Hausa Novels

Lu’u Lu’u 37

Kan kujera Ayam ta zaunar da Juman da ta ga kamar akwai abinda ke damunta saboda yanda take kallon Musail da shi bai ma kula ba, ita ma zaunen tayi ta buga tagumi tana kallon shige da ficen jama’a.

Haka suka karad’e gidan wajen neman Zafreen amma babu ita babu dalilinta, da suka sake fad’a masa haka kamar zai yi hauka ya ciro wayarsa zai kira lambarta, cak Umad ya rik’e hannunshi, suna had’a ido ya girgiza masa kai a tausashe yace “Tana nan zuwa, za ta zo, yanzun nan.”

Da mamaki a fuskar Musail yace “Kamar ya? Ya aka yi ka sani? Ta na ina?”

Wani d’an murmushi yayi ya d’auke kan shi yace “Idan ta zo zaka ji.”

Jim yayi yana kallon sai kuma ya d’auke kai shi ma ya kalli Adah yace “Adah, duk inda Dhurani ya ke ka kawo min shi gabana yanzu yanzun nan.”

Da sauri Adah ya amsa da “Angama ranka shi dad’e.”

Duka dakarun suka bi bayanshi hakan yasa falon ya rage daga Musail sai Juman da Ayal sai kuma Umad, amma klwa ya fita wanda yasan ya ji ciwo yana gaban motar asibiti, wasu da aka harba kuma wanda harbin bai zo da ajali ba tuni an d’aukesu zuwa asibiti dan ceton gaggawa.

Cikin nutsuwa Umad ya shiga takawa zuwa d’akin baccinshi dan ya samu damar yin sallah subah da lokacinta ya yi, kamar jiran tafiyarshi suke Musail ma ya fita a falon ya nufi b’angaren shi.

Ganin su kawai suka rage Ayam ta kalli Juman ta dafata tace “Mah, me yake damunki ne?”

Kallon Ayam tayi ta k’ura mata ido, ta jima tana tunani tana kallon fuskarta sai kuma ta sauke ajiyar zuciya mai k’arfi, girgiza kai tayi tace “Ba komai.”

Jinjina kai Ayam tayi tace “Kin tabbata?”

Sake jinjina mata kai tayi alamar e, ita ma jinjina kai tayi tace “Mu je muyi sallah, na ga hasken alfijir ya keto.”

Jinjina kai Juman tayi kawai ta mik’e, tsoro da fargaban ko har yanzu wani abun zai iya faruwa ya sa Juman ta ce su d’aura alwala a ban d’akin dake falon kusa da gurin cin abinci, a nan sukayi alwalar suka fito, Ayam da kanta ta shiga d’akin Juman ta d’auko musu duk abun buk’ata wajen sallah.

Suna kabbara sallarsu motocin jami’an tsaro suka danno cikin gidan su ma, abun ka ga abinda ya shafi mulki da kud’i, sai gidan ya k’ara hautsinewa da hayaniya, inda yan kwana kwanan sukayi nasarar kashe gobarar ba tare da ta yi k’amarin da ta bar madafar ba, saidai d’akunan dake kusa da ita sun fara d’aukar bak’in hayak’i wasu kuma silling d’insu har ya fara kamawa da wutar, cikin sa’a dai babu wanda ya ji rauni daga wutar sai jakadiyar sarki da aka d’auka ranga ranga sakamakon hayak’in daya daketa saboda asim dake gareta.

Suna daf d gama sallar Musail ya shigo tare da sipetan (Inspector) jami’in tsaron da ke son yi ma kowa tambayoyi yanda hakan ta faru, inda sauran jami’an ke ta duba gawawwakin mutane suna d’aukarsu hoto da binciken k’wak’waf.

*Umad* ma na idar da sallah wayarshi k’arama ya rik’e ga hannu yana kallo, tunane tunane kala daban daban ne suka ziyartarshi a lokacin, yana so ya kira wayar tangarahon dake falo da kowane d’aki dan yayi magana da Mah d’inshi, jiya ta kasheshi da al’ajabi kafin bacci ya d’auke shi, sanda aka kirashi ya ga sarki Wudar ne, amma yana d’agawa ya ji muryar da tun yana shekara shida rabonshi da ita, saida ya jiri ya jefashi kan gado ya fita a hayyacinshi, sai ga shi yana zubar da hawaye abinda ya jima bai yi ba, ita kuma shi kuka aka rasa mai rarrashin wani.

