Lu’u Lu’u 29
*29*
Kamar jiranshi ake ya koma b’angaren shi Adah ya mik’o masa wayarshi yace “Yallab’ai ana kiranka a waya.”
Kallonshi yayi kafin ya sa hannu ya karb’a ya duba lambar da babu suna, k’arasawa yayi cikin falon ya nemi guri ya zauna tare da aje wayar gefenshi har ta tsinke, a tsanake Adah ya kalleshi yace “Ranka shi dad’e, na ga har kiran ya tsinke baka d’aga ba?”
Yatsin fuska yayi yace “Bak’uwar lamba ce.”
Cikin ladabi Adah yace “Hakane ranka shi dad’e, amma akwai yiwuwar wani mai mahimmanci ne, duba da lambarka ce ta manyan mutanenka.”
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce wani abu sai kiran ya gajeren sak’o ya shigo wayar, kallon Adah yayi yace “Duba ka gae aka ce.”
D’auka yayi ya duba kamar yanda ya ce, da sauri ya kalleshi yace “Yallab’ai, *Abraham Joshua* ne fa, komishinan kud’i da kake shirin yanda zaku tattauna da shi.”
Da sauri ya zura hannu ya karbi wayar yana k’ok’arin maida kiran yana fad’in “Ka tabbata? Abraham Joshua?”
Kiran da ya sake shigowa yasa sarki Musail kallon wayar, jim yayi bai d’aga ba na yan dak’ik’u, daga bisani kuma sai ya d’aga, Adah na gefe yana kallonshi jin yanda suke gaisawa kamar sun san juna dama, bayan gaisuwar ne Abraham ya d’ora da “Ranka shi dad’e sarki na, dama wata muhimmiyar magana ce ta sa na kiraka.”
A tsanake shi ma ya amsa da “Muhimmiyar magana kuma? To ina jinka, Allah yasa dai lafiya?”
Da fara’a yace “Ah lafiya lau, dama d’an waje na ne ya ke fad’a min ya ga d’aya daga cikin ‘ya’yanka kuma ya na so.”
Shiru yayi daga haka na dak’ik’u sannan ya d’ora da “To na amince masa ya nemi aurenta a wajenka, saidai ya cika sauri dayawa, da na fad’a masa zamu je tare nan da kwana biyu bayan na dawo daga tafiya, sai ya nuna bai yarda da hakan ba, ‘ya’yan manya a kowane lokaci farautarsu a ke, dan haka ya ce shi zai fara zuwa a yau, ni sai na zo daga bayan.”
Numfasawa yayi sosai sannan yace” Fatan dai ba muyi gaggawa ba ranka shi dad’e?”
K’urawa Adah ido yayi yana kallo tare da shiga kogin tunani, hark’allar da yake son k’ullawa da kwamishinan kud’in ta isa ta sa ya amince masa, dan haka ya d’an murmusa yace” Ok, wannan ai ba matsala ba ne, ya zo kawai, nan ma kamar gidan su ne.”
Numfashi ya sauke kusan sau uku kafin yace” Amma…wace a cikin gimbiyoyin na wa?”
A hankali yace” E to…ina jin dai kamar k’aramar.”
Jim sarki Musail yayi sai kuma ya tab’e baki a ranshi yake fad’in” Idan ta zama gawa kafin nan sai a maida auren kan gimbiya Zafreen.”
A zahiri kuma murmushi yayi ya amsa da ba komai kawai sai sun zo, har da tagomashin fad’in” Zan tura dreba ya je ya d’aukoshi.”
Da sauri Abraham yace” Yallab’ai sai dai ba shi kad’ai ya taho ba, tare yake da mai tsaron lafiyarsa.”
Jinjina kai Musail yayi yace” Wannan ba damuwa bane, ko su na wa zasu zo akwai masaukinsu.”
Suna Ida wayar ya kalli Adah yace” Ka kula da komai Adah, ka tura dreba ya d’aukosu a filin jirgi, sannan ka sa a shirya musu tarba ta musamman, dan neman aure zasu zo.”
Da sauri Adah ya kalleshi cikin ladabi yace” Ranka shi dad’e a gafarce ni, amma neman auren wa daga cikinsu?”
