Lu’u Lu’u 21

*Suna* shiga ciki Umad ya sake gyara zama ya sauke numfashi ya kalli sarki Abdallah, cikin nutsuwa da son fahimtar da shi yace “Ranka shi dad’e, akwai wani abun da ban fad’a maka ba, ban san ta ya zaka fahimce ni ba.”
Murmushi ya masa irin na babba da yaro yana d’an girgiza kai a tsanake yace “Yarima Umad, karka damu kan ka, ka fad’i abinda kake son fad’a, ai yanzu mun zama d’aya.”
Sunkuyar da kai yayi k’asa yace “Magana ta gaskiya an d’aura mana aure da ita, amma fa…”
Kallon sarki Abdallah yayi dan ya karanci yanayin daya shiga jin hakan, amma sai ya ga fara’a ce a fuskarshi da kuma mamakin dake nuna yana son jin yaushe haka ta faru? Sake sunkuyar da kai yayi alamar jin kunya yace” Ita kan ta bata sani ba, na yi hakane dan na tabbatar da zamanta a tare dani, dan na rasa wanda zan iya yarda da shi game da lamarinta bayan su Utais, su kuma a kowane lokaci za’a iya farmakarsu har da ita kan ta.”
Da tsantsar farin ciki sarki Abdallah ya dafa kafad’arshi yace” Masha’Allah Umad, ka yi aiki mai kyau gaskiya, hakan ya tabbatar min zaka iya yin komai akan jinkar nan ta wa.”
Da mamaki kad’an a fuskarshi yace” Amma yaushe haka ta faru?”
Da kunya ya amsa da “A ranar dana samu had’uwa da su Utais, shi ha ba ni aurenta kuma na karb’a, bayan su da kai yanzu dana fad’a babu wanda ya sani.”
Jinjina kai ya sake yi yace “Hakan yayi kyau gaskiya, saidai wani hanzari ba gudu ba.”
Wani azababben fad’uwa ya ji gabanshi yayi da bai san dalili ba, hakan ya bashi damar k’ure sarki Abdallah da ido yana jiran ya ji me zai ce, cikin dattako sarkin ya d’ora da “Ina ga me zai hana ka fad’a mata? Dan gudun samun wata matsalar.”
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani sakayau a zuciyarshi kafin ya jinjina kai yace “Insha’Allah zan fad’a mata, amma ba yanzu ba, ina jiran lokacin daya dace ne.”
Jinjina kai yayi yace “Shikenan, amma dai ka kula, kar ka tsaya jiran lokaci kuma wani abun ya b’ullo.”
Murmusawa yayi a zuciyarshi yace “Hakan ma ba zai faru ba.” A zahiri kuma bai ce komai ba.
*Man d’umi* ta bata ta shafe jikinta da shi kafin ta mayar da kayanta suka fito, zaune suka samesu suna shan shayi suna ta murmushi alamar hira suke kuma tana musu dad’i, zaune sukayi inda Ayam ta kalli Umad cikin muryar data disashe tace “Yallab’ai yaushe zaka tafi gida? Dare fa yayi sosai, ko nan zaka kwana ne?”
Kallonta sukayi dukansu inda sarki Abdallah ke sakin murmushi, cike da raha da nishad’in daya jima bai samu irinsa ba yace “Ai d’aki zamu ware muku na musamman ke da shi.”
Zaro ido tayi sai kuma ta kawar da kan ta ta tab’e baki tace” Ka daina fad’in haka.”
Dariya suka saka inda sarauniya Bilkis ta jawo kanta ta d’ora a cinya tace” Rabu da shi kinji, kwanta ki huta.”
Sarki Abdallah ne yace” Wane hutu kuma bayan yanzu zasu koma.”
Da sauri Ayam ta mik’e zaune tace” Me? Yanzu kuma? Ni gaskiya babu inda zan tafi, na zo kenan kawai shi ya tafi.”
Satar kallonta yayi ta gefe ido lokaci d’aya kuma ya d’auke kan shi, sarki Abdallah ne yace” Kin fa san duk sanda zai zo nan to ya kan faki ido ne, jimawar ta su a nan zai karkato da hankalin mutane da dama, kuma kinsan ba kowa ya san muna nan ba.”
