Hausa Novels

Lu’u Lu’u 23

Cikin nutsuwa Utais ya kalleshi shi ma yace” Gaskiya bansan ta wata hanya da zaka iya shiga ba tare da ka samu matsala ba, dan ko masu fitar da sirrin masarauta wad’anda aka sani ne kuma suke ciki shekaru da dama.”

Dafe k’ugu yayi yana nazari sai kuma ya jinjina kai yace” Ku shirya zan wuce da ku na aje ku sai na wuce.”

A d’an d’arare Utais yace” Zuwa ina kuma yallab’ai?”

Saida ya juya zai fita yace” Zaku tafi Egypt tare da sarki Abdallah, nan ne zaku fi samun tsaro da kulawa, ina jiranku a waje.”

Kallon juna sukayi saidai babu mai bakin magana, juyawa sukayi suka shiga d’akinsu dan tattara abinda zasu iya su wuce, dan wannan karan ma ai da sauk’i tunda shi zai tafi da su, waccen had’uwar ta su ta farko da saida ya gama tsoratasu da maganar yan sanda suka fita a gidan, suna hanyarsu ta zuwa wani wurin kawai mota ta tarbi gabansu aka ce su shiga, shi ne aka kawosu nan ba tare da sanin ina suke ba saida ya zo suka ganshi kad’ai hankalinsu ya kwanta.

*Khazira*

Da k’yar mutanen dake k’ofar gidan suka gusa aka shigo da motocin, Ayam da ke cike da zulumin abinda ta gani a d’akin Umad sai ta manta da komai tana kallon mutanen suna ta rububi da tururuwar lek’a a cikin motar kamar dai wacce ta aikata wani laifi yan jarida na son jin ta bakinta, motocin na shigewa masu gadin suka gaggauta mayar da k’ofar suka rufe, hakan yasa wurin k’ara kaurewa da hayaniya da cecekucen mutane.

Daidai k’ofar shiga b’angaren suka paka motar da take ciki, daga ciki da take zaune ta kalli k’ofar, dattawa ne a k’alla su bakwai cikin shiga ta alfarma, k’arewa fuskokinsu kallo take ta ga ko zata ga mahaifinta a ciki, bata ganshi ba sai Khatar data gani wanda ba zata manta fuskarshi ba, bud’e k’ofar motar da akayi yasa ta dawowa daga hangen data tafi.

A hankali ta zuro k’afarta mai d’auke da farin takalmi k’irar shelar na mata, yanda suka ma siririyar k’afarta kyau abun sha’awa, kafin ta zuro d’ayar dattawan nan suka juya suna kallon mai fitowa, ita ma bin bayansu tayi da kallo.

Take ta ji gabanta ya tsananta fad’uwa ganin mahaifin na ta, hular kansa da sandar hannunshi, ga wata kabceciyar sark’a a wuyanshi, hannunshi dake rik’e da sandar ya mak’ala wata agogo ga zabuna kuma kaf kayan nan duk narkakken gwal ne dan nuna alfahari da k’arfin mulkinshi, kyakyawar fuskarshi take kallo, shin gyara da kulawa ne yasa yake d’an matashi? Ko kuma dai matashin ne a gaske? Dan fuskarshi babu farin gashi ko d’aya, idonshi manya masu kyau da d’aukar hankali zagaye suke cikin bak’in kwalli daya masa rau a ido, shauk’i da kuma soyayyarshi da ta ji a lokaci d’aya yasa ta k’arasa fita a motar da sauri.

Tsaye tayi tana ta had’iyar kukan dake son kubce mata tana kallonshi har ya tsaya a kan matakalar, a hankali ya sauko k’afarsa kan matakalar ta farko, sannan ya sauko d’ayar ma a matakala ta biyu har ta d’aya inda sukayi kusa sosai, a hankali ta lumshe ido take kuma hawayen suka biyo kumatunta.

Tabbas gana jin soyayyar su Utais da kuma shak’uwa na wad’anda ta fara bud’a ido ta gani a duniya, amma soyayyar wad’anda take gani yanzu sai take sake gasgata abinda ake alak’anta ta da su d’in, kallon farko data musu take jin wata bayyanannar soyayyarsu a zuciyarta, sai ta kasance mai son zama da duka iyayen na ta dan ta ji me ke faruwa a cikin rayuwar ta? Tana son tasan asalin gaskiyar komai? Dan har yanzu kanta a kulle yake game da wasu abubuwan, musamman da aka ce mahaifinta ya rufe mahaifiyarta saboda ita, to saboda me?