Ba tare daya kalleshi ba yace” Zafeera.”
Da mamaki yace” Zafeera kuma? Ranka shi dad’e wacce muke shirin turata wata duniyar, me ye hikimar yin hakan?”
Wani lallausan murmushi yayi yace ” Ka zuba ido kawai ka sha kallo.”
Rusunawa yayi ya jinjina kai tare da fad’in” Na barka lafiya sarkina.”
*Suna* zaune d’akin Juman hadimai biyu suka shigo da farantan abinci, Ayam dake duba zoben da Juman ta nuna mata na azurfa wanda ta ce Urab ya bata shi, ajeshi tayi kan k’aramin teburin, suna zuwa su ma suka aje kwanukan akan teburin, a tsanake Juman ta kallesu tace “Me aka dafa yau?”
Cikin ladabi d’ayar ta shiga bud’e mata kwanukan dan ta gani da idonta, murfin kwanan ta aje a k’asan zoben, hakan yasa Ayam data gani tace “Mik’o min zoben nan?”
D’aukowa hadimar tayi ta mik’o mata, karb’a tayi saidai sub’utar hannu yasa zoben sub’ucewa ya fad’a cikin farfesun kifin da ke kusa, da sauri Ayam ta furta “Oh Allah.”
Da sauri hadimar ta d’auki cokali tana fad’in “Oh! Sannu gimbiya, bai fallatsar miki ba?”
Girgiza kai tayi tace “A’a, ki gaggauta ki ciro shi.”
Cokalin ta sa ta d’auko zoben nan na azurfa, abun mamaki ya canja kala yayi bak’i sid’ik, sam Ayam bata fahimci me sauyin zoben ke nufi ba, amma Juman da ta san komai tuni ta mik’e tsaye tana dafe da k’irjinta tace “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un.”
Kallonta Ayam tayi tace “Mah, me ya faru? An ciro shi ai.”
Hankali tashe tace “Ayam baki gani bane? Guba ce a abincin nan.”
Zabura tayi ita ma ta mik’e tsaye tace “Guba kuma? Ta ya mah?”
Nuna mata zoben tayi da hannun hadimar har ya fara rawa tsabar kad’uwa tace “Dubi zoben mana ki gani, ya canza kala.”
Kallon zoben tayi sannan ta kalli hadiman tace “Ta ya haka ta faru? Wani ne ke sonkashe min uwata?”
Girgiza kai sukayi a tare alamar a’a suna neman fashewa da kuka, cikin tsawa Juman tace “Yanzu da ku za’a had’a baki a nemi kashe min ‘yata? Me ta muku? Wa ya saka ku? Me aka baku da ni ba zan iya baku ba?”
Kallonta Ayam tayi a nutse tace “Mah, kwantar da hankalinki.”
Kallon hadiman tayi tace “Ku d’auke abincin ku fita da shi, ku fad’a musu Allah ya fi su.”
Cikin rud’u Juman ta fashe da kuka tace “A’a Ayam, dole mu san…”
Matsawa tayi kusanta ta rumgumeta tace “Shiiii! Ya isa Mah, ki nutsu kin ji, ki bar min komai a hannu na.”
Jinjina kai tayi tana sauke numfashi ta bi hadiman da kallo da su har ga Allah basu san ta ya haka ta faru ba.
D’agowa tayi daga jikin Ayam tace “Bari na je da kai na na samo mana ko da kayan marmari ne, daga yanzu ba zamu sake yarda da kowa ba.”
Jinjina kai tayi alamar to, zaune tayi bakin gadon inda Juman ta fita a d’akin dan samo musu abin ci.
*Giobarh*
Tana kwance kan doguwar kujera da wayarta tana amsawa, cike da kissa take farfar da ido tana fad’in” Haka ni ma na yi kewarka waziri na, yanzu ka fad’a min yaushe zamu had’u?”
Daga wajen wanda ta kira waziri ya amsa da” Ina so mu had’u Joy, sai dai dole mu dinga taka tsantsan, kinsan fa abubuwa sun fara canjawa, musamman yanzu da shegiyar yarinyar nan ta bayyana garemu.”