Hausa Novels

Lu’u Lu’u 38

*38*

 

Gyara zama Umad yayi yana kallon Musail a shek’e cikin isa da k’asaita yace “Ina nufin mahaifiyarta, yallab’ai duk abinda ya faru jiya zuwa yau, yarinyar nan ce Zafreen, kuma ta yi hakane da taimakon wasu da suke da burin ganin bayanka, daga ciki akwai Bukhatir, wannan malamin da kuma tsohuwar hadimarka *Nanna*.”

Juman dake tsaye kallonshi tayi da mamaki amma kuma ta kasa cewa komai, cikin jin haushi Zafreen ta matso kusan Umad ta nuna shi da yatsa tace” Dama kai ne ka shiga d’akina ka min bincike? Akan wane dalili? Baka da wannan damar malam.”

Galala ya kalleta tare da d’ora k’afa d’aya kan d’aya yace” Ba yau na ke bincike a kan ki Zafreen, tunda na fara aiki na ke bincike akan duk wani dake zagaye da Ayam, sannan na kan dasa ayar tambaya akan duk wani dake da kusanci da ita, na nesa ko na kusa, musamman ma ke da kika sake tabbatar min da zargina ta hanyar shiga makarantar da ta ke.”

Kamar wacce kanta zai yi bindiga Juman ta dafe kai ta kalli Musail tace” Ban fahimci komai ba, Zafreen dama ba ‘yata ba ce?”

Wuru wuru ya fara yi da ido yana sinne kai k’asa, a gadarance Umad ya kalleta yace” Sarauniya dan Allah zauna, ni zan fad’a miki komai, dan na gaji da wannan nuk’u nuk’un.”

Da sauri ta zauna tana zuba masa ido dan abinda take son ji kenan, gyara zamanshi yayi a mutumce ba tare daya kalleta ba yace” Sarauniya, duk abinda zan fad’a miki abinda na ji ne daga bakin wacce abun ya faru da ita, ma’ana tsohuwar hadimarku Nanna Kapoor, ta fad’a min awa d’aya da rabi ne bayan kin haihu ita ma ta fara nak’uda, allurar da aka miki ta bacci ta sa baki samu damar ganin abinda kika haifa ba wanda bai zo a raye ba, a wannan tsakanin ita kuma ta haife abinda ke cikinta wanda sarki Musail shi ne musababbin shi, k’arfin mulkinshi ya nuna mata tare da mata alk’awarin kud’ad’e masu yawa idan har ta ba shi yarinyar da ta haifa, amma sai tayi taurin kai saboda soyayyar d’a da uwa, to fa hakan ne yasa aka koreta a wulak’ance sannan ya raba da yarinyar wacce aka baki a matsayin yar da kika haifa.”

Kallon fuskarta yayi cike da ladabi yace” Amma magana ta gaskiya ke namiji ma kika haifa ba mace ba.”

Yanda ta saki baki ta saki ido tana kallonshi, hawaye kawai ke malala a idonta, juyawa tayi ta kalli Musail tace” Da gaske ne abinda ya fad’a?”

Lak’was jikinsa yayi tare da komawa ya zauna kan kujera kanshi k’asa yace” Hakane, gaskiya ne abinda ya fad’a.”

Fashewa tayi da kuka tