Hausa Novels

Lu’u Lu’u 29

Yar dariya tayi tace” Da alama tsoronta ya gama tasiri a zuciyarka, ai ban sanka da tsoro da sarewa ba, k’aramar yarinya ce fa? Ubanta ma ya ya iya da mu bare kuma ita?”

Jinjina kai yayi daga inda yake yace” Hakane, amma kinsan ita daban ce, a gaskiya bana iya d’aga idanu na a gaban yarinyar nan, kwarjininta ya fi na ubanta Musail, kamar…wata zakanya haka nake ji idan na ganta.”

Tsaki tayi ta tashi zaune tana fad’in” Ya isa haka malam, ya kake so ka nuna min ka fara sarewa da lamarin, kana so kace kenan mu hak’ura da burinmu?”

A sanyaye yace” Ko bamu hak’ura ba Joy do’e dai mu bi a hankali.”

A hassale tace” Ba zamu bi d’in ba, zamu tafi da gudu dan cika burinmu, ta jima ba tayi abinda za tayi ba, kar ka manta shekara ashirin da shida mun aikata abinda har yanzu babu uban daya ganemu bare ya d’aga canzan, kuma idan akwai wanda za’a zarga a ciki sarki Musail ne.”

Numfasawa yayi yace” Na san da wannan, matsalata da ke garaje, Joy hanyar da muka bi muka aiwatar da waccen tsarin, idan kika bi a hankali wannan ma haka zamuyi.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Shikenan na ji, yanzu ya zamuyi da kai?”

A hankali ya amsa mata da “A game da me fa? Halan kud’i kike so?”

Yatsina fuska tayi tace “E mana, kai ma kasan ai zan buk’aci kud’i, tunda Wudar ya juya min baya saboda banzar yarinyar nan.”

Numfashi ya sauke yace “Shinkenan na ji, zan turo miki anjima, dan nasan wajenku yanzu dare ne.”

A sangarce ta amsa da “Hakane, shikenan sai na ji ka.”

Aje wayar tayi a gefe ta koma ta kwanta ta lumshe ido tana tunanin abubuwan da suka aikata masu yawan gaske ita da waziri Khatar d’in, wanda ba komai ya jawo haka ba sai soyayya, asali a makaranta suka fara soyayya a babbar jami’ar Khazira, a k’arshe sai iyayenshi suka zab’a mishi mata yayi aure, dan dama shi da ita soyayyar shan minti ce aka buga, duk da auren da yayi su kan ziyarci juna su kuma sha soyayyarsu, tsawon lokaci kuma bayan irin kitimurmurar da suka k’ulla ne na son cikar burinsu sai ta koma Giobarh wajen yayarta tana kula da ita.

Yanda ta ji an d’ora hannu a k’irjinta yasa ta zabura ta tashi zaune tan kiran “Kai! Waye…”

Sarki Wudar ne tsaye gabanta cikin saussauk’ar shigarshi ta kayan bacci, hular dake kan shi kuma ta tabbatar mata akwai abinda yake so gareta shiyasa ya shigo ta b’arauniyar hanya zuwa wajenta, had’e fuska tayi ta kauda kai daga gareshi ba tace komai ba.

Murmushi yayi tare da zaa gefenta ya jawota jikinshi yana sumbatar kumatunta yace “Oh my madam, me ya faru ne haka ake had’e min fuska kuma?”

Tureshi tayi da k’arfi cikin masifa tace “Me ma ya faru kake tambaya ta? To ban sani ba, ka ga tashi ka fita daga d’akin nan.”

Sake jawota yayi cikin dubara ya zura hannunshi kan mamanta dake babu bras a cikin rigar bacci, farin gemunshi ya fara shafa mata a kafad’a, inda bakinshi ke kan kunnenta yana rad’a mata” Haba sarauniyata, me yasa za ki fad’i haka? Ni ne fa, sarkinki.”

K’ok’arin kubcewar da tayi yasa shi sake k’amk’ameta a jikinshi, mayar da hannunshi yayi kan mararta ya shafa, tauri da kuma d’umin da take ji a wurin da neman mai tallafa mata a lokacin yasa ta lumshe ido ta sauke numfashi.

Cikin dakusashiyar murya ta furta “Me yasa ka dinga wulak’antani a kan ta?”

A hankli ya shiga sauke numfashi a cikin kunnenta ya rufe ido shi ma, a zuciyarshi ya amsa mata da “Saboda ta fiki komai a wajena, da ita zan kai matakin da babu wanda ya zata a duniya.”

A zahiri kuma cikin taushin murya yace “Kiyi hak’uri kin ji, ai yanzu bata nan.”

Cikin fad’a tace “Amma ai na ji labarin kun yi alk’awarin aure da ita, ko ka d’auka ban san me ake ba ne a gidan?”

Jim yayi da tunanin a sanda sukayi maganar nan wa ya ji? Sai kawai ya share dan yasan kad’an daga aikin gidan masarauta kenan, cikin gurnani na abinda ke damunshi wanda shi ya kawoshi nan ya sake zura hannu yana shafa mamanta yace” Rabu da kowa kinji, ki kwantar da hankali yanzu, kinsan fa ba ke kad’ai ba ce ko?”

D’ago kanshi yayi yace” Yanzu tashi mu je ciki ki ga wani abu.”

Matsawa tayi daga gefenshi tace” Ka ga malam, ni ba yarinya ba ce da zaka min wani banzan wayo kamar wata yar talla, na san me ya kawoka wajena kuma ban da buk’ata ni.”

D’auke kai tayi daga gareshi tace” Sai ka je can figaggiyar Zafeera ta ke ko wa? Ta sauke maka abinda yake damunka.”

Mik’ewa tayi tsaye d’auki wayarta sannan ta kalleshi ta sake fad’in” Ko kuma ka je nakasashiyar matarka ta biya maka buk’atar, amma ni ma daga yanzu na san ciwon kai na.”

Tana gama fad’a ta juya da sauri ta shige d’akin baccinta ta rufe da makulli, da kallo ya bita har ta rufe k’ofar, tab’e baki yayi ya mik’e yana d’an girgiza kan shi, to in banda abun Joyran ma ta ya sarki zaki fad’a masa haka? Gidan nan da ke cike da bayi da hadimai.

D’akinshi ya koma inda ya samu d’aya daga cikin masu tsaron k’ofar shi ya kirashi zuwa ciki, bayan sun zauna ya nutsu ne yake fad’a masa “A cikin hadiman gidan nan wacece ka yarda da tsaftarta da kuma rik’on sirrin ta?”

Sadde kai ya sake yi cikin girmamawa yace “Wajen tsafta kam ba za’a rasa ba ranka shi dad’e, a ge da rik’on sirri dai ne bamu da tabbas, amma zamu iya d’orata a hanya mu da kanmu.”

Jinjina kai sarki Wudar yayi yace “Wa ya fad’a maka amana koyawa mutum ita ake? Ai da ita ake haihuwar mutum.”

K’ara sadda kai bafaden yayi a zuciyarshi yace “Amma ni a zaman da na yi da abokina na fahimci addininshi ne ya koya masa zama hakan, ko ba’a haifeka da ita ba indai kana wannan addinin, to ya zama wajibinka ka koyawa kanka ita, rashin samun amana kuma a wajen mutum mai wannan addinin, to tabbas ka tabbata gurb’atacce a cikinsu.”

A zahiri kuma cewa yayi” Hakane ranka shi dad’e, amma girmanka ya isa ya samar da mai amana da rik’on sirri.”

Jinjina kai yayi amma bai xe komai ba, kusan minti biyu a haka kafin yace” Ka je ka zo min da ita nan.”

Da sauri ya mik’e yace” An gama sarki na.”

Fita yayi da sauri dan cika umarninshi, sarki Wudar kuma mik’ewa yayi ya koma d’akinshi dan zaman jiran wacce za’a kawo masa.

A k’alla minti ashirin ya d’auka kafin suka dawo tare da wata budurwa, har k’ofar d’akin ya k’wank’wasa ya basu izinin shiga, shiga sukayi a tare ind ya d’ora ido akan matashiyar, bata da laifi kam kyakyawa yar duma duma, jikinta ma babu alamar k’azanta ko datti, saidai alamu sun nuna a tsorace take, dan gaba d’ay cikin d’ar d’ar take ta k’ame ta k’i sakin jikinta.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button