Da k’yar Kossam ta rarrashe shi sannan ta tambaye shi inda yake, k’in fad’a mata yayi da fari sai dai kawai ya tabbatar mata yana lafiya, saida ta yi ikrarin zata nemeshi sannan ta je inda ya ke kad’ai ya fad’a mata yana Khazira, abinda ta fad’a masa a lokacin ta kuma kashe waya shi ne yasa shi shiga wani yanayi na daban, sai ya rasame zai yi a lokacin, gashi daya maida kira sai aka k’i d’agawa har ta tsinke.

Yana so ya ji da gaske mahaifiyarshi zata iya aikata abinda ta fad’a cewa ” *To ni ma zan zo Khazira gobe da safe, za mu had’u da kai sannan mu je masarautar Musail, zan nema ma ka auren ‘yarsa Zafeera yarinyar da ta kula da ni, kuma a dalilinta na samu sauk’i yau, na gani a mafarki na Umad, aurenka da ita alkairi ne.*”

Abinda ta fad’a kenan ta kashe wayar, ganin tunanin ba zai gyarashi sai ya kai hannunshi zai aika kiran, jin jiniyar motocin jami’an tsaro da ya yi yasa ya mik’e daga kan sallayar ya soka wayar aljihun wandonshi ya fita a d’akin da sauri.

Yana k’arasowa falon daidai da zuwan Haman, haka ma sarki Musail ya zauna kan kujera haka ma sipetan yan sandan, su Ayam ma suna sallame sallarsu suka gyara zama, kan kujera Juman ta zauna amma Ayam sai ta gyara zama a k’asa.

Jami’in ne ya kallesu a harshen slovaque yace “Ina tayaku jimami sarauniyata.”

D’an lumshe ido tayi ta gyad’a kai alamar ta amsa, d’orawa yayi da fad’a musu sunanshi da kuma aikinshi sannan ya ci gaba da fad’in “Me zaku iya cewa game da wannan abun da ya faru?”

A tare kuma a sanyaye suka girgiza kai alamar ba komai, gyara zamanshi yayi dan su fahimce shi da kyau yace “Am sarauniyata, ina nufin…”

D’aga masa hannu Musail yayi fuskarsa a had’e yace “Jami’i, ka dakatar da tambayoyinka har sanda mai laifin ya k’araso, su basu san komai ba game da abinda ya faru.”

A ladabce jami’in ya kalleshi yace “Ranka shi dad’e, muna so mu tattara bayanan da zamu samu wata makama ne, bincike muke so mu yi game da al’amarin nan, duba da cikin maharan duka dakarun masarauta sun kashesu, guda biyu ne muka samu a raye kuma mugun rauni ne a jikinsu, wanda kafin mu iya ji daga bakinsu zai d’aukemu kwana uku.”

Shirun da Musail yayi ya tabbatarwa jami’in ya yarje masa kenan ya ci gaba, sake gyara zamanshi yayi cikin kujerar ya juya ya kalli wata jami’a dake sanye da kayan aikinta hannunta rik’e da alk’alami da takarda yace” Ki d’auki duka bayanansu.”

Jinjina kai tayi tare da kafa alk’alaminta akan takardar tana kallon Juman da Ayam, a tsanake ya fara tambayarsu inda kowace tambaya da wacce ke amsa mi shi ita.

Umad na ganin haka ya nufi d’akin Zafreen, yana tura k’ofar ya shiga babu kowa a d’akin sai hasken fitila, d’akin shiru kuma a gyara tsaf babu wani abu da ya same shi, da hanzari ya nufi wajen drowerta ya bud’e, bincikawa ya fara yi yana d’add’aga kayan yana dubawa ko zai samu wata makamar.

A k’ank’anin lokaci ya hautsina d’akin da bincikenshi, har k’ark’ashin gado saida ya lek’a amma babu abinda ya samu, mik’ewa yayi ya rik’e k’ugu yana kallon d’akin, tsaki yayi zai fita na jin haushin bai samu komai ba, har zai fita sai kawai wani abu ya zo masa a rai, lokacin daya taka kujerar dake gaban madubi ya lek’a sama, daya sauko ya manta ya rik’e drower sosai ta yanda indai aje ne take to tabbas za ta motsa, amma sai ya tuna batayi motsi ba alamar a kafe take.

Da sauri ya dawo tare da dubawa, sai kuma hasashenshi ya bashi daidai, komawa yayo b’angaren shi na hagu ya tura kwabar zuwa dama, jin bata motsa ba yasa ya koma b’angaren dama ya tura zuwa hagu, sai gashi kamar k’ofa mai taya drower ta motsa k’ofa kuma ta bayyana.

Murd’a k’ofar yayi ya shiga d’akin mai duhu, wayarshi ya ciro ya kunna fitila da taimakonta ya kunne hasken wurin, hanya ce doguwa da zata kai ka har zuwa fita a bayan garin, wanda kowane d’aki na sarki da iyalansa akwai hakan.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button