani yallab’ai, saidai lokaci d’aya na fahimci ana ciyar da madam gubar da a kullum take dad’a kassara mata gabb’an jikinta, imma a ruwa ko a abinci.”

Tare Umad da sarki suka kalli Joy, rarraba ido ta shiga yi tana kallonsu tace” A’a, ya kuke kallo na kuma? Wannan yarinyar fa na kula munafuka ce, tunda ta zo gidan nan take min wani gani gani, ta ya kuke tunanin zan cutar da yar uwata? Ita kad’ai fa ta rage min a duniyar nan.”

Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka, Umad da ya ji tuni zuciyarshi ta fara d’arsa masa shakkunta ne a mugun dak’ile yace” Goggo kin ji mun ce wani abu ne ? Kallonki fa kawai mukayi, miye na tsarguwa kuma?”

Dakatawa tayi da kukan ta kalleshi tace” Ni ba tsarguwa na yi, kula nayi kamar kun yarda da abinda da ta fad’a.”

Sarki Wudar ne ya tab’e baki yace” Idan ma aka samu da hannunki a rashin lafiyar matata babu abinda zai hanani hukunta ki.”

Da mad’aukakin mamaki ta kalleshi tace” Wudar, dama zaka iya hukunta ni?”

Da mamaki Umad ya kalleta jin ta ambace shi da sunanshi wanda bai tab’a jin haka ba, Haman da ke neman haukacewa daga zaune shi ma tsatsaresu kawai yake da ido yana neman dalilin da zai tashe shi a wurin nan kafin yarinyar nan ta masa *bankad’a*, dan ya kula daga cikin dalilin da yasa kowa ke nemanta akwai son fallasa abinda ke b’oye, tunda gashi har ta zak’ulo sirrin daya b’oye shekara da shekaru.

Sarki Wudar kam ranshi b’ace yace “Ko waye a duniyar nan zan hukunta shi indai akan matata ce uwar d’ana k’wallin k’wal a duniya.”

Malaacin murmushi tayi ta kalli Ayam sama da k’asa tace “Har wannan ma zaka iya hukuntata akan Kossam?”

Wani abu Umad ya ji ya soki zuciyarshi da yasa shi wurga mata wani kakkausan kallo, Ayam kam mik’ewa tayi tsaye ta kalleta ta kalli sarki Wudar tace “Me kike nufi da abinda kika fad’a?”

A wulak’ance Joy ta gyara zamanta tace “Ina nufin…”

Tsawar da sarki ya daka mata tasa ta yin shiru ta kalleshi tana hararenshi, kallon su Umad yayi da Ayam yace “Ku jira a waje kun ji.”

A hassale Umad ya mik’e ya fita Haman da Ayam kuma su’a bayanshi, suna fita Haman kam bai yarda ya tsaya dan shi ma a tsorace yake, motarshi ya shiga ya tayar ya bar gidan, Umad na tsaye yana hangenshi har ya fita a gidan, bayanshi Ayam ta tsaya tace” Me nake yi a masarautarku?”

A hankali ya juyo ya kalleta, kawae da kai yayi a gadarance yace “A yanzu dai kam ban sani ba ni ma, tabbas mahaifina ma yana cikin masu nemanki, sai dai bansan me ye manufarsa a kan ki ba, mu jira lokaci kad’an kamar yanda ya fad’a mu ga me zai bayyana mana.”

Da mamaki a fuskarta tace “Ko da manufarsa zata iya saka rayuwata a had’ari kana nufin mu zuba ido har sai zai aiwatar zamu sani?”

Jinjina kai yayi ya juya mata baya yace “Kusan haka?”

Cikin jin haushi ta koma ta gabanshi ta fuskance shi bakinta d’auke da masifa da niyyar tace “Wai kai wanene? Me kake ji da shi? Kai bana son iskanci ka ji ko, ka d’auke ni a nan ka mayar da ni garina.”

Amma kuma yana saka k’ananan idonshi masu sirkin ja a cikin na ta sai kawai ta sunkuyar da kan ta muryarta a tausashe sosai tace “Kana yi kamar baka damu da rayuwata ba yallab’ai, idan hakane to ka maidani garinmu.”

Wata dariyar rainin hankali ya mata yace “Damuwa da rayuwarki? Oho na gane! Wato so kike nima kamar sauran marasa aikin yi, na dinga binki sau da k’afa ina washe miki baki, ina nuna miki babu kowa sai ke ko? To ba zai yiwu ba, ni ba sakarai bane.”

Da sauri ta kalli fuskarshi tace “Sakarci? Hakan wai shi ne sakarci? Yanzu idan da ni k’anwarka ce zaka yarda kana kallo mutanen da ban sani ba suna neman juya min rayuwata? Ko kuma da soyayua muke da kai zaka yarda a rabamu ne? Da kuma ni matarka ce fa a ce z…”

A mugun tsawace yace “Shiru malama.”

Zabura tayi tare da rintse ido gam ta k’ame wuri d’aya, k’urawa fuskarta ido yayi yanayin firgicin data nuna sai ya ji kamar yayi ta kallonta, sanyayyan murmushi ya saki a b’oye a zahiri kuma ya had’e fuska yace “Abinda na fad’a miki jiya ma baki yarda da ni ba, ya kike so na yi kenan?”

A take ta bud’a idonta tace “Ka kaini wajen iyaye na to.”

A shek’e ya kalleta yace “Wane daga ciki?”

Kallonshi tayi da fari da mamakin tambayar, sai kuma ta kawar da kai tace “Iyayena, wanda suka raine ni har na girma.”

Shi ma kawar da kan yayi yace “Suna cikin tsaro a inda suke, rayuwarsu na cikin had’ari, ba zan iya nuna miki su ba.”

Da mamaki tace “Me ya sa rayuwarsu a had’arin? Me suka aikata?”

Kallon fuskarta yayi ya saki murmushi mai ciwo, kamo sark’ar wuyanta yayi yace “Ina kika samu wannan?”

Kallon hannunshi tayi dake rik’e da sark’ar tace “Iyaye na suka bani.”

“Tun yaushe?” Ya tambaya yana tsareta da ido, ba alamar tabbaci a tare da ita tace “Ban sani ba nima, na ganta a wuyana ko da nayi wayo.”

Murmushi yayi yace “Wannan sark’ar a ranar da aka haifeki aka saka miki ita, Ayam karki dameni da son ganin marik’anki a yanzu, duk tambayoyin da kike da muradin yi musu kina da amsoshinsu idan kika aje hankalinki, ki nutsu ki fara tariyar alak’arki da su, dan su basu d’aukeki a ‘yar da suka haifa ba sai yar da sarauniyarsu ta haifa, ma’ana gimbiyarsu.”

Matsawa yayi daf da ita ya saki sark’ar yace” Kina son ganin abun mamaki a rayuwa?”

Idonta ta zuba cikin na shi tace” Ina son abubuwan mamaki a rayuwa, idan ban k’aru da ilimi ba na kan samu alfanu a tare da hakan.”

Jinjina kai yayi yace” Idan kowa yayi bacci zan tasheki sai mu je wani wuri.”

Da mamaki tace” Me yasa sai kowa yayi bacci? Me yasa baka son kulani a gaban mutane?”

Juyawa yayi yana fad’in” Saboda tsaro ne.” Da kallo ta bishi har ya shiga wani b’angaren da take tunanin na shi ne.

A ciki kuma suna fita a hassale sarki Wudar ya rik’o hannun Joy yace” Me kike so ki tabbatar a haka? Me ye na k’ok’arin fad’a musu abinda ba yanzu na ke da niyyar fallasa shi ba.”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button