Hausa Novels

Lu’u Lu’u 34

Da k’yar ya k’arasa bakin gadon ya zauna, sai gashi madadin raka’a biyu daya saba yi kafin kwanciya bai tsaya yin ta ba, bai kuma d’auki na’urarsa ya fara binciken wasu abubuwa ba, sai kawai ya dinga tunani da k’walwarshi dan sai ya ji na’urar ma bai yarda da ita ba.

*Washe gari* da k’yar ta tashi tayi sallah, a haka ma dan Juman ta bata magani tasha na rage rad’ad’i da zazzab’i, tana idar da sallah ta koma ta kwanta ta ja lallausan bargo ta rufe, da kallo Juman ta bita sannan ta girgiza kai, duba agogon d’akin tayi sannan ta mik’e daga kan sallayar, wayar fax d’in dake d’akin gefen gado ta d’auka, a nutse ta shiga jera lambar wayar likitarta sannan ta aika mata kira, saida wayar tayi k’ara kamar zata tsinke sannan ta ji an d’aga, cikin girmamawa da mutumtawa suka gaisa da juna kafin ta fad’a mata tana buk’atar ganinta gida, a ladabce ta amsa mata da “Shikenan ranki shi dad’e, in sha Allah zan shigo nan da wasu mintuna.”

Jinjina kai tayi ita ma tace “Nagode, sai kin zo.”

Aje k’aramar carbin hannunta tayi mai duwatsun irge talatin da uku sannan ta cire hijabinta mai riga ta nufi ban d’aki, wanka tayi kafin ta fito ta shirya a sauk’akakk’en shiri ba kwalliya a fuska, tana kammalawa ta fita a d’akin tare da sakawa k’ofar makulli dan sam bata yarda da gidan nan ba, cire makullin tayi ta tafi da shi zuwa madafa.

Shigarta yasa duk ma’aikata kama jikinsu suka dinga gaisheta, amsawa tayi a lokaci d’aya kafin ta nufi duk inda tasan zata samu abinda take da buk’ata, wata hadimar ce tace “Ranki shi dad’e me kike da buk’ata? Ki bari sai a had’a miki.”

Girgiza kai tayi tana yatsina fuska tace “A’a ku barshi, yanzu ni bansan da wa zan yarda ba a gidan nan, tunda har a cikin nan za’a kai min abinda aka saka guba, wato na ci da ni da ‘yata ba?”

Sake girgiza kai tayi ta shiga d’aukar k’wan da take son soyawa, duk jinin jikinsu suka sha suka ci gaba da aikinsu, mai dafa abincin mai martaba na kari daban, masu shara da goge madafar daban, masu dafa abincin bak’i ma daban.

*Bacci* ya fara d’aukarta daga ta cikin ban d’aki wani da bak’ak’en kaya da rufaffiyar fuska ya hauro ta siririyar tagar dake ciki, a daidai bahon wankan ya saukar da k’afafunshi dan kar ya fad’a ciki gaba d’aya, saida ya tabbatar ya tsaya da kyau sannan ya tsallaka bahon ya sauko, a hankali ya bud’e k’ofar ya shigo d’akin, ganin Ayam dunk’ule tana bacci ya lallab’a saida ya je daf da ita, hannunshi mai d’auke da safa bak’a da wani k’aramin abu kamar reza mai kaifin gaske ya ciro, sake matsawa yayi kusa da ita sosai ya d’ora a gefen wuyanta da niyyar ya mata mummunan yankan rago.

Saidai k’ofar da aka tab’a kamar za’a shigo ne yasa ya yanki wuyanta ba daidai ba, ganin jini ya b’allo daga wuyanta ita kuma ta farka a razane tana dafe wuya tare da furta “Auch!”

Da gudu ya juya zuwa ban d’akin inda Ayam ta zuro k’fafu da niyyar sauka ta bishi, sai kuma ta ji rad’ad’in wuyanta na k’aruwa, hannu ta kai ta murza wurin lemar da ta ji yasa ta dubi hannun na ta, zaro ido tayi ganin jini ne ya wanke hannunta, da sauri ta mik’e tana sake rik’e wurin gam ta tunkari k’ofar da kai tsaye ta ji ana bubbugawa.

Murd’a k’ofar ita ma tayi amma sai ta ji a rufe, jijjiga k’ofar ta dinga yi da hannu d’aya inda d’ayan ke kan wuyanta sai neman shure shure take, a gigice sarki Musail dake bakin k’ofar yace “Wai Juman ba zaki bud’e k’ofar ba ne?”

Daga bayanshi Juman dake tahowa d’auke da farantin abincinta ta furta “Gani nan mana sarki na.”

Ta k’arashe a aladabce saboda gilmawar hadimai ta ko ina da kuma masu kula da gidan, juyawa yayi da sauri ya kalleta da mamaki, saida ta zo daf da shi cikin rad’a yace “Ina Zafeera?”

Wani wawan kallo ta masa sanda take k’ok’arin zura makullin ta hudar k’ofar tace “Tana ciki.”

Cikin rad’a ya sake cewa “Me yasa kika barta ita kad’ai?”

K’ofar data bud’e ta kuma murd’a lokaci d’aya yasa ta zuro kai tana fad’in “Saboda ba jaririyar da zan goya ba ce a baya n…”

Turus ta ja ta tsaya sanda idonta suka gane mata Ayam durk’ushe cikin jini sai kawai ta saki farantin ta druk’ushe tana kiran “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un! Ayam me ya same ki?”

Da k’arfi ya shigo shi ma ganin wannan yasa ya sunkuya yana fad’in “Zafeera? Zafeera? Lafi…”

Sai kawai ya k’arasa kusan gadon ya fara waige waige, k’ofar ban d’akin dake bud’e ya shige yana ganin taga a bud’e ya juyo da sauri, cikin hargagi ya kalli Juman da daidai shigowar likitarta yace “Ku bata kulawar da ta dace, karki kuskura ki k’ara yin nesa da ita.”

Ficewa yayi daga d’akin ba tare daya kula da komai ba, likitar na duba yankan wuyan Ayam d’in ta kalli Juman hankali tashe tace “Sarauniyata, ya kamata mu kaita asibiti, tana zubar da jini dayawa da buk’atar a ma ta d’inki.”

Mik’ewa Juman tayi tace “To me mu ke jira? Mu tafi mana.”

Kamata sukayi suka fita da ita, cikin kid’ima Juman ta kalli wani bafade tace “Ka kira mana dreba ya kai mu asibitin cikin gida.”

Da sauri bafaden yayi abinda ta umarceshi, kafin su fita k’ofar falon har drzba ya paka mota, shiga sukayi inda ya kewaye shukokin nan sannan ya zagaya ta bayan gidan tafiya ce mai d’an tsayi idan a k’afa ne, yana aje su daga cikin asibitin ma kujerar marasa lafiya aka fito da ita aka d’orata suka shige cikin asibitin da tsarin gininta yayi kamar wani k’aramin gida mai kyau.

Suna shiga kai tsaye bloc aka wuce da ita dan kula da lafiyarta.

Tunda ya shiga fadarshi ya ja baki yayi shiru yana jin maganganun fadawan na tashi sama sama, bai ce komai ba sai zuba musu ido, bai kuma nuna yana cikin tashin hankali ba, saidai yana lura da yanayin kowa da kuma son ganin wanda yake zargi d’in ya shigo.

A hargitse ya shigo fadar yana kama babbar rigarshi, da sauri sarki Musail ya gyara zamanshi ya tsura mishi ido, kujerarshi ta kusa da sarki Musail d’in ya ja ya zauna yana kallonshi bayan ya rusuna masa.

A d’an daburce Khatar ya kuma kallonshi sannan ya kalli Dhurani a b’angare d’ayan kusa da sarkin sannan yace “Ranka shi dad’e, yanzu nake samun mummunan labari a cikin gida.”

Rik’e hab’a sarki Musail yayi a dak’ile yace “Wane irin labari kuma waziri?”

A sanyaye yace “Ranka shi dad’e, gimbiya Zafeera ce aka farmaketa a d’akin sarauniya, yanzu haka sun tafi asibitin cikin gida.”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button