Hausa Novels

Lu’u Lu’u 21

 

Ta k’arashe tana kallon duka dattawan, a nutse sarki Abdallah ya jawo kan ga ya d’ora a k’irjinshi ya shiga shafa kanta, a tausashe ya shiga fad’in” Shin yanzu lokacin da kike buk’atar sanin wannan ne? Me zai hana ki maida hankali kan mahaifiyarki wacce a yanzu take kurkuku a d’aure saboda ke.”

 

Da sauri ta d’ago ta kalleshi tace” Mahaifiya ta? Habb… Sarauniya?”

 

Jinjina mata kai yayi yace” Ita.”

 

A rikice ta mik’e tsaye tace” Tana ina yanzu? Me yasa take d’aure a kurkuku ? Wane laifi ta aikata?”

 

Mik’ewa Abdallah yayi ya kama hannayenta yace “Kwantar da hankalinki, babu laifin data aikata wanda ta cancanci wannan hukuncin, dama can shi ba adalin sarki bane, shiyasa yake ganin yaudara ce tayi data kub’utar dake daga sharrinsa.”

 

Sororo ta kalleshi tace “A tak’aice dai mahaifina ba mutumin kirki bane? To mahaifiyata fa? Ya zanyi ta kub’uta?”

 

Girgiza kai Abdallah yayi sai kuma yayi murmushi yana kallon fuskarta yace “Duk da kowa ya yarda ke ce mai kawo sauyi a k’asar, amma bamu san ta ina kuma yaushe ne hakan zai faru ba, da fari dai mu zuba ido mu jira mu ga e lokaci zai mana, daga nan sai mu san abun yi.”

 

Cikin fashewa da kuka tace “To amma a ce ba zamu iya cetota ba har sai abinda lokaci yayi da mu?”

 

Umad dake zaune yana ta kallonsu kamar ya samu wani kyakyawan film ne ya katseta da fad’in “Saboda shi lokaci ya fi komai adalci a rayuwa, shi ya fi yin sakamako mai kyau sannan ya hukunta kowa.”

 

Cike da tausayin kan ta ta koma kujerar ta zauna, a hankali ta d’ora kan ta a cinyar Bilkis tana shashek’ar kuka, shafa gashinta ta dinga yi tana fad’in” Kiyi hak’uri kinji, tsawon shekaru muka d’auka muna hak’uri mu ma, amma a yanzu zamu iya cewa komai ya kusa zuwa k’arshe.”

 

Kamo hannun Bilkis tayi ta rumgume shi a k’irjinta tace” Ku ma wai kun yarda ni yar baiwa ce? Wannan wace irin baiwa da zata saka kowa mararin halaka ka?”

 

Gyara zama Umad yayi ya kalli fuskarta yace” A duniya kowane d’an adam da kalar baiwar da ubangiji yake hallitarsa da ita, Allah shi ne yafi sanin daidai da kuma ba daidai ba, wani mutumin a zahirinsa k’ansk’antacce ne kuma fak’iri, amma a bad’ini ubangiji kan iya aje baiwar da babu mahalukin da ya ma ita sai shi, ko a cikin littafi mai tsarki akwai ayoyi da dama da suke fad’akar da mu girmama d’an adam ko baka san shi ba, haka ma a hadisai ingantattu akwai irin haka, k’aramin misali da zan baki shi ne akwai wani sahabin Manzon Allah (S.W.A) da Allah ya hallice da siraran k’wabri, sai wata rana yana nufo majalisar fiyayyen hallita, sai sahabai suka dinga masa dariya suna nuna k’wabrinsa, a take fiyayyen hallita ya fad’a musu cewa wannan k’wabrin da suke gani sirara kuma k’anana, sun fi *dutsen* uhud nauyi a sikeli wajen Allah, dan haka su daina raina hallitar ubangiji.”

 

D’orawa yayi da fad’in” Haka kuma akwai wani sahabin Manzon Allah (S.W.A) da Allah ya jarabce shi da shan giya, kullum ya zo majalisin annabi ya kan zo ne a buge cikin maye, hakan yasa kullum sai annabi ya sa an mishi bulala, wata rana sai sahabbai suka dinga aibatashi suna masa fad’an akan me zai sa ba zai daina ba? Suna ta aibata shi sai annabi ya dakatar da su ta hanyar fad’a mu su ya zasu taimakawa shed’an a kan d’an uwansu, su mi shi addu’a mana Allah ya shirye shi, dan shi wannan da suke gani yana son Allah manzonsa.”

