Hausa Novels

Lu’u Lu’u 19

Amma dan rashin mutumci shi ne yake tambayar wai suna lafiya? Da k’yar ya d’aga labb’anshi yace “Suna lafiya, sai dai ba sa cikin farin ciki.”

Tab’e baki Musail yayi yace “Hakane zai kasance dama, kuma kai ma nasan ba ka farin cikin, amma ka sake jaddada musu su sake yin nesa da ita, dan halin da take ciki yanzu idan suka ji zuciyoyinsu bugawa zasuyi su mutu a take.”

Yar harara Bukhatir ya wurga ma k’eyarsa sannan ya jinjina kai alamar to, ficewa yayi Dhurani na bin bayanshi shi kuma ya bi su da kallo da son sanin me kuma ke faruwa da Juman d’in? Tana ina ma? Me yake damunta? Shin tana farin ciki da auran waccen dabban ne ko kuma a’a?

Girgiza kai yayi cike da rashin jin dad’i ya d’auke kan shi daga k’ofar yana d’an jan tsaki, mik’ewa yayi ya fito ya dawo falon ya samu Zeyfi zaune tana kallo, haushi ya ji ta bashi da kallon fuskarta, gefenta ya zauna yana sake murtuke fuska, ita kuma cikin ladabi ta kalleshi tace “Lafiya ko? Me kuka tattauna haka? Naga kamar ranka b’ace?”

Ture hannunta yayi data dafa na shi hannun yace “Ba komai malama, zaki iya yi min shiru.”

A sanyaye tana had’e kukan dake taho mata a mak’osho tace “Me zai hana?”

D’ora kan ta tayi bisa kafad’arshi taake cukukuiye hannunshi tana siraro yar k’walla, cikin jin haushi ya kalleta dan har k’asan zuciyarshi yake jin tsanar yarinyar, baya sonta bai kuma tab’a son ta ba, ita kawai zab’in mahaifinsa ce ba yanda ya iya, amma shi kad’ai yasan irin dakon kayan da yake a game da ita, zama da wanda baka so babban k’unci ne da zai iya baibaye maka rayuwarka har abada, indai yana kusa da ita to baya farin ciki bare murmushi, ita kuma ga ta da na ci da jaraba a ganinshi, shiyasa in zaiyi wata bai nemeta idan ta kai kanta gareshi sai ya kirata da jarababbiya mayya.

Yanzu ma ya so tureta daga jikinshi, amma daya tuna sarki Musail ya ce zai wadatasu da abinci saiya k’yaleta, ammafa sai tsaki yake yana ta had’e fuska kamar kashi nea jikinshi, yayin da ita kuma take jin wata nutsuwa na sauka a zuciyarta na ganin bai turetaa jikinshi ba, sai ta ssamu kan ta da sake shige masa tana sauke ajiyar zuciya.

*Giobarh*

 

*Da yamma* sarki Wudar na zaune a lambun cikin masarautar tare da fadawa biyu dake nesa da shi yana jin dad’in yanayin, wazirinsa ne ya shigo bayan mai tsaron k’ofar ya masa izinin shiga, da sauri kamar zai tashi sama ya k’araso, zube gwiwoyinshi yayi k’asa yana mik’awa sarki Wudar takardar hannunshi yace “Shugaba na, gashi, akwai matsala fa babba.”

Rai b’ace ya kalleshi ya karb’i takardar yace “Waziri ba na fad’a hutu nake buk’ata ba kar wanda ya dameni?”

A kid’ime yace “Ka gafarce ni yallab’ai, wannan takardar ta fito ne daga sarki Musail, hankalina ne a tashe shiyasa.”

