Hausa Novels

Lu’u Lu’u 22

Mugun kallo ta wurga mata ka d’auka ita ma yanka mata tapi zatayi, a hassale sosai ita ma ta juya zata fita tana yin k’wafa, ta fita kenan mai tsaron k’ofar ya rufe Juman ta matsa kusan k’ofar tace “Ki ji da kyau, ki rik’e abinda zan fad’a miki yanzu da mahimmanci, ki rubuta ki ajiye Zafreen, addini na zai mamaye k’asar nan, dan ina ji a jikina a duk inda yar uwarki take tana cikin hasken rayuwa mai cike da saitin shari’a.”

Tana gama fad’a ta juya ta koma inda take zaune, ita ma a hassale ta wuce inda Adah ma ya dinga binta da sauri har suka bar kurkukun.

 

*A* wajen sarki Musail ma dako yake hakan yasa ko rintsawa bai yi ba kamar dai sarki Wudar, ya kasa ya tsare yana son gari ya waye ya gae sarki Wudar d’in zaiyi, idan har ya turo masa yarinyar sa to ya zab’i zaman lafiya kenan, idan kuma rana ta fito babu labarinta hakan na nufin ya zab’i tashin hankalin da salwantar da rayuka, kuma shi tun jiya ya shirya ma hakan haka ma dakarunsa.

*Giobarh*

Kayan daya tura aka kai mata su ta saka, riga ce doguwa kalar bleue mai haske, bata da wata kwalliya ta zo a gani, sai dai daga k’asa tana da kwalliya kamar bakin lesh, haka dattijuwar jakadiyar ta nad’a mata d’an kwalin gwanin sha’awa, hakan yasa tayi kyau da ita duk da ba kwalliya tayi ba.

Fitowa sukayi zasu wuce amma ta nemi izinin shiga d’akin sarauniya Kossam dan ta mata sallama, dan ita kad’ai tasan me take shiryawa a zuciyarta, indai har ta tafi kam ba zata dawo ba har sai ta gyara tsakaninta da mahaifinta.

A hankali ta shiga d’akin tana mai zuba idonta akan gadon, k’arasawa tayi kamar kullum ta zauna kusa da ita, rik’o hannunta tayi tana mai fad’ad’a murmushin fuskarta cikin sanyin murya tace “Madam, ni zan tafi gidan mahaifina, ban sani ba ko zan dawo, amma dai nasan zanyi kewarki, kuma wata rana zan zo na ganki.”

Hannunta dake cikin na ta ta sumbata tare da sakin hannun ta mik’e tsaye, sake sunkuyawa tayi ta sumbaci goshinta sannan ta kalli idonta tace” Na barka lafiya, ina rok’on ubangijina ya dubi lamarinki ya ci gaba da tsareki, Allah ya baki lafiya.”

Juyawa tayi ta fita ba tare data juyo ba dan tausayin matar yasa yar k’walla taruwa a idonta, sarauniya Kossam ma k’ura mata ido tayi tana son tace” Tsaya.” Saidai ya gagara hakan, tana ficewa a d’akin ta lumshe ido sai taji kamar zatayi kuka saboda tafiyar yarinyar da ko sunanta bata ji ba har yanzu.

Tana saukowa daga matak’alar daidai Joyran tana tsaye, ko kallonta ba tayi ba ta nemi wucewa ta barta, cikin jin haushi ta shak’o wuyan rigarta ta nunata da yatsa tace “Ke ce kika bada izinin a hanani shiga wajen yar uwata?”

Da k’arfi ta fizge rigarta ta kalleta sama da k’asa tace “Ba ni ba ce halinki ne.”

Zata rab’ata ta wuce ta sake rik’o wuyan rigarta, cikin jin haushi Ayam ta buge hannunta da k’arfi tare da turata baya tana jan dogon tsaki, da sauri Joyran ta dafe mararta tare da fad’in “Kai kai kai!”

A hankalce ta bita da kallo ta kuma kalli marar data dafe, sarki Wudar dake tahowa kusansu cikin shigarshi ta alfarma ganin abinda ke faruwa yasa shi saurin k’arasowa, babu wacce ta kula da shi sai ma wani malalacin murmushi da ta saki ta gyara tsayuwa tana k’are mata kallo tace “Ya kamata kisan wani abu, dan kin kassara rayuwar uwar gidan nan ba hakan ke nufin zaki samu nasarar maye gurbinta ba, haka zalika ko da kin samu ciki da wanda kike ganin makusancin gidan nan ne, ba zaki samu abinda kike da buk’ata ba, dan sarauniya ta kusa samun lafiya da izinin Ubangiji.”

