Lu’u Lu’u 20
Sanyayyan murmushi tayi tace “Yallab’ai, tsawon shekaru kusan ashirin da bakwai mace na kwance babu lafiya, dan bata magana sai ku kasa fito da wata hanyar da zaku iya magana da iga dan jin damuwarta? Hakan sam bai yi ma’ana.”
Bata jira me zai ce ba kawai ta turata tare da rab’asu ta wuce suka fita, cikin dubara suka sauka a matakar k’waya d’aya dake akwai, suka sauka tayi kwana da ita inda ta nufa d’azu data fito.
A hankali saruniya Kossam ta lumshe idonta k’am, wani dogon numfashi ta ja a hancinta tare da sanyayyan k’amshin shukokin sannan ta fesoshi ta bakinta, har yanzu kuma idonta a rufe suke tana sauraren wannan danddad’an yanayin data jima bata ji irinshi ba, hatta da d’an ta Umad mai tsananin bata kulawar sai dai ya bud’e mata taga ko ya sa a bud’e da tunanin ta ga hasken rana ita ma dan k’warin ido, ko kuma ta shk’i wani iska na daban mai cike da yalwa da babu takura a ciki, amma yau ga shi wata daga zuwanta jiya yau ta fito da ita ta shak’i sabon iska mai tattare da nagartaccen oxygen.
Bud’e idonta tayi a hankali ta sauke akan shukokin duk da duhu ya fara yi, saida Ayam ta kai ta daf da wurin sannan ta dakata, zagayawa tayi ta durk’usa gabanta tana kallon wani bayyanannen farin ciki dake fuskarta tare da nuna jin dad’in fitowar ta waje, ita ma murmushi ta mata tace “Yanayin ya miki dad’i ko madam?”
Lumshe ido tayi alamar e, sake fad’ad’a murmushinta tayi tace “Da zan zauna a gidan nan da kullum na dinga fito da ke kema kina ca’za iskar shak’arki.”
Wani kallo sarauniya Kossam ta mata mai d’auke da alamar tambaya, fahimtar haka yasa Ayam fad’in “Ina son barin nan madam.”
Tsareta da ido tayi tana son tayi magana mai tsayi da ita sai dai babu baki, mik’ewa tayi tsaye ta dafa hannunta tace “Bari na d’an barki ki huta kad’an.”
B’angaren ta nufa zata koma amma lura da wani b’angare da bata san na waye ba? Kuma baya da kyalkyali kamar sauran yasa ta nufa can b’angaren, dan ko dogari babu ko d’aya a bakin k’ofar, tayi sa’a kuma k’ofar a bud’e take, tana kwank’wasa ta ji shiru sai kuma k’ofar ta d’an bud’e, a hankali ta tura ta shiga.
Falon shiru hatta da hasken fitila ma ba mai haske bane sosai, tana cikin k’arewa d’akin kallo ganin wani sassauk’an tsari dake gareshi mai birgewa, ba zato ba tsammani ta a daidai k’aramin teburin tsakiyar da taga laptop ajiye ta ji tayi tuntub’e, tuntub’e kam ba k’arami ba dan abu ne ta ji tayi karo da shi kamar mutum, hakan kuma yasa ta tafiya gaba d’ayanta ta gaba har saida ta ji ta tsallake binda ke gaban na ta sannan ta fad’i, amma kuma ikon Allah sai ta ji bata kai k’asa ba an rik’eta, kuma ko shakka ba tayi cewa mutum ne ya rik’eta.
Umad dake zaune kan sallaya gama sallarshi kenan yana tasbishi da hailala da takbiri ya ji an k’wank’wasa d’akin, da ya ji an shigo kula sai ya fara tunanin kalar tijarar da zai saukewa ko ma wane/ce hadima ce suka shigo masa d’aki bai bayar da izini ba, kafin ya ankara shi ma ya ji an tokareshi a k’ugu da k’afa sai kuma ji da yayi ana neman tausheshi daga zaune, dan haka ya fahimci ko ma wanene bai san da shi ba, da sauri ya tare mai neman fad’o masa ko dan kar su kassara dukansu.
A cikin siririn hasken suka had’a idonsu, tsaf irin rik’on nan ne ya mata na d’aukar jarirai, k’afafunta a mik’e har rigarta ta d’an ‘dage zuwa gwiwanta, hannun na hagu kam a k’ amk’ame yake kan kafad’ar Umad duk ta zaro ido saboda tsorata da tayi.
A hankali ya sauke wani tattausan numfashi ya d’an lumshe idonshi sakamakon b’oyayyan k’amshin turaranta da baya tashi sosai sai ga wanda suka samu kusanci irin haka, dan kuwa rexona ne mai sanyayyan k’amshi da dad’i.
