Hausa Novels

Lu’u Lu’u 26

A hankali tace” To amma Mah, idan har kunyi soyayya irin haka da mahaifina, me yasa ya manta da komai ya jefaki a magark’ama saboda ni?”

Dariya Juman tayi har saida hak’oranta sirara masu kama dana Ayam d’in suka bayyana, girgiza kai tayi tace” Ayam kenan, yarinya ce ke har yanzu.”

Da mamaki tace” Kamar ya Mah, ni fa na girma.”

Ta fad’a tana kumburo baki, dariya ta sake yi tace” Ayam ba haka abun yake ba, a shekara ta 1985 sarakunan gargajiya sunyi taro na musamman dan sake hab’aka zumunci da kawar da bambamce bambamce a tsakanin k’asashen, sarkin Egypt wato mahaifina, da sarkin Khazira wato mahaifinki, da kuma sauran sarakuna daga ciki har da sarki Wudar na Giobarh, duka sun hallara a wannan babban taron wanda mahaifina shi ne mai alhakin sauke bak’in, ma’ana a k’asarmu aka gudanar da taron, kwana uku aka d’auka ana wasanni kala daban daban, a na ci a na sha cikin farin ciki da annashuwa, b’angare d’aya kuma sarakuna na gudanar da abinda ya kawosu.”

Numfasawa tayi ta d’an gyara k’afarta data tank’washe sannan ta ci gaba da fad’in” A kwana ukun da akayi na kamu da soyayyar wani d’an baiwa, kinsan me yasa na kirashi da d’an baiwa? Saboda shine zakin daya fara sace zuciyata, da kallo d’aya ya birgeni ya kuma shiga zuciyata, lokacin da nake jin dad’in satar kallonsa ina tunanin hanyar da zan fad’a masa abinda ke zuciyata kafin su bar k’asar, sai ya turo da k’aramin k’aninsa mai shekara shida a duniya ya fad’a min wai shi ma yan so na.”

Damk’e hannun Ayam tayi sosai tana jijjigawa cike da farin ciki tace” Kin kuwa san irin farin cikin da na kwana ina yi a ranar? Na ji kamar duniya aka bani da komai dake cikinta, saidai kash! Ban tab’a tunanin wannan bak’in taro ne a gareni ba saida Musail ya shigo rayuwata, ki gafarceni idan kin ji ba dad’i Ayam saboda soyayyar d’a da uba, amma dai tabbas ban ji dad’i ba.”

A sanyaye Ayam tace” Me ya faru Mah?”

Girgiza mata kai tayi tace” A’a Ayam, bana so daga had’uwarmu na zauna na yi ta fad’a miki mugayen halayen mutanen dake zagaye da ke.”

Rik’o hannunta tayi tace” Please Mah, ki daure ki fad’a min komai, na fad’a miki mutanen da ban sani ba suna kawo min farmaki ta hanyar rikita min k’wak’walwa, ina so na san komai daga gareki, hakan shi ne zai cire min kokonto na akan kowa da komai.”

Girgiza kai tayi tana sako da hawaye a idonta tace” Ba zan iya fad’a miki wannan ba Ayam, ki gafarce ni.”

Jinjina kai tayi alamar gamsuwa tace” To shikenan na ji, amma ki fad’a min waye wanda kika so a zuciyarki? Sannan ki fad’a min me ya hana aurenku?”

Murmushi tayi tace” Ayam ai idan na fad’a miki abinda ya hana aurenmu an gudu ba’a tsira ba kenan, dan abinda ya hana auren na mu shi ne abinda bana son fad’a miki.”

Jinjina kai ta sake yi tace” To na ji, waye shi?”

Saida ta saki sanyayyan murmushi tace” Sunansa *Urab*, babban d’an sarki Wudar.”

Zazzaro ido tayi tace” Sarki Wudar Mah?”

Jinjina kai tayi tace” E, d’an sarki Wudar.”

Da mamaki a fuskarta tace” Hakan na nufin yaya ne ga yallab’ai Umad? Dama ‘ya’yan sarki biyu ne?”

Gyad’a mata kai tayi tace” E, su biyu, Umad d’in ai shine k’aramin k’aninsa da nake fad’a miki.”

Juyar da kanta tayi gefe a ladabce tace” Kenan yallab’ai Umad sosai ya sanni ba sanin shanun talla ba? Kenan tabbas saboda ni ya je makarantar nan? Kuma mahaifinsa ya san wacece ni, amma kuma duk da haka yake cewa yana son…”

Shirun da tayi yasa Juman saurin fad’in” Yake son me? Kin had’u dasu dukansu? Ta ya ya?”

Girgiza kai tayi dan bata san me hakan zai janyo ba kafin tace” Ba komai Mah, na zauna tare da su na kwana biyu.”

Tsaf ta kwashe abinda ya faru ta fad’a mata, sai daga bisani kuma ta kalleta a tsanake tace” Mah, to ina shi yayan yallab’ai d’in yake? Ko gidansu dana zauna ban ji ko da labarinshi ba.”

Kallonta tayi sosai ita ma a tsanake tace” Ya rasu shekara ashirin da hud’u da suka gabata.”

Dafe k’irji tayi tamkar mahaifinta aka ce ya mutu tace” Me?”

Jinjina mata kai tayi alamar e, girgiza kai tayi kamar zatayi kuka tace “Amma ta ya Mah?”

Girgiza mata kai tayi tace “Kinga yanzu dai manta da wannan, bana so ki sa kanki a damuwa, yanzu bani labari game dake?”

“Kamar me kenan Mah?” Ta fad’a kamar mai rad’a, jan hancinta tayi tace “Kamar k’awayenki, samarinki, karatunki, matsayin addininki a gareki.”

Bushewa tayi da dariya tace “Mah, a b’angaren karatu na dai kam zan iya miki albishir da ce wa tun dana fara daga ajin farko zuwa inda nake yanzu, indai za’ayi jarabawa to ni ke zuwa farko, k’ok’ari na ma yasa har idon gwamnati ya zo kai na suka dinga d’aukar nauyina.”

Rausayawa tayi ta ci gaba da fad’in” Kawaye kuma ni kam ban da tsayayya, duk k’awayen makaranta ne, da zaran mun rabu to shikenan ni da su sai ko kan hanya idan an had’u.”

Cikin jin kunya tace” samari kuma…ban tab’a yi ba Mah, ko na wasa.”

Jin tayi shiru yasa Juman fad’in” To addininki fa? Me ye matsayinsa a gunki?”

Waina idonta tayi tace”…

 

*In shaa Allah sai litinin kuma*

 

*Alhamdulillah*

The post Lu’u Lu’u 26 first appeared on 2gNovels.com.ng.

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button