Hausa Novels

Lu’u Lu’u 37

_Bismillahir rahamanir rahim_

*37*

 

A hassale yace “Zan iya mana, zan iya, zan iya.”

Da gudu ya juya ya nufi hanyar d’akin na ta, Haman kuma k’arasawa yayi kusa da hadiman nan da suka lab’e bayan kujeru.

Daga waje kuma har yanzu sara da suka ake da harbi tsakanin dakarun sarki Musail da maharan nan, inda cikin k’warewa duk su ka yi nasarar kashe maharan sannan rabin su suka tunkari b’angaren sarki Musail, wasun su kuma suka shigo falon dan ba wa sarki da iyalinshi kariya.

Kasancewar Adah wanda ya san sarki Musail farin sani ne, sai ga shi cikin tawagar wad’anda suka shiga falon da kiyyar kare iyalinshi, yanda Haman ya saitasu da bakin bindiga yasa Adah saurin d’aga hannayenshi yace “Kar ka yi harbi, mu ne.”

D’auke bindigar yayi sannan ya matso kusa da su yana fad’in “Wannan harin fa? Daga ina haka?”

Da sauri Adah yace “Ba wannan lokacin, dole mu gaggauta ba wa iyalin mai martaba kariya kafin su cimma su.”

Sama ya tunkara zai hau tare da mabiyanshi sai Haman yace “Ina ga suna d’akin gimbiya Zafeera.”

Juyowa Adah yayi ya kalleshi sai kuma ya kalli wani yace “Ku biyu ku je d’akin gimbiya Zafreen, ku tabbatar babu abinda ya sameta, akwa mab’oya ta sirri a d’akin, ku yi k’ok’arin dubata a ko ina.”

Da gudu gudu suka nufi inda ya fad’a musu suna kuma rik’e makamansu a hannu, shi kuma tare da wasu suka nufi d’akin Ayam d’in dan ba ta kariya.

*Umad* na isa k’ofar d’akin ya tsaya tare da duba bindigarshi dan ganin alburushi na wa ya rage masa, k’waya biyu ne dan haka ya mayar ya sake d’anata, lumshe ido yayi yana jin yanda rad’ad’in nan ke ratsashi, bud’e ido yayi tare da jan dogon numfashi sannan ya sauke, a hankali cikin sand’a ya sake kawowa daf da k’ofar, d’an lek’awa yayi dan ganin k’ofar d’akin a bud’e take, saidai babu abinda ya gani, k’arar fad’uwar abu da ya ji tare da k’arar Ayam yasa yayi kukan kura tare da mantawa da komai ya danna kanshi cikin d’akin yana mai saita daidai kan mutum da bindigar.

Cak ya tsaya saboda ganin wata rufaffiyar fuskar da aka nad’e da rawani, wannan mutumin da ya shigo d’akin na jikin shi ga dukkan alama kuma ya kashe shi ta hanyar murd’e masa wuya.

Sakin mutumin yayi hakan yasa shi fad’uwa k’asa ba rai bare ya motsa, fad’uwar da ya yi tasa Ayam ta saki kwalbar turaren data d’auka dan kare kansu daga sharrin mutumin nan, amma kafin ta kai ga haka kawai ta ga wannan mutumin da fararen kaya ya fito daga wata k’ofar ta cikin d’akin da bata san da ita ba kawai ya damk’i mutumin nan, wanda da ita ce a k’alla zasu d’auki awa d’aya suna gabza fad’a, ita bata yarda ya kayar da ita ba, shi ma kuma bai fad’i ba saboda girmanshi.

Da sauri Umad ya tunkari inda take tsaye ya d’an shiga k’are mata kallo sannan ya kalleta yace “Ba abinda ya same ki?”

Girgiza kai tayi alamar e, sannan ta kalli Juman dake kusa da gado tana kallon mutumin dake gabanta, kallo ne take masa zuciyarta na bugawa sosai, jinin jikinta kanshi tsitsinkewa yake, kallon sani take masa ba kuma sanin shanun talla ba, farin sani mai sunan farin sani dake nuna kasan ciki da waje na mutumin, yanda take sororo a tsaye ta kasa gusawa har saida Ayam ta dafata cike da kulawa tace “Mah! Kina lafiya?”

Kallon Ayam tayi kamar wacce ta farfad’o daga doguwar suma, sai kawai ta girgiza mata kai alamar ba komai.

A hanzarce mutumin ya taka zai bar d’akin da sauri Umad ya rik’o hannunshi, hakan yasa mutumin juyowa ya kalli hannun Umad dake rik’e da na shi hannun, a hankali ya d’aga jajayen idonshi manya ya kalleshi, murya a dak’ile Umad yace “Wa ye kai?”

Maida kallonshi yayi ga k’ofa ba tare d ya ce komai ba, shiru yayi bai amsa ba haka kuma ba alamar zai amsa d’in, saidai da alama yana jiran ya sake masa hannu ne.