Hanyar fita ta nufa haka shi ma sarki Wudar ya bita ba tare daya kula da Joyran d’in ba, cikin takonsu d’aya bayan d’aya sarki Wudar ya kalleta yace” A ina kika san tana da ciki?”

Da sauri ta kalleshi a zuciyarta tace” Kenan dai gaske tana da cikin?”

A zahiri kuma dakewa tayi tace” Yallab’ai ba fa iya gandun daji na ke da burin karanta ba.”

Jinjina kai yayi ya saki murmushi har suka fita, motoci ta samu a laye da tarin dogarai duk suna jiranta dan su rakata, kallonshi tayi tace” Yallab’ai wannan tawagar fa?”

Da fara’a yace” Karki damu kan ki gimbiya, zasu rakaki ne har masarautarki.”

Cikin damuwa tace” Amma ai sun yi yawa.”

Girgiza kai yayi yana murmushi yace” Ba zaki gane ba, amma idan kika isa masarautar Khazira zaki fahimci girman matsayinki.”

D’an juyawa tayi ta sake kallon dogaran sannan ta kalli b’angaren Umad, a sanyaye ta kalli sarki Wudar cikin ladabi tace” Yallab’ai zan iya zuwa muyi ban kwana da yallab’ai d’anka?”

Jim ya d’anyi ya kalli b’angaren na Umad shi ma, sai kuma ya jinjina kai ya mata alama da sandarshi fara tas wacce aka lullube da wani yadi sak kayan jikinshi yace” Zaki iya, amma karki jima, kinsan ana jiranki.”

Da fara’a ta nufi b’angaren Umad da farin cikinta, tsaye tayi k’ofar falon tana k’wank’wasawa a hankali, saidai shiru babu motsi bare a amsa mata, gyara tsayuwa tayi ta ci gaba da bubbugawa, amma da ta ji shiru dai sai tayi tunanin ko kamar jiya ne yana sallah, a hankali ta tura k’ofar tana fad’in “Yalkab’ai.”

Mayar da k’ofar tayi ta rufe ta shiga takawa a hankali, d’akin d’uf sai duhu hakan yasa ta shiga waige waige, d’an motsi ta ji daga gefenta haka kuma da alamar hasken wuta a d’akin, sakin jikinta tayi alamar ta ji dad’in haka, da d’an sauri ta nufi shiga d’akin tana zuwa ta tura k’ofar tana sake fad’in “Yallab’ai ni zan…”

Cak ta tsaya tare da zuba idon ta akan abinda take gani, yawo ta dinga yi da idonta tana k’arewa k’aramin d’akin kallo wanda gaba d’aya bangon aka zagaye shi da hotuna birjik, a sanyaye kamar wacce k’wai ya fashe ma ta dinga d’aga k’afarta tana k’arasa shiga ciki, jinin jikinta ta ji yana tsintsinkewa, gabanta kuma na ta fad’uwa kamar zai kayar da ita.

Tsaye tayi a tsakiyar wani allo dake shak’e da hotunan mutane wasu an musu alamar an gama da su, wasu kuma an rubuta harafi a kai ko kuma lamba, wasu mutanen kuma jan zare aka mak’ala aka ja zuwa wata fuskar alamar akwai alak’a a tsakanin ababen zargin.

Babban abinda ya d’aga hankalinta ta ji numfashinta na neman tsayawa bai wuce ganin hoton mahaifinta da tayi ba da kuma na ta hoton a ciki, haka kuma akwai hoton wannan mutumin data gani tare da wacce ake fad’in yar uwarta ce (Khatar).

Me kenan hakan ke nufi? Me hakan ke nufi? Me yallab’ai Umad ke shiryawa? Waye shi? Kafin ta samu amsar hakan ya shigo kunnensa manne da yawa alamar yana amsawa, da sauri ta juya ta zuba masa ido kamar yanda shi ma yana ganinta ya mata k’uri ya ajz wayar, hawayen da tayi k’ok’arin rik’ewa ne suka gangaro mata, cikin dagiya da kafiya ta share hawayen ta gyara tsayuwarta tace “Who are you? What are you looking for me? What about my father?”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button