Lu’u Lu’u 19
Irin kallon nan na galala ta masa kamar wacce bata hayyacinta, duk da labarin sabin iyayenta ba wai ta yarda ba ne, amma dai sai ta ji abinda ya alak’anta mahaifinta da shi ya mata ciwo yana kuma neman zautar da ita, zunbur ta mik’e tsaye tace” No! No! No… No…Hakan ba zai faru ba.”
Cikin d’aga murya tana nunashi da yatsa tace” Yallab’ai ku gaggauta dakatar da labarin k’anzan kuregen nan na ku, kuna neman ku haukata da wannan banzayen labaran, kun manta ni d’in yarinya ce? Shekaru na ba zasu d’auki wannan k’arairayin na ku ba, please yallab’ai ku daina na rok’eku.”
Had’e hannaye tayi alamar rok’o tace” Na rok’eka ka mayar da ni garinmu, ka taimaka ka kaini wajen iyayena ina son ganinsu.”
Mik’ewa yayi tsaye yana neman kamo hannayenta yace”…
*Alhamdulillah*
The post Lu’u Lu’u 19 first appeared on 2gNovels.com.ng.
[ad_2]