Sannu sannu Ayam ta fara takowa kusansu saida ta zagaya inda fuskar mutumin ke kallon k’ofa, d’aga kanta tayi kad’an dan ya d’an fita tsayi, ido cikin ido suka dinga kallon juna wanda su kad’ai ne suka fito daga fuskarshi.

Irin yanda ta tsareshi da idon nan sai ya samu gabanshi da fad’uwa, kwarjini da tasirin baiwar dake cikin idonta, sun dame na shi sun shanye duk da kuwa shi ya *haifeta*.

Waro idonta ta yi a sanyaye sosai cikin murya kamar ta rad’a tace ” *Pah*, Abba na, kai ne?”

Sai kuma ta k’ank’ance idonta ta ziraro da hawaye tace “Na sani dama, na sani babu ta yanda za ayi a ce mahaifina ne ke son kashe ni, Pah, yau gashi ka nunawa duniya kai masoyina ne, ka nunawa kowa da ke da tarihina zaka iya fansar rayuwata da na ka ran…”

Fad’awa tayi kirjinshi tana sake fashewa da kuka, da sauri Juman ta d’ago k’afarta ta nufosu, tana zuwa gabanshi ta tsaya ta sa hannu ta jaye rufin fuskar nan yayi k’asan hab’arshi, da sauri ta rufe bakinta da tafin hannu tsabar mamaki ta zaro ido, kyarma jikinta ya d’auka tana ci gaba da kallon fuskar Musail dake kallonta shi ma idonshi taf da hawaye yana shafa bayan Ayam dake rusa kuka.

Da k’yar bakinta ya iua fuska “Kai ne? Mu…s…”

Sai kuma ta d’ora hannunta a kan ta tare da ture d’an kwalin kan na ta, hakan ya bayyanar da dogon gashinta bak’i k’irin ya sauka a gadon bayanta, ganin yanda jikinta ke rawa kamar ba zata iya tsayaw da kanta ba sai kawai ya jawota ita ma ta fad’o k’irjinshi ya rik’eta tsam tsam.

Umad kallonsu yake bakinshi d’auke da manyan tambayoyi, saidai ba damar furta ko kalma d’aya a yanzun.

Kamar wanda aka tsikara Ayam ta d’ago ta kalli fuskar sarki Musail tace “Pah, yar uwata? Ta na ina?”

Da sauri shi ma ya dawo hankalinshi ya d’aga Juman daga jikinshi, da azamaya tunkari k’ofa zai fita sai kuma su Adah da tawagarsa suka shigo, duk tsayawa sukayi suna kallonsu, da ido Adah ya musu alama tuni suka zagayesu, cikin dakakkiyar murya Adah yace “Ranka shi dad’e babu abinda ya sameku?”

Girgiza kai sarki Musail yayi yace “Lafiya lau muke a nan, ina Zafreen?”

Adah ne yace “Na tura dakaru d’akinta, za su kula da ita.”

Jiniyar motar kwana kwana da ta asibiti da suka ji ne yasa sarki Musail nufa hanyar fita, tareshi Adah yayi yace “A’a sarki na, har yanzu bamu tabbatar da tsabtace gidan nan daga mahara ba, ka jira anan tukuna.”

Wani jan kallo ya masa yace “Ba ka da hankali, ka san me ye nauyin al’umma kuwa?”

Da sauri ya fice a d’akin yana fad’in “Ka zauna nan ka kula min da iyalina.”

Fita yayi hakan yasa Umad da wasu daga cikin dakarun suka bi bayanshi, Adah kuma nuna wa su Ayam gado yayi yace “Ku zauna.”

Hannun Juman ta kama da kufin su zauna kamar yanda ya ce, amma sai Juman ta fizge da sauri ta fita a d’akin, da gudu gudu Ayam ta bi ta bayanta haka shi ma Adah ya bisu da sauri tare da dakaru ukun da suka rage tare da shi.

Yanda suka samu mutanen dake falon ne yasa suka dakata a nan, lokacin da jami’an kwana kwanan suke shiga da gudu da kayan aikinsu na kashe wuta, lokacin dogaran nan suka fito daga d’akin Zafreen suka tsaya gaban sarki Musail suka ce “Yallab’ai gimbiya Zafreen bata d’akinta.”

Cikin tashin hankali Musail yace “Kamar ya? Ta na ina?”

Girgiza kai d’aya a ciki yayi yace “Ba mu sani ba yallab’ai.”

A tsawace sosai yace “Maza ku nemo min ‘yata, ku nemota duk inda take.”

Da sauri aka sake bazuwa dan neman Zafreen, inda masu aikin kwana kwana da ke ta aikin kashe wutar nan, motocin asibiti ma da suka zo suna ta shiga da gadon majinyata dan duba ko akwai wanda ya jikkata.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button