Lu’u Lu’u 34

A kasalance sarki Musail yace “Kenan bata mutu ba yanzu ma? Wai wane irin mutane ake ba wa aikin nan ne?”
Kaf fadar suka dinga kallo kallo sai Dhurani daya kalli sauran fadawan da basa cikin tsarinsu yace “Zaku iya jira a waje, da alama mai martaba na cikin alhini.”
Jiki a sab’ule cike da takaici suka mik’e suka fita, wanda ya rage Khatar ne da shi Dhurani sai kuma Adah, da sauri Khatar ya kalleshi yace “Sarki na, da alama akwai mai ruguza mana tsarinmu, jiya cikin dare mutanenmu sun ziyarci d’akin gimbiya Zafeera, amma basu sameta gaba d’aya, saidai ko ma waye ya kai mata farmakin nan yanzu, bana jin d’aya ne daga cikin mutanenmu, dan har yanzu babu wanda ya tuntub’e ni da maganar.”
Da mamaki Dhurani yace” To wa ye kenan ya yi?”
Girgiza kai Khatar yayi yace” Ban sani ba gaskiya, sai dai nan gaba zamu sani.”
A k’ufule sarki Musail ya kalleshi yana ji ya shak’i wuyanshi sannan bakinshi ya furta” Kai Khatar ‘yar ta wa kake so ka kashe? Yata ta ciki na? Shin me ta tsare maka a rayuwa?”
Amma sai ya dake yace” To wane irin hwanb’asawa kake game da lamarin? Ba dan ka ce na bar maka a hannunka ba, da yanzu na shak’e wuyanta.”
Da sauri Khatar yace” A’ a yallab’ai, ai shi yasa na ce zan yi komai, kar ka d’auki matakin nan da hannunka, ina k’ok’ari a kai.”
Cikin d’aga murya yace” Wane k’ok’ari ka ke?”
Cikin ladabi yace” Yallab’ai ai jiya mun yi k’ok’arin ciyar da su guba a abinci, amma sai wani abu ya faru suka tsallake wannan tarkon…”
D’aga masa hannu yayi tarz da duk’ar da kanshi k’asa, k’afarshi dake sanye cikin takalmi masu kyau da k’yalli ya dinga buga k’afar d’aya bayan d’aya, wani huci ya fara jerawa yana saukewa, jikinshi rawa ya fara d’auka tsabar takaici da k’uluwa, d’aga kanshi yayi da sauri ya mik’e tsaye da wani irin sauri ya kama hanya ya fita tsabar haushi har k’afafunshi na hard’ewa.
Da kallo suka bishi har da Adah ma daya bi bayanshi da sauri yana hararen Khatar, kallon junansu sukayi Khatar yace “Me ya faru kuma?”
Girgiza kai Dhurani yayi yace “Ba na ce ba, ban dai fahimci komai ba, duba da ko halin da aka fad’a masa ‘yarsa na ciki bai damu ba.”
Cikin rad’a Khatar yace “Ko dai bai ji dad’i ba ne da na fad’a masa.”
Harara Dhurani ya wurgawa k’ofar kafin ya kalli Khatar yace “Rabu da shi.”
*Sarki Musail* na fita daga nan cikin sauri ya shiga takawa zuwa asibitin, da girmamawa Adah yace “Ranka shi dad’e, ka bari a d’auko mota.”
A hassale yace “Ni rago ne ? Na ce ba zan iya tafiya can d’in ba?”
Wucewa yayi kamar zai tashi sama Adah na bin shi, daf da k’ofar shiga Umad ya zagayo ta bayan asibitin shi maa kid’ime suka kacame, turus sukayi suna kallon juna sai kuma suka fara k’ok’arin shigewa.
Karo sukayi da juna hakan uasa Umad dakatawa Musail ya wuce sannan ya shige shi ma da gudu, inda suka ga Juman tsaye suka tsaya a tare suka had’a baki wajen fad’in “Ya jikin ta?”
“Ya jikin ta?” Kallon juna sukayi sai kuma suka kalli Juman da ta ja majina tace “Ban sani ba ni ma, tana ciki har yanzu basu fito ba.”
Lumshe ido yayi ya jingina a bango ya rumgume hannayenshi, k’ok’arin dakatar da zuciyarshi kawai yake akan abinda take raya masa, sam baya so ya fara d’aukan mataki sai ya ji halin da take ciki, indai har aka fito masa da gawarta yanzu, to shakka babu Zafreen ma za ta bi yar uwarta ba da jimawa ba, dan a dalilinta zai bayyana waye shi a duniya.
Tsantsar tashin hankalin shi ne rasa dalilin da yasa za ta yi haka, saboda sarauta ne? Ko kuma dai son zuciyarta? Ko kuma wani ya sakata? Girgiza kai ya fara yi a hankali idonshi a rufe yana jinjina lamarin.
Takon takalmin da suka ji a bayansu an shigo ne yasa su juyawa shi ma a nutse ya bud’e ido, zuba mata su yayi tun daga k’asan takalminta masu tsinin gaske bak’ak’e, zuwa dogon wandon jikinta daya kamata bak’i, sai rigar mai siraren hannaye ita m bak’a da gashinta data d’aure, dan kyau kam akwai shi, saidai kyan d’an maciji ne.
Sarki Musail ma kallonta yake da mamakin abinda ya kawota, idan har ta san me ya faru shi ne zata shigo haka? Ba wani alamar abun ya dameta a matsayin Zafeera na yar uwarta, girgiza kai shi ma ya d’auke kanshi daga kallonta, tana zuwa ta ja birki ta tsaya ta kalli Juman a shek’e tace “Mah, ta mutu ne?”
Wannan tambayar da tayi ita tasa kowa dake wurin kallonta, gyara tsayuwarsa yayi ya dafe k’ugu d’aya irin zai kirta rashin mutumcin nan yana kallon k’wayar idonta yace “…
*Alhamdulillah*
The post Lu’u Lu’u 34 first appeared on 2gNovels.com.ng.
[ad_2]