Lu’u Lu’u 24

*24*
Tsoro matuk’a ya kamata ganin abinda y faru daga zuwanta, da an samu akasi kenan da ita ce zata mutu? Shin wane irin had’ari ne wannan a daidai wannan lokacin? Shin me yasa sai… Kafin ta sake tambayar kan ta ta ji sarki Musail ya shigo a rud’e yana nuna tashin hankalin k’arya, rumgumota yayi jikinshi yana duddubata yana fad’in “Gimbiya Zafeera kina lafiya? Ba abinda ya sameki dai ko?”
A raunane tace “A’a pah babu komai, saidai ita…matar ta mutu.”
Ta fad’a tana fashewa da kuka, shafa bayanta yayi ya sauke ajiyar zuciya yana feso iskan rashin jin dad’i, likitar agajin gaggawa dake cikin gidan ne suka fito da gawar a gadon arasa lafiya suka fita da ita, hakan uasa Ayam sake fashewa da kuka, shi kuma sai daddab’ata yake alamar tayi shiru.
Suna fita da gawar Zafreen na shigowa da saurinta ta kalli sarki Musail tace “Pah lafiya? Me ya faru?”
Girgiza kai yayi yace “Wani had’ari ne ya faru, sai dai abun ya zo da sauk’i tunda wata baiwa ce ta mutu ba ‘yata ba.”
Kallonshi Ayam tayi haka ma Zafreen Ayam ta kalla tana mai had’e fuska, cikin nuna kulawa Ayam tace “Pah ita ma fa mutum ce, kenan da ya zakuyi idan ni ce?”
D’an tsaki yayi daya nuna maganar ta haushi ta bashi yace “Karki damu da wannan, ki je kiyi wanka ki shirya.”
Sakinta yayi ya juya zai fita tayi saurin fad’in “Pah, idan so samu ne ina so na ga Mah d’ita yanzu, a zan iya wankan nan ba a yanzu dan na tsorata.”
Wani kallo ya mata tare da sakin murmushi yace “Tsoro? Ke d’in zab’abb’iyar Khazira?”
Fashewa yayi da dariya wanda hakan ya zama jikinshi sakamakon yawan ta’ammali da giya, kallonshi ta dinga yi sai ta ji tsoronshi na samun muhalli a zuciyarta yana zaunawa, saida ya ga dama dan kanshi ya tsagaita ya nunata da yatsa yace” Ke ce zaki bayar da tsoro abisa tsarin, amma ba dai ke kiji tsoro ba.”
Shafa kuncinta yayi yace” Ki samu ko huta, zaki ga Mah d’inki anjima.”
Da kallo ta bishi har ya fice a d’akin, a wulak’ance Zafreen ta k’yasta mata yatsunta tace” Malama ji nan.”
A hankali ta kalleta da idonta da suka d’auki launin ja mai duhu kad’an, matsawa tayi daf da ita a gadarance tace” Kina farin ciki ne saboda kin zo babbar masarautar Khazira? Hummmmm! To kar ma ki fara yarinya, dan farin cikinki nan gaba kad’an zai koma ciki.”
Ba tare da hayaniya ba Ayam ta sake kallonta tace” Me kike nufi?”
Murmushin gefen labb’a tayi tace” Ina nufin ni ce babbar ‘ya a msarautar nan, hakan na nufin ni ce magajiyar duka fada da kuma kujerar mulkin, dan haka ki gaggauta barin nan sannan ki manta kina da ahali a nan d’in, idan kuma ba haka ba nadama ce zata biyo baya.”
K’asaitaccen murmushi Ayam ta sauke ta rumgume hannayenta a k’irji ta gyara tsayuwarta tace” Da alama ke kuma abinda ya sha miki kai kenan, to ki sani ni ban ma san da wannan masarautar ba sai kwana biyu zuwa uku da suka wuce, infact har yanzu ban ji na gama yarda da cewa ku d’in ahalina bane, har yanzu zuciyata raya min take tatsuniya ake rad’a min a kunnuwana, sarauniya Juman ce kad’ai na ke son had’uwa da ita ta kuma tabbatar min, idan har ta tabbatar min da bakinta shi ne zan yarda da sauki burutsunku.”
