Hausa Novels

Lu’u Lu’u 31

Numfashin da Ayam ke saukewa ne yasa ta satar kallonta, ai kam idonta a rufe alamar bacci, da alama kuma ta fara jin dad’inshi saboda yanda ta turo baki hannunta akan cikin Juman, murmusawa tayi ta d’an muskuta kwanciyarta sannan ta gyara hannunta ta fara shafa gashin Ayam d’in.

Irin dad’in da take ji marar misaltuwa na ratsata sanadiyar kasancewa tare da ‘yarta, hakan yasa murmushi ke shinfid’e akan fuskarta idonta a lumshe tana d’an rera wak’a a can k’asan zuciyarta ta farin ciki da godiya ga Allah, sannu sannu ita ma har baccin ya d’auketa mai dad’in gaske data jima ba tayi irinsa ba.

Yanda ya ji shiru daga d’akin yasa shi shigowa cikin sand’a, ganin dukansu bacci suke yasa ya ci gaba da takawa saida ya zagaya inda Ayam ke kwance, a hankali savoda baya so su farka ya sunkuya tare da d’an d’ora hannayenshi a kan gadon ya tokaresu, matsawa ya dinga yi saida ya kai kanshi kusa da na ta, cike da shauk’i da so da k’auna ya d’ora labb’anshi ya sumbaci kanta, a hankali ya d’ora hannunshi akan gashinta ya shafa wasu k’walla na cika masa ido.

Motsawar da Ayam ta d’an yi ce tasa ya zabura ya mik’e tsaye ya rarraba ido cikin rashin gaskiya, kamar zata bud’a ido sai kuma ta sake yin ram da cikin Juman ta ci gaba da shek’a baccinta.

A hankali ya zagaya ta b’angaren Juman yasa hannu ya daddab’ata, a tarz suka bud’a ido suka kalleshi kafin su raba jikinsu dana juna, cikin had’e fuska sarki Musail yace “Ke me kike a nan? Ba ga d’akinki can ba?”

Turo baki tayi gaba tace “Pahh, nan nake so na kwana, kai ma ka zo ka kwanta a nan.”

Murmusawa yayi yace “Zafeera, ki je d’akinki ki kwanta kinji, na zo ganin mahaifiyarki ne tunda na ga ita bata san ta je inda nake ba.”

Cikin magagin baccin daya kasa sakinta ta kalli Juman sannan ta rarrafa ta sauka daga kan gadon, ganin kamar tana had’a hanya yasa shi saurin kama hannunta ya rumgumota a jikinshi, saitin kunnenta ya rad’a mata” Ki tabbatar baki je d’akinki ba a daren nan.”

D’aga kanta tayi t kalleshi da mamaki da kuma fad’aw tunani, amma kafin ta ankara ta turata k’ofar d’akin ya rufe ya barta tsaye da zulumi.

Ganin gidan shiru ga fitilu duk an kashe yasa ta saurin d’aga k’afa ta nemi haurawa sama, dakatawa tayi sai kawai ta bi ta wata kusurwar duk da bata san ina zata kai ta ba, cikin tsoro tsoro take tafiya tana sand’a, duk k’ofar data wuce saita kalla da mamakin yawan d’akunan dake cikin gidan, jin ana bud’e wata k’ofar daga bayanta da makulli yasa ta saurin ruguwa cikin sand’a, d’akin dake k’arshen kusurwar kawai ta bud’a ta kuma yi sa’a a bud’e yake, dan tsoronta bata san wa ye zai fito ba, kuma sak’on nan da kuma abinda mahaifinta ya fad’a mata ya tsorata ta sosai, ga ka duhun cikin gidan wanda sai d’an siririn hasken jar fitila kawai.

Tana shiga d’akin ta mayar da k’ofar da sauri ta rufe tare da juyawa ta dafe k’irji dan ta sauke numfarfashi, sai dai bala’in data gani ne ya yi barazanar tafiya da numfashinta, kakkafewa idonta sukayi inda ta ja numfashi amma bata samu damar saukeshi ba, ga hannunta akan k’irji ta tsaya k’am kamar gawa.

Fitowarshi kenan daga wanka ya gama goge jikinshi, wandonshi ya d’auka 3 quater zai saka, hakan yasa shi zame towel d’in dake d’aure a k’ugunshi, amma da ya ji an shigo d’akin kamar ba lafiya ba sai ya dakata ya juya da k’arfi rai b’ace da tunanin wane marar tunanin ne, ganinta yasa komai na shi ya tsaya ya rasa abun yi, musamman daya fahimci kamar ta fita hayyacinta sakamakon mugun ganin da ta yi. 馃槍

A saib’ance ya sunkuya ya d’auki towel d’in ya d’aura yana jan tsaki da fad’in “Ko ma menene ke kika ja.”

Wani tsakin ya kuma saki tunawa haka ma waccen ranar ta bankad’o mata kai d’aki, saidai anyi sa’a ranar yana cikin ban d’aki ne.

Sake juyawa yayi ya kalleta ya ga tana nan yanda take, girgiza kai yayi ya fara takawa zuwa gareta, yana tsayawa gabanta ya k’yasta mata hannu yace “Ya dai? Kin ga wani abu ne?”

K’arfin halin irin na ta yasa ta d’aga baki za tayi magana, sai ta ji babu abinda zai iya fitowa sai kurmanci, hakan yasa ta daddagewa ta d’aga bakinta ta kwamtsa k’ara, da wani irin sauri ya sa hannu ya rufe mata baki tare da jawota jikinshi ya had’e gam, tana jin haka sai kuma numfashinta ya b’ace b’at ta sume a jikinta, hakan yasa jikinta ya saki kamar wata matatta.

 

_Domin samun *lu’u lu’u* da kuma *Badak’ala*, ki biya naira d’ari biyu kacal ko kuma 400f cfa, dan samun na ki tuntub’i wannan lambar 94-98-56-52._

 

*Alhamdulillah*

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button