 

Gyara zama yayi yace” Kinga kenan zunubin da yake aikatawa bai hana ubangiji ya wadace shi da baiwar son shi da kuma manzon sa ba, dan samun wannan soyayyar ma babbar baiwa ce wace ba kowa Allah ya yake ba wa ita ba.”

 

A nutse ya ci gaba da fad’in” Ayam manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa ya fad’a mana, a cikin mutane akwai wanda da zai rantse ya ce za’ayi ruwa, to girma da darajarshi ya isa ubangiji ya tsallakar da rantsuwarshi ta hanyar kautar da shi daga yin kaffara, shiyasa babu kyau raina hallitar Allah kowace iri ce.”

 

Gyara zamanshi yayi sosai yana kallonta sanda take tashi zaune ta nutsu sosai tana saurarenshi yace “Ayam na yarda kina da baiwa ke ma, sai dai baiwarki ni a wajena a zahirance take, babbar baiwarki bata wuce canjin yare da ubangiji ya yassare miki kina yi ba, ke kan ki wani yaren baki san wane iri bane ko na wace k’asar ba, amma haka koke samun kan ki da shi a bakinki, inda aka samu matsala kuma shi ne da manyan dattab’ai suka shiga cikin lamarin baiwarki, hakan yasa aka dinga farfagandin zuwanki har maganar baiwarki ta fara zama kamar kasuwanci, da haka kuma sai mutane suka dinga yayatawa masu k’arawa na k’arawa masu ragewa suna ragewa, har aka tunbatsa baiwarki ta kai matakin da wasu suke ganin kamar zasu mayar dake waliyiyarsu, daga cikin masu nemanki dana tattauna da su burinsu kawai su had’a hannu da ke wajen hab’aka nauyin aljihunsu, ma’ana su mayar dake bokanya dan su dinga samun na kashewa.”

 

Wani dogon numfashi ya sauke ya dafe goshinshi yayi shiru alamar doguwar maganar nan tasa kan shi fara juyawa, Abdallah ne ya saki murmushi ya d’ora da fad’in” A wajensu babban malami Dhurani ma kusan haka take, malamin fada ne da mahaifinki ke matuk’ar yarda da maganar sa, saidai zan iya ce miki shi ne k’ashin bayan dake ingiza mahaifinki wajen ganin sun kasheki, dan kuwa ya san ko ba dad’e ko ba jima dole zalincinsu zai zo k’arshe, hakan yasa yake d’aya daga cikin masu son kasheki.”

 

Ajiyar zuciya sarauniya Bilkis ta sauke tace “Yarinyata, kinga tashi muje ciki ki huta, wannan labaran zasu iya tarwatsa miki tunaninki.”

 

Kallon sarauniyar Umad yayi yace “Ku tayata farin ciki, d’azun nan ta karb’i addinin musulunci ita ma.”

 

Da farin ciki suka kalleshi tare inda sarauniya ta jawota jikinta tace “Kai amma na taya ki murna, hakan yayi kyau sosai.”

 

Umad ma murmushin yayi yace “Saidai ku fara d’orata kan abubuwa muhimman dya kamata ta fara sani, dan lokaci bai bani damar sanar da ita ko da wankan daya hau kan ta ba.”

 

Mik’ewa sarauniyar tayi ta kama Ayam suka mik’e tace “Karka damu kanka da wannan, yanzun nan zan taimaka mata tayi komai.”

 

Kamata tayi suka nufi d’aki suka bar su nan zaune, suna shiga ta saketa ta nufi ban d’aki ta d’auko farin towel ta kawo mata tace “Cire kayanki zakiyi wanka ne.”

 

Cike da kasala tace “A wannan daren?”

 

Murmusawa tayi amma ba tace komai ba sai kallonta har ta cire kayan ta d’aura wannan towel d’in, hannunta ta kama suka shiga ban d’akin, wata kujerar roba mai kyau ta nuna mata ta zauna sannan ta aje mata k’aramin bokiti da ruwa a ciki masu tsarki da tsarkakewa, sakata tayi ta cire towel d’in sannan ta ce ta d’aura niyya a zuciyarta zatayi wanka na tsarki na shiga addinin musulunci sannan ta fara da kama ruwa daga k’ugunta zuwa, a haka ta taimaka mata tayi wankan tsarki sannan ta d’aure jikinta da towel suka fito.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button