Hausa Novels

Lu’u Lu’u 27

Da giramawa ya fad’i “Hakane ranka shi dad’e, Allah ya k’ara maka lafiya da nisan kwana.”

“Ameen.” Sarki Abdallah ya fad’a yana jinjina kai a hankali, shiru motar ta d’an d’auka na wani lokaci kafin sarki Abdallah yace “Bukhatir, ka san me yasa na ta so da kai na na zo yanzu?”

Girgiza kai yayi yace “Ban sani ba mai martaba, sai dai na shiga zulumi da tunanin me ya hana sarkina zaunawa a d’akinshi na alfarma ya jira na d’an lokaci ni na sameshi.”

Jinjina kai sarki Abdallah yayi yace “Hakane, abu ne mai mahimmanci da ya shafi rayuwata, shiyasa na kasa hak’ura gari ya waye.”

Numfasawa yayi a hankali yace “Bukhatir, ka san da na had’u da ‘yar’ yata wato d’iyar Juman Zafeera?”

Da sauri ya d’ago kai ya zuba idonshi cikin na shi, amma da sauri ya sadda kan shi yana mai jin gabanshi na tsananta fad’uwa, hatta da jikinshi saida ya ji ya fara kyarma zai d’auki rawa, yanda ya kasa furta komai yasa sarki Abdallah d’ora da fad’in” Na had’u da ita, kuma na yi farin cikin haka, saidai akwai wata babbar matsala.”

Da k’yar ya bud’i bakinshi yace” Sarkina wace irin matsala kuma?”

Jim sarki Abdallah yayi sai kuma yace” Kamar yanda ka sani ne daga haihuwarta zuwa yanzu ta rayu cikin had’ari, amma ubangiji yana kareta daga sharri duk wani mai sharri, ban tab’a jin d’ar a lokacin da aka rasata ba, amma a yanzu ina jin zuciyata ta kasa samun sukuni saboda inda ta kai kanta.”

A ladabce Bukhatir yace” Ina ta kai kanta haka ranka shi dad’e?”

Shiru sarki Abdallah yayi kamar ba zai yi magana ba, can ya numfasa yace” Wajen mahaifinta, sarki Musail.”

Da sauri ya kalli sarki Abdallah duk da dai yasan da maganar, amma dan kar ya saka mishi wani shakku yasa shi fad’in” Wajen sarki Musail? Kasheta fa yake son yi?”

Jinjina kai yayi yace” Sanin haka yasa hankali na ya kasa kwanciya.”

Shi ma jinjina kai yayi tare da tunanin bari ya fad’a masa shawarar da shi kan shi ya yanke a kan ta d’in, kallonshi yayi a hankali yace” Sarki na, kwanciyar hankalinka shi ne kwanciyar hankalin duk wani dake k’asar nan, ka kwantar da hankali, ni na ma ka alk’awarin zuwa safe zan samo maka labarin yanda take ciki, daga haka kuma sai mu san abun yi, dan gaskiya zamanta a can akwai had’ari.”

A tsanake ya kalleshi yace” Ka tabbata zaka iya yi min haka Bukhatir?”

Jinjina kai yayi yace” In shaa Allah sarki, wannan alk’awari na ne a gareka.”

Jinjina kai yayi a hankali yace” Shikenan Bukhatir, na yarda da kai, ina jira na ji daga gareka.”

Da haka suka rabu ya fito a motar su kuma su ka bar unguwar yana mai jin ya fara samun nutsuwa a zuciyarshi.

 

_Ga duk wanda bai siyi *lu’u lu’u* ba ya hanzarta ya siya dan fara samun *Badak’ala* nan kusa_

 

*Alhamdulillah*

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button