Lu’u Lu’u 23

*23*
Saida suka d’auki hanya aka shaidawa sarki Musail Ayam tana hanyar zuwa, irin farin cikin daya tsinci kanshi baya misaltuwa, dan ganinshi kawai yake ya kasheta kuma ya ci gaba da mulkinshi a nutse.
A cikin k’ank’anin lokaci ya sa aka k’awata masarautar nan aka dinga shiga da fita ana shirin tarbanta kafin ta k’araso, duk da bai fad’a ba iya masarauta ne kawai, amma sai ga shi maganar har ta fita wajen masarauta mutanen gari sun fara d’auka suna yayatawa, kafin ka ce kwabo sai ga dayawa daga cikin talakawa sun fara cika k’ofar masarautar suna son ayi komai a gabansu.
Mutanen sun kasu uku ne, wasu so suke su ga yanda take kawai, shin ta kai irin kurantata da ake? Ko kula dai ba akwai nak’asu ta wani wajen? Wasu kuma har zuciyarsu suke son ganinta dan su saka mata albarka na sabon canjin da ake fad’a ita zata kawo shi, inda kaso na k’arshen kuma su yan kashe kwarkwatar idon su ne kawai, su ga da gaske ne ko kuma k’arya ce?
Tunda ta ji labarin wai Zafeera na hanyar zuwa, ta fito farfajiyar gidan ta ga an kacame sai kaye-kaye ake hankalinta ya rub’anya tashi, tambayarta bata wuce “Me yasa aka fi fifita Zafeera akan ta ba? Mutanen gari basu san ko kamanninta ba, amma daga cewa zata zo shi ne suke wani k’warya k’wayan biki? To ita me ye makomarta kenan?”
A zafafe ta juya zata koma ciki dan d’aukar wayarta ta kira wanda zai bata shawara, tana shiga falon sarki Musail ya fito cikin wani shiri da ita dai bata tab’a ganinshi haka ba, k’are mata kallo yayi cikin had’e kyakyawar fuskarshi yace” Ya ke kuma baki shirya ba? Baki san k’anwarki zata zo bane?”
Yamutsa fuska tayi tace” Sai me dan zata zo? Me ya dameni ni kuma?”
Tsaki ta ja zata wuce abinta yace” Zafreen.”
Nunata yayi da yatsa yace” Ya kamata kisan ni mahaifinki ne, ba komai ne ya fito bakinki zaki fad’a min ba, ki kiyaye gaba.”
Turo baki tayi gaba zata had’eshi ta wuce rai b’ace gana gunguni, saida ya ga b’acewarta ya shiga dogara sandarshi wacce tsabar alfahari yasa aka sarrafa mi shi iga da narkakken gwal, cikin takon k’asaita kamar wani d’an agwagwa ya dinga takawa yana k’arewa gyara da shirin da ake ga ma gidan.
*Giobarh*
Suna fita a gidan da sauri ya koma ciki yana danna kiran lambar Haman, cikin sa’a bugu d’aya ya d’aga, duk da hankalinshi tashe yake ta yanda gaba d’aya baya da nutsuwa, amma haka ya tattaro nutsuwarshi a dak’ile da yan tsirarun kalmomi yace “Hukumarmu tana da hannu a cikin sanarwar da ake a gidan telebijin ne?”
Cikin rashin tabbas Haman yace “Bana jin suna da hannu a ciki, saidai suna son sanin abinda ke faruwa.”
Cikin d’aurarriyar murya k’asan mak’oshi yace “Su kwantar da hankalinsu, yanzu haka tana daf da isa wajen mahaifinta.”
Da k’arfi Haman yace “Me? Kana nufin wai Khazira?”
“E.” Ya fad’a a take kuma ya kashe wayar, da kallo Haman ya bi wayar ya mik’e tsaye ya fara safa da marwa, rarako ido yayi yana tunanin inhar tana wannan babbar fada shi kam ta ya zai iya samun cikar buri sa ko kuma ya ce alk’awarin daya d’auka, ganin tunanin ba zai fisheshi ba yasa shi d’aga wayar ya danna wasu lambobi ya kira, bata jima tana kururuwa ba aka d’aga, shi ma hankali tashe ta yanda ya gagara b’oyewa a harshen larabcin parsi yace “Kinsan kuwa me ke faruwa ta wajen can? Ina ga kawai ki hak’ura da buk’atar nan ta ki, dan yanzu haka Zafeera tana hanyar zuwa Khazira dan had’uwa da sarki Musail, kinga kenan ba sai kin tiasta ni aurenta ba dan kasheta zai yi shi.”