Jinjina kai tayi tace” Hakane, amma ina so na zauna da ita.”
A nutse yace” Zaku zauna idan da rai, amma mu yi addu’ar komai ya daidaita tukuna.”
Jinjina kai tayi kamar zata fashe da kuka ta kalli fuskar Ayam ta shafi kumatunta tace” Allah ya miki albarka, ki kula da kanki kinji ko.”
Ita ma kamar za tayi kukan ta jinjina kai alamar to, mik’ewa tayi a kasalance ganin shi ma Umad ya mik’e, rumgume juna sukyi da sarauniya sosai har da matso k’walla, da k’yar suka rabu sannan ta juya ta rumgume sarki Abdallah, daddab’a bayanta yayi yace “Ki kula da kanki.”
Jinjina kai tayi ta d’ago daga jikinshi ta kalli fuskarshi, dariya tayi ta jawo farin gemunsa tace “Ina son wannan.”
D’an dungure mata kai yayi yace “Ja’ira, gemun na wa?”
Dariya tayi ta d’an mak’ale a jikin sarauniya tace “To ai yayi fari ne sosai.”
Dariya suka saka gaba d’aya sai Umad daya murmusa yana girgiza kai dan shi ma abun ya birgeshi sosai, kallonta sarki Abdallah yayi yace “Kin san shekaru nawa ne a kai na kuwa?”
Da yar harara ta kalleshi tace “Zasu fi d’ari ne?”
Jawo hannunta sarki yayi hakan yasa ta tahowa kamar zata fad’a masa, sai kuma ya turata a k’irjin Umad yana fad’in “Kaga rabani da ita ku tafi kafin gari ya waye mu ku.”
Tsit sukayi suna kallon juna saboda tana fad’owa sai ya d’auka ko zata fad’i ne sai ya rik’e k’ugunta gam da hannunshi, jim sukayi suna kallon juna sai kuma ta d’an shiga k’ok’arin zamewa, da sauri ya saketa tare da juyawa yace” Saida safenku.”
Bai k’ara juyowa ba bare wani ya masa magana har saida ya fita, jiki a sanyaye ta bi bayanshi tana d’aga musu hannu, yana shiga motar ita ma ta bud’e ta shiga, saida suka ga tafiyarsu sun hau titi kafin suka rufe k’ofar suka koma ciki.
Ta yanda akayi suka zo nan ta haka suka koma gidan, saidai suna isa asuba tayi fadawa har sun tashi kowa ya fara shirin tsayawa kan aikinshi, wanda da musulmai ne da sallah suke a lokacin, ganin mutane na ta shawagi yasa Ayam rik’e hannunshi gam a matuk’ar tsorace tace “Babu ta yanda zaka barni na shiga ni kad’ai, kawai mu tafi tare ka rakani.”
K’ok’arin k’watar hannunshi yayi yana fad’in “Sakeni malama, sallah zan yi.”
“Nima ai sallar zanyi, muje idan ma kasheni za’ayi a kashemu tare.” Tayi maganar tana jan shi zuwa ciki, ba yanda ya iya haka ya dinga binta har suka taka matakalar d’aya ta tura k’ofar suka shiga dan masu tsoron k’ofar basu iso ba, falon shiru babu motsi kuma babu haske, hakan yasa shi zame hannunshi ya nuna mata hanyar yace “To wuce.”
Kallonshi tayi sai kula ta juya zata tafi, juyawa yayi shi ma zai fita suka ji muryar sarki Wudar yace “Daga ina kuke yarima?”
Cak ya tsaya ya rufe ido alamar sam bai so haka ba, ita ma da sauri ta kalli inda ta ji sautin, zaune ya ke ya saka tv gaba saidai bata san kallo yake ba ko kuma akasin haka, gyara tsayuwarta tayi tana kallon Umad daya juyo a hankali ya kalleshi shi ma.
Sosa k’eyarshi yayi cikin rashin gaskiya yace “Am.. Pah, dama…”