Da sauri ya shiga warware takardar ya k’ura ido dan karantawa, firgitattun kalamai ne kamar haka _”Daga yanzu zuwa wayewar garin gobe ina buk’atar ganin ‘yata gimbiya Zafeera dake hannunka, watsar da buk’atata kuma yana nufin yak’i kake nema da ni, kuma a shirye nake da fuskantarka dan ina da adadin dakarun da zasu iya k’wato min babbar kadarata.”_

A razane ya kalli wazirin yana jin zufa zata keto masa, jefar da takardar yayi ya tunkari hanyar fita, da sauri wazirin mmaa ya bi bayanshi yana mai son jin hukuncin da sarki Wudar d’in zai yanke, dan in har ya zab’i yak’i da sarki Musail to fa shi dai kam babu hannunsa, magana ta gaskiya ma zai tattara iyalinsa su bar k’asar har su gama sai ya dawo, dan ya sani ne ba zasu iya da sarki Musail ba, alfaharinshi kad’ai ya isa ya saka shi d’auko wasu rundunoni daga mak’wabtan masarautu dan su yak’esu su kuma yi kaca-kaca da su.

*Ayam* na d’akinta zaune duk ta matsu dare yayi ta ga abun bazatar nan ta ji an banko k’ofar an fad’o, da sauri ta mik’e tsaye tana gyara rigarta, da ladabi tace “Barka yallab’ai.”

Murmusawa yayi tare da saita nutsuuwarshi wuri d’aya sannan yace “Barka gimbiya Zafeera.”

Kallon idonshi tayi tace “Yallab’ai, zan fi jin dad’i idan ka kirani da Ayam.”

Murmushi yayi ya rik’o hannunta cikin na shi, fad’uwar da gabanta yayi ne yasa ta saurin saka idonta akan fuskarshi, kakkausan kallo ne ta masa dake nuni da me hakan ke nufi? D’an motsa hannunta tayi alamar tana so ta k’wace, amma sai ta ji kam ya rik’eta sosai, jan ta yayi zuwa bakin gadon suka zauna, sam ta k’i d’auke idonta a kan fuskarshi yayin da shi kuma ya kasa kallonta saboda kallon da take masa, idonshi na kallon cinyoyinta duk da cikin riga suke ya shiga fad’in “Gimbiyata, ina so ne na fad’a miki wani abu, sai dai ina jin tsoro.”

Mutsu-mutsu ta dinga yi da hannunta saida ta k’wace kafin ta d’an kawar da kan ta tace “Ina jinka yallab’ai, fad’a min ko menene.”

Gyara zamanshi yayi ta hanyar matse mata wuri, da sauri ta ja baya ta sake jefa masa kallon bansan iskanci tare da yatsina fuska tace “A’a yallab’ai, wai me ye hakane?”

Fuskarshi d’auke da murmushi yace “Kina ji ko? Ban san ko wani ya fad’a miki tarihinki ba…”

Da sauri ta jinjina kao tana sake matsawa baya tace “E e, an fad’a min, amma ban yarda ba, watak’ila kai zaka fad’a min gaskiya.”

Tsurawa fuskarta ido yayi yace “Kinsan komai game da ahalinki kenan?”

Girgiza kai tayi tace “Ta ya zan san komai a game da su? Bayan ko kamanninsu ban sani ba.”

A nutse ya sake kallonta yace “Kinsan bayanin b’atanki?”

A shashance tace “E, yallab’ai Umad ne ya fad’a min wai mahaifiyata ce ta bayar da ni dan ta kareni.”

Da alamar tambaya a fuskarshi yace “Umad? Dama kun yi magana da shi ne?”

Tuna kalaman Umad da tayi cewa saboda tsaro yake nesa nesa da ita yasa ta saurin fad’in “A’a ai d’azu ne da ka ce mu jira a waje, mun fara maganar sai kuma na nuna masa ban fahimci komai ba kawai.”

Jinkina kai yayi alamar gamsuwa yace “Kin tabbatar ya fad’a miki mahaifiyarki ta ceci rayuwarki daga masu son cutar dake ne?”

A gatsine tace “Haka ya fad’a, amma ni ina ganin me ye dalilin da zai sa a rabu da ni tun jinjira? Shin masu son cutar da ni d’in suna tare da ni ne a lokacin da take ganin rayuwa a cikinsu zai sa ni cikin had’ari?”

“Tabbas.” Ya fad’a yana kallonta, da mamaki ita ma ta kalleshi tace “Kamar ya?”

Fuskantarta yayi da kyau yace “Gimbiya Zafeera, a lokacin masu son kasheki dayawa ne, saidai wanda ya fi su had’ari kuma babban cikinsu shi ne, sarki Musail, wato *mahaifinki*.”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button