Ita ma mik’ewa tayi daga inda take tace” Ka tabbata?”
” Na tabbata man.” Ya fad’a cike da tabbaci, cikin saurin maganarta dake samo asali lokaci zuwa lokaci tace” Kana ji d’an uwa na, ba zamuyi sake da wannan al’amarin ba, tsakanin ‘ya da uba fa sai Allah, ba lallai sarki Musail ya kasheta ba kamar yanda kowa ke hasashe, ka ci gaba da saka ido akan su dan Allah, idan har shi bai yi wani yunk’uri ba kai sai kayi.”
Iska ya furzo yace” Yar uwata, kinsan abinda da kike nema na da shi akwai hatsari sosai, idan fa akayi rashin sa’a zan iya rasa rai na bayan na rasa abokina da kuma yardarsa.”
D’an tsaki tayi tace” Ka manta da Umad dan Allah, kai dai kayi komai da taka tsantsan kawai, babu abinda zai faru da kai, kuma kar ka manta ni ma a had’arin nake, amma a k’arshe idan mukayi nasara rayuwarmu ce zaga gyaru ni da kai.”
Jinjina kai yayi yace” Shikenan, zan ci gaba da jarabawa, ki kula da kan ki.”
Asanyaye ita ma tace” Ka kula da kanka kai ma.”
Da haka ya kashe wayar yana ajeta gefenshi ya dafe k’ugu yana tunanin lamarin shi kam, yana yi ne dai amma a tsorace yake musamman ma Umad shi ya fi d’aga masa hankali, idan har ya fahimci manufarshi wallahi kai tsaye zai iya harbeshi da bakin bindiga ba tare da ya ji ta bakinsa ba bare ya masa uzuri.
*Wajen* Umad kuma suna gama wayar jalabiyar jikinsa ya canza ya fito rik’e da makullin motarshi, cikin hanzari ya nufi inda ake aje motocin ya shiga motarshi ya bar gidan.
Tafiyar awa uku yayi kafin ya isa bakin ruwa (Beach), kai tsaye d’akin da aka k’erashi da nagartaccen katako, yana k’wank’wasawa d’aya yayi jim bai sake ba, yan sakanni aka bud’e k’ofar, da fara’a Habbee ta matsa gefe dan ya shigo tana fad’in “Sannu da zuwa yallab’ai.”
Ba tare daya kalli fuskarta ba yace “Yana ciki ne?”
“E.” Ta fad’a tana sake kaucewa a hanyar, shigewa yayi ciki amma yayi tsai yana duba ta inda zai ga Utais d’in, Habbee data rufe k’ofar kallonshi tayi tace “Yallab’ai me za’a kawo…”
Bai bari ta dire ba yace “Yana ina ne? Ki masa magana.”
A tsanake ta kalleshi tace “Yallab’ai kamar da matsala ko?”
Waina idonshi yayi alamar ya k’agu ba wannan yake son ji ba, jinjina kai tayi ta nufi d’akin baccin na su, tana kama hannun k’ofar zata bud’e Utais na fitowa daga ciki, juyowa tayi tana fad’in “Yawwa, dama yallab’ai ne ya zo.”
Da fara’a ya k’araso kusa da inda Umad d’in ke tsaye, d’an rusunawa yayi alamar girmamawa yace “Barka da zuwa yallab’ai, zauna mana.”
Ba tare daya amsa gaisuwar ba ko kuma tayin zaman daya mi shi ya kalleshi yace “Ayam ta tafi Khazira, na yi k’ok’arin hanata amma bata hanu ba, jikina yana bani akwai matsala babba, shiyasa nake so na ji daga gareku ta ya zan shiga masarautar nan ba tare da na samu matsala ba? Sannan na fad’a muku zaku bar nan yau d’in nan.”
Kallon fuskarshi Habbee tayi da tsoro taf a fuskarta tace” Me kuma yake shirin faruwa da gimbiyarmu? Ya akayi ta yi wannan kuskuren?”