D’auke hannayenta tayi daga k’irji tace” Shawara d’aya yar uwa, ki rage soyayyar nan da kike wa mulki, dan idan har kika sameshi alamu sun nuna giyarshi zata fi haukataki.”
Sama da k’asa ta harareta tare da jan dogon tsaki ta fita a d’akin tana fad’in” Matsalarki ce kuma wannan.”
Da kallo kawai ta bita a zuciyarta tana fad’in” Ke ma zata zama ta ki nan gaba kad’an.” Fita tayi a d’akin ita ma ta koma falo ta zauna jiran tsammani.
Ta jima zaune ita ba kallo ba ita ba bacci ba har saida aka k’wank’wasa k’ofar d’akin, da sauri dan dama ta k’agu da zaman tace” Shigo.”
Bud’ewa akayi aka shigo, cikin ladabi hadimar ta sunkuya tace” Ranki shi dad’e, sarkina ne ya umarceni da na rakaki zuwa sama dan ganawa da mutanen gari.”
Da mamaki tace” Sama kuma?”
Yar fara’a tayi tace” A saman bene nake nufi.”
Mik’ewa tayi tana fad’in” Oho.”
Fita sukayi suka bi ta matakala, suna kan tafiya a hawa na uku suka had’u da d’aya daga cikin dogaran gidan, rab’ewa sukayi dan hanyar ba wata mai fad’i bace, kamar Ayam ji tayi ya damk’a mata abu a cikin hannunta, abun mamakin kuma bai kalleta bai sai rusunawa da yayi saboda sanin matsayinta ya gaisheta kai tsaye kuma ya wuce abin shi.
Ganin hadimar tayi gaba bata kula bda komai ba yasa Ayam bud’a tafin hannunta, k’aramar waya ce mai kyau fara sol da ita mai murfi k’irar Samsung, da mamaki take kallon wayar ta sake juyawa ta kalli mutumin har ya sauka, “Waye shi?” Shi ne abinda ta tambayi kanta ta bi bayan hadimar nan kawai tana sake jimk’e wayar a hannu.
A saman fili ne da shi ma aka k’axatashi dan shan iska, wata k’ofa ta bud’e ta d’auka wani wurin zasu shiga, sai gani tayi kawai ashe titi ne zaka iya hange, kamar jira suke dama sai kawai ta ji ihun da saida ta zabura ta rike hannun hadimar nan, d’aruruwan mutane da suka taru dan ita, da mai kyakyawar niyya da mai akasin haka dukansu, gashi sai ihu suke suna d’aga mata hannu alamar jin dad’in ganinta.
Cikin girmamawa hadimar tace “Duk dan ke suke nan ranki shi dad’e, shekaru wasun su suka kwashe suna fatan bayyanarki, dayawa sun ci buri akan dawowarki da sa ran sabon tsarin da zaki kawo musu, daga cikin talakawan nan akwai wad’anda suke sadakar abincinsu dan abun bauta ya kareki a duk inda kike sannan ya dawo musu dake lafiya.”
Da mamaki Ayam ta kalleta tace” Mutanen da sukayi sadakar abinci saboda ni, kuma shi ne za’a bani izinin ganinsu daga nesa?”
Gyara tsayuwa tayi ta had’e fuska wanda ita kanta bata cika sanin tana kama jikin nan ba tace” Muje ki kaini ta inda zan gansu ga da ga.”
Kallonta hadimar tayi da niyyar yi mata gardama, sai kuma ta sake rusunawa jikinta na b’ari tace” Ranki shi dad’e izinin da mai martaba ya bani kenan, idan na sab’a masa zai iya hukunta ni.”
Saida ta gama saurarenta tas tace” Ki kaini na ce.”
Jinjina kai tayi jiki na kyarma ta rufe wannan k’ofar ta juya bayanta, ita a Ayam juyawa tayi sai ta ga ta bud’e wata k’ofar, rab’ewa tayi tace” Muje tanan ranki shi dad’e.”