*Wani* murmushin mugunta ya saki wanda ya sake bayyana kyawunsa, saida ya shanye komai dake zuciyarsa da fuskarsa a lokacin ya bud’e hannayensa da fara’a akan fuskarshi yace “Gimbiyata, ashe dama zan ganki ido da ido?”

Kamar wani ne ya ingizata sai kawai ta fad’a jikinshi ta fashe da matsanancin kuka tana fad’in “Pahhhh!”

Duk da idonshi k’amas suke ba alamar hawaye, amma haka ya k’ak’aro kukan makirci ya dinga kukan k’arya yana sake k’amk’ameta a jikinshi yana daddab’ata da fad’in ” ‘Yata, nayi kewarki sosai, na kasance cikin jiranki a kowace safiya, kowace fitowar rana kowane dare, nayi kewarki sosai.”

Ita ma k’amk’ame shi tayi tace “Ban sani ba Pah, bansan komai ba, Pahhhh!”

Raba jikinshi yayi da na ta a zahirance wani mugun kallo ya mata, amma sam Ayam bata d’auki haka a matsayin wata manufa marar kyau a zuciya ba, d’an juyawa yayi ya nunawa dattawan fadarshi ita yace “Ga ‘yata, ku gaisheta.”

Dukansu sai gani tayi sun rusuna kawunansu k’asa wasu na mata kirari da mai girma yar mai girma, wasu kuma suna gaisheta a ladabce musamman ma Khatar da baya fatan ta gane shi, da mamaki take kallonsu ta d’auka ai ita ce zata gaishesu da girmamawa saboda girmansu, tana cike da wannan mamakin ta ga ya sake nuni da hannunshi yace “Ki karb’i gaisuwa daga wajen jama’arki, shekaru suka d’auka suna bauta ga sunanki.”

Juyawa tayi inda yake mata nunin, take ta bud’e baki ta sake shi da alamar mamaki tana zazzaro ido, kafatanin fadawan gidan ne da hadimai da dogarai sama da guda d’ari suka jeru a bayanta kayansu kala d’aya duk sun k’ame sun rattab’e hannaye kamar wasu gunkaye, a tare duk suka rusuna kamar sunyi ruku’i suka fad’a a tare da “Barka da zuwa gimbiyarmu.”

Ganin babu wani yunk’uri da tayi yasea sarki Musail janyota jikinshi ya kwantar da kanta a k’irjinshi, a kunne ya rad’a mata “Ki musu murmushi, sannan ki d’aga musu hannu.”

Murmushin yak’e ta musu ta d’an d’aga hannu ta musu bye bye tace “H…hhi.”

Ta gefen ido ya wurga mata wata harara jin yanda muryarta ke rawa, jinjina kai yayi ya kalli fadawan yace “Gimbiyar Khazira mai girma Zafeera ta saka muku albarka, ku je ku ci gaba da ayukanku.”

Tare suka sake rusunawa suka ce “Godiya muke shugabanmu.”

Juyowa yayi da ita a hankali tana ga jikinshi har yanzu suka nufi ciki, had’a ido ta sake yi da Khatar hakan yasa ta nunashi da siririyar yatsarta tace “Kai ne?”

Da sauri ya rank’wafa yace “Ni ne ranki shi dad’e, tuba na ke, ki gafarce ki abisa abinda ya faru.”

Ajiyar zuciya ta sauke ta kalli k’ofar shiga falon da mahaifin na ta ke neman shiga da ita, k’arewa komai kallo take tana ganin ikon Allah, lallai anyi almubazzaranci wajen kera masarutar nan, dan kud’in da aka kashe abun har ya wuce d’aukar tunanin mai hankali, sai kuma yanzu ta yarda da abinda sarki Wudar ya fad’a ce wa idan ta zo msarautarta zata gani.

A babban gurin cin abincin suka zauna, duk da ta d’anyi kalle kalle a masarautar Giobarh da gidan Bukhatir, amma kam wannan gidan ya dame wad’ancen dole ta saki ido tana kallo, har aka kawo abinci aka zuba a plate na alfarma masu tsada da k’yalli bata sani ba tana ta kallon komai da take ganin kamar da gwal aka yi shi, dan ko kujerun d’aukar ido suke kuma kalarsu kalar ruwan gwal ne, shiyasa take ta tamtama da tunanin ko gaske ne ko kuma zubin ne aka musu na gwal.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button