Lura da tayi har wani k’ara tallabota yake yi a jikinshi kamar zai rumgumeta yasa ta d’an muskutawa ta kyabta idonta tace “Yallab’ai.”
Wani luuuu yayi da idonshi da sukayi mi shi wani ruwa ruwa ya k’ara k’ank’ancesu, kamar wanda baya hayyacinshi sai ya knara kusanto da fuskarshi kusan ta ta, da sauri ta d’auke hannuta a kafad’arshi ta shiga yunk’urin tashi zaune.
A d’an zabure ya janye hannayenshi daga kumkuminta ya ja baya yana mik’ewa tsaye gaba d’aya, sai kuma ya had’e fuskarshi iya had’ewa ba alamar wasa, ita ma mik’ewa tayi tsaye tana gyara rigarta cikin raha take fad’in “Sannu yallab’ai, ka gafarce ni ban kula da kai bane sam, ashe dama nan ne sashinka?”
Kawar da kan shi yayi tare da zaunawa kan kujerar ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya, a d’an kaikaice ya kalleta fuska a gimtse yace “Me ya kawoki nan?”
Kallon salayyar daya tashi tayi, a nutse ta kalleshi ta saki murmushi, sosai shigarshi ta birgeta ya had’e cikin doguwar riga kalar ruwan toka da kuma wata k’aramar hula a kan shi kalar kayan, girgiza kai kawai tayi tace “Ba komai.”
Takawa tayi zata wuce ta tsakanin k’afafunshi da k’aramin tebur d’in, saida ta wuce sai kuma ta juyo ta kalleshi tace “Yallab’ai, wai me yasa baka sakani a addinin nan na ka ba? Akwai wani sharad’i ne na shiga? Ko kuma dai saida tarin dukiya? Ka fad’a min na ji idan zan iya mana.”
Kallonta yayi duba da ta zo da maganar da yake son yi mata tuni a kan ta, dan abun farin ciki da alfaharinshi ne a dalilinshi wani ya karb’i addinin musulunci, nuna mata gefenshi yayi alamar ta zauna, da zumud’i ta zauna tana kallon fuskarshi, a nutse cike da dattako da shan k’amshi na jinin sarauta daya gama ratsa duka sassan jikinshi ya kalleta kamar wata wacce ke bashi haushi, da k’yar ya d’aga labb’an yace “Da gaske kina son shiga?”
Jinjina kai tayi tace “E, ina so sosai.”
A hankali ya d’an jinjina kai sannan yace “Akwai sharad’i, sharad’in kuma shi ne ki tabbatar da zuciyarki kike so ba wani ne ya tilastaki ko kuma wani dalili na daban, sannan addinin musulunci addini ne da bai yarda da ka shiga yau kuma anjima ka ce zaka fita ba saboda wani dalilin, saboda haka ma har aka tanadi hukunci mai tsaurin gaske akan duk wanda yayi ridda, ma’ana ya bar addininsa da gangan.”
Cike da tabbaci tace “Na yarda da sharad’in yallab’ai, ba zan tab’a fita ba, kuma da gaba d’aya zuciyata zan shiga.”
Jinjina kai yayi ya numfasa yace “Shikenan zaki shiga ke ma, amma fa idan kin shiga akwai abubuwa dayawada zaki koyesu daga gareni, kinga kenan babu maganar tafiya gida.”
Tsam ta kalleshi da mamaki tace “Kamar ya? Hakan na nufin zan ta zama a nan kenan?”
Hararanta yayi yace “Ke kuma baki son haka ko?”
Turo baki tayi gaba tace “E gaskiya, na fi so na koma gidanmu ni ma.”
Murya k’asan mak’oshi yace “Kuma kina da dalilin zama a nan?”
Tab’e baki tayi tace “Ni dai yanzu fad’a min yanda anyi na shiga addinin nan.”
A nutse yace “Ki fad’i abinda duk na fad’a.”
Jinjina kai tayi ta k’urawa labb’ansa ido, a tsanake ya shiga furta mata kalmar shahada tana maimatawa har suka kai k’arshe, kallonta yayi da sanyayyan murmushi a fuskarta yace “Alhamdulillah, yanzu ke ma kin zama kamar ni, ma’ana kin musulunta.”
Da farin ciki ta bud’e hannaye da niyyar ta rumgume shi alamar nuna farin cikinta na zamowar silar shigarta addinin, sai kawai ya d’aga mata hannu fuska a had’e yace “Dakata, hakan da kike shirin aikatawa yanzu haramun ne a addinin ki, duk namijin da tsakaninki da shi akwai yiwuwar aure, to hakan laifi ne dan shed’an zai iya shiga tsakaninku.”