Lu’u Lu’u 25

Jinjina mata kai tayi ita ma tana kukan tace “Tabbas ni na d’aura miki ita da hannu na a lokacin dana haifeki.”
A hankali tace “To amma me yasa?”
D’an murmushi ta k’ak’aro tace “Saboda ta zama tsaro a gareki, sannan shaidar da zan iya ganeki ko a cikin dubu, sannan hujjar da zan iya nuna miki cewa ni na haifeki.”
Fashewa tayi da kuka mai ban tausayi ta saki sark’ar daga hannunta tace “Me yasa kika rabani da ke a lokacin da na fi buk’atarki? Me yasa kika zab’i kiyi nesa da ni a sanda zamanmu a tare shi ya fi komai mahimmanci?”
Da sauri Juman ta saki towel d’in take rik’ewa hakan ya bayyanar da wuyanta dan d’aurin k’irji ne jikinta na farin towel babba, rumgumeta tayi tsam a jikinta suka fashz da wani sabon kukan, cikin magiya take fad’in” Kiyi hak’uri ‘yata, ban yi haka dan bana sonki ba, da banyi abinda nayi ba da yanzu ba kya raye, idan kuma kin rayu to da kin sha wahalar da ni kuma ba zan juri ganin kina shan ta ba, shiyasa nayi nesa dake dan ki rayu cikin aminci, sannan ki zama mai kyawun d’abi’a da ba irin na mahaifinki da ‘yar uwarki ba.”
K’am k’am Ayam ta rik’eta tana sauke ajiyar zuciya da fad’in” Na fahimta Mah, na fahimceki Mah na.”
D’agota tayi daga jikinta ta kalli fuskarta ta hanyar d’aga hab’arta tace” Kin yafe min kenan?”
Langab’e kai tayi tace” Ban rik’eki ba Mah, ina sonki sosai.”
Ta fad’a tana sake komawa jikinta, ita ma matseta ta sake yi tana murmushi, daga bayansu jakadiyar sarauniya Juman ce tace” Ranki shi dad’e na fito miki da kayan da kika buk’ata.”
Cikin shagwab’a da sangarta Ayam ta bud’a ido ta kalli jakadiyar tace” Babu mai rabani da Mah ta, anjima ta saka.”
Dariya jakadiyar tayi haka ma Juman data d’agota daga jikinta tace” Sai yaushe kenan? Nayi ta zama a haka?”
Rik’o hannayenta Ayam tayi tana mamatsawa musamman ruwan zafi’ da tayi wanka da su yasa duk fatarta tayi taushi saboda rashin samun lafiyayyar shinfid’a a kurkukun nan, cikin shagwab’a tace” Mah, zaki zauna tare da ni ko? Akwai abubuwa dayawa da nake son tambayarki, ina rok’onki ki zauna tare da ni kuma ki amsa min, dan babu mai fad’a min gaskiya har yanzu.”
Jawo hannunta tayi ta zaunar da ita bakin gado sannan ita ma ta zauna, kallon jakadiyar tayi tace “Ku je jakadiya, zan nemeki anjima, yanzu lokacin ‘yata ne.”
Rusunawa sukayi tace “To sarauniyata, mun barku lafiya.”
Dukansu suka fita kafin sarauniya Juman ta maida hankalinta kan Ayam tana murmushi tace “Ya kika rayu ba tare da ni ba?”
A take tace “Cikin aminci, k’auna da soyayya.”
Jinjina kai tayi tace “Kin tabbatar kin rayu babu barazanar talauci?”
Girgiza kai tayi tace “Babu Mah, sun ciyar dani da dad’i da ba dad’i, sun d’auki nauyin karatu na har zuwa sanda gwamnati ta d’auke musu nauyin, sun tufatar da ni iya iyawarsu.”
Jinjina kai ta sake yi tana k’asaitaccen murmushi kafin tace “Game da lafiyarki fa? Babu abinda ke damunki?”
Girgiza kai tayi kafin tace “Babu Mah, idan da akwai ciwon dake damuna bai wuce yawan mafarkai ba tun ina k’arama, shi ma yanzu kuma na fahimci wa nake gani a mafarki na.”
Cikin zolaya ta lak’aci hancinta tace “Wa kike gani haka? Ko dai sirikin na wa ne?”
Dariya tayi tana rufe fuskarta da tafin hannu tace “Lahhh! Mah ki daina.”
Dariya tayi ita ma kafin tace “To fad’a min wa kike gani?”
Bud’e fuskarta tayi ta d’ago tace “Ke ce Mah, ke nake gani kullum kina neman taimako na, bansan me hakan ke nufi ba?”
Numfasawa tayi ta rik’e hannunta gam suka kalli juna, a sanyaye tace “Ayam…”
Da mamaki ta kalleta da sauri kuma tace “Ya akayi kika san sunan dana tashi ina amsawa? Tunda na baro Larhjadin yallab’ai Umad ne kad’ai ke kirana da sunan.”
Dariya tayi har saida hak’oranta suka bayyana sannan tace “Saboda ni na fad’awa Habbee ta rad’a miki sunan *Ayam*, sunan dake birgeni kenan tun da jimawa, na so sakawa yar uwarki Zafreen, amma sai mahaifinku ya zab’a mata sunan Zafreen.”
Dafa kafad’arta tayi tace “Mafarkin da kika kasance kina yi ni na fara yin shi na tsawon lokaci, amma ina haihuwarki komai ya wuce.”
K’asa tayi da kan ta tana sakin murmushi tace “Umad? Umad?”
Sai kuma ta kalli Ayam tace “Ta ya kika san Umad? D’a ga sarki Wudar.”
Da mamaki ta kalleta tace “Ya akayi kika san shi Mah?”
Sosai tayi murmushi kafin ta kalleta tace “Yanzu dai ki bari na saka kaya, daga baya zamuyi magana bayan na ci abinci.”
Kyab’e fuska tayi ta ware hannayenta ta rumgumo Juman d’in tare da fad’in “Mah bana so kiyi nesa da ni ko na sakan d’aya, please ki zauna tare da ni.”
D’ago hab’arta tayi tace “Wai tsaya ban tambayeki ba, ta ya kika iya yaren slovaque? Su Habbee ne suka koya miki?”
Girgiza kai tayi a harshen larabcin parsi tace “Ko d’aya Mah, kawai dai na iya ne saboda ni yar garin nan ce asali.”
Da mamaki ta waro idonta tace “Hada yaren k’asar haihuwata ma kin iya?”
A harshen faransanci tace “Oui m猫re (e mahaifiya ta).”
D’aga hannaye tayi ta dafe kanta tace “Tsaya tsaya! Wai me ye haka? Ta ya kike yaren nan a bakinki?”
Zaune tayi da kyau tace “Ki je ki kammala duk uzurinki, sai muyi magana daga yanzu har wata safiyar.”
Kallon tuhuma sa kuma tsoro ta mata tace “Kin tabbatar?”
Jinjina mata kai tayi tace “Na tabbata.”
Mik’ewa tayi ta nufi wajen kayan da aka fito mata da su ta shiga k’ok’arin sakawa, Ayam duk na zaune tana kallo ta shirya a tsanake babu mai cewa komai, saidai jefi jefi sukan kalli junansu suyi murmushi, kowa na jin zuciyarsa na masa wani iri game da d’an uwansa.
Har ta gama shiryawa ta nufi wajen zaman mutum biyu gaban teburin da aka jere mata abinci mai rai da lafiya, kallon Ayam tayi ta mata alama da hannu ta taso, mik’ewa tayi ta nufeta ta zauna kusa da ita, zuba abincin tayi sannan ta kalleta tace “Mu ci.”
Da fara’a ta tsoma hannunta ba cokali ba ta d’ebo loma ta nufi bakin Juman, da fara’a ita ma ta bud’e bakin ta saka mata, ita ma d’iba tayi ta saka mata hakan yasa su sakin murmushi.
Cikin farin ciki da jin dad’i da annashuwa suka dinga ciyar da junansu amma ba hira suke ba sai k’orafin da suke wa junansu na sun k’oshi, amma a haka Juman zata sake jefa mata loma a baki, sai ita ma tace sai ta rama haka har suka cinye wanda suka zuba a farantinsu.
*Alhamdulillah*