Lu’u Lu’u 35
Gyara tsayuwa yayi da kyau cikin isa da fitar da kowane harafi yace” Kin d’auka sanarwar da aka dinga yi daga gwamnati saboda mahimmancinta a gare su ne ? Ko kad’an, ni ne na yi haka dan na jawota gare ni, daga yanzu kuma ni ne zan dinga kareta har sanda numfashi zai bar gangar jikina.”
Juyawa yayi zai zauna kan kujerar dake gefen gadon na zaman mutum uku, rik’e hannunshi tayi tace” Kamar ya zaka kareta da kan ka? Ba kai kake son kasheta ba?”
Tsaki yayi ya bige hannunta tare da zaunawa kan kujerar yana sake kallon fuskar Ayam, komawa tayi ta zauna ita ma tana kallonshi sai tunanin abinda ya fad’a take yi, sai dai sam zuciyarta ta kasa yarda da abinda ya fad’a, dan ita a ganinta abubuwan da ke faruwa har yanzu bai d’auki mataki d’aya ba a kai.
*Giobarh*
Abun al’ajabi ne tashin sarauniya Kossam da k’afafunta a safiyar yau, abun kamar al’amara, ba taimakon kowa ba kuma sanin kowa haka aka wa yi gari aka ganta da k’afafunta kamar yanda take a da shekaru da suka wuce, kowa kallonta yake kamar ya ga sabuwar hallita har sanda sarki Wudar ya zo inda ta ke da mamakin da ya fi na kowa.
Ido cikin ido suke kallon juna amma mamaki ya hanashi magana, d’an murmusawa tayi a ladabce tace “Mamaki ko? Ba abun mamaki ba ne.”
D’an jujjuyawa ta fara kamar tana neman wani kafin ta kalleshi tace “Ina yarinyar nan?”
K’asan k’afafunta ya kalla ya dai tabbatar ita ce sannan ya kalli fuskarta, da mamaki yace “Wai…ya haka? Kossam, ya haka ta faru?”
Murmushi tayi mai tsadar gaske tace “Wannan yarinyar ce, a duk inda take yanzun na tabbatar suna tare da Umad, na ga hakan a mafarki na kuma na gasgata.”
A kid’ime ya zaro ido yace “Me? Umad? Da Zafeera?”
Da mamaki da kuma fara’a ta kalli fuskarshi tace “Zafeera? Ita ce dama? Sunanta kenan?”
Hankali a tashe yace “E, amma me ya had’ata da Umad kuma?”
Girgiza kai tayi tace “Ban sani ba, amma dai akwai wani abu dake faruwa a tsakaninsu.”
Da k’arfi cikin rud’u yace “Baki sani ba?”
Cike da izgili ta d’aga kafad’a alamar e ta juya zata fita tace “E, ban sani ba, amma yanzu zan sani tunda na samu lafiya.”
Fita tayi daga falon ta tunkari b’angaren Joyran, a hankalce take tafiyar tana kallon k’afafunta da mamakin yanda farat d’aya ta tashi yau, haka kawai a mafarkinta ta ga wannan yarinyar da kuma Umad, hak’ik’a tun ranar da yarinyar ta hana kowa shiga wurinta sai amintattunta, tun ranar Joyran bata sake shiga d’akinta ba, abincin da take bata da abinda take shafa mata a jiki duk ta daina, tun daga ranar ta fara jin canji a jikinta, daren jiya kuma bakinta ne ta ji yana tirsasata tayi magana, haka kawai ta fara d’aga harshenta da a baya kamar shi ne aka danne aka hana mata magana da shi, amma sai ta ji ya saki har ta fara furta sunan d’anta Urab da kuma Umad.
Tsakiyar dare tana bacci sanda mafarkin nan ya zo mata tana ganin hoton fuskar yarinyar da kuma d’anta a gefenta, yanayinta ya nuna kamar shagwab’a take dan tayi takwaf takwaf da fuska ne, amma bata tantance ba kawai ta ji ta zumduma ihu da ya sa ta tashi daga baccinta a firgice, mantawa tayi da larurarta kawai ta mik’e tsaye tana zazzare ido, saida ta hangi kanta a madubi ne sannan ta kula ita ce fa a tsaye, tsaye kan k’afafunta yau? Sai kawai ta shiga takawa tana godiya ga abun bautarsu tana mai son sake ganin yarinyar nan da har yanzu bata san ko da harafin farko na sunanta ba.
Joyran na tsaye tana ta kai da kawo da wayarta a hannu tana fad’awa k’awarta cewa “Ki taimaka min k’awata ki je ki samu mutumin nan ya min wani sabon aikin, nan da India ai ba wata tafiya ba ce, kuma zan d’auki nauyin komai na tafiyar ta ki, kin ga na rantse miki ina cikin tashin hankali.”
Jim tayi alamar gana sauraren abinda ake fad’a daga can, da sauri ta d’auka da fad’in” Ba zaki gane ba k’awata, komai fa nema yake ya lalace a nan, kinga dai kwana uku kenan ban ba ta abinci ba bare na saka maganin, gaba d’aya yarinyar nan ta lalata komai, yanzu haka Wudar d’in ya juya min baya, jiya ya shigo yana son na bashi had’in kai, na d’auka zai sake dawowa saboda ba zai iua hak’ura da ni ba, amma kuma har yanzu bai waiwaye ni ba, gashi Khatar ma da ya ce zai turo min kud’i har yanzu shi ma bai turo ba.”
Marairaicewa tayi tace” K’awata, idan har lamarin nan ya lalace na rantse miki barin garin nan zan yi, tattarawa zan yi na koma can gurin Khatar, dan cikinsa ne a jikina.”
Daga bayanta ta ji an ce” Ki bar nan ki je ina ‘yar uwa?”
Da k’arfi ta juyo tana zazzago idonta dan tabbas tasan murya da jimawa, ganin Kossam tsaye gabanta ta k’are mata kallo tas, sai kawai ta saki wayar ta fad’i k’asa da k’arfin tsiya tace” Kossam? Ke ce a kan k’afarki? Ta ya ya? Bayan bokan nan ya fad’a mana haka zai faru ne kawai idan sauyi ya zo.”
Saida taa gama fad’a sai kuma ta fahimci me ta aikata, wata dariya Kossam ta dinga shek’awa kafin ta girgiza kai tace” Haka ya fad’a? Da alama kun jima baku had’u ba ko? Tunda bai fad’a miki sauyin ya zo ba.”
Rarraba ido ta fara yi tare da k’ak’aro murmushi tace “Amm..yaya…ba fa abinda…nake nufi ba kenan, kawai dai…”
Shiru tayi ba tace komai ba, da fara’a a fuskar Kossam tace “Na fahimta, yanzu dai barin garin nan ba shi ne mafita ba, ki zauna tare da ni, zan ji dad’i sosai.”
Juyawa tayi zata fita sai kuma ta tsaya ta kalleta, a dak’ile tace “Cikin jikinki, me yasa kika so d’orawa mijina da farko? Amma yanzu kuma daga bakinki na ji asalin na wa ye.”
Girgiza kai tayi cike da takaici tace “Ban tab’a tsammanin haka daga gareki ba, Joyran kin ci amanata kuma kin zalince ni, amma…”
Jinjina kai tayi ta cije leb’e tare da juyawa ta fice a falon, tana ganin fitarta ta d’ora hannu a kai ta durk’ushe ta fashe da kuka tana fad’in “Na shiga uku ni Joyran, me na aikata haka? Ya zan yi yanzu?”
Kamar an tsikareta sai kuma ta zabura ta mik’e tana rarumar wayarta a k’asa ta shige d’akin baccinta dan had’a kayanta, dan ba zata k’ara awa d’aya gidan nan ba sai ta barshi, matsala d’aya shi ne isashen kud’i da bata da a hannu, amma duk da haka zata harhad’a kan kud’ad’enta da kuma siyar da kadarorinta in ya so ta kama gabanta.
*Egypt*
A falon na alfarma mai d’auke da mafiya dattijai suka gama tattaunawa, sun jima suna hirar data shafi ci gaban talakawa akan tallafin da masarautar zata bayar na ilimin yara k’anana.
Bayan sun kammala duk da ya gaji sosai yana kuma buk’atar hutu, amma haka ya sa aka shigo masa da Bukhatir, zaune yayi d’aya daga kujerun wanda suka tashi a ladabce, cikin girmamawa yace “Ranka shi dad’e ka ce ka na son gani na, ina fata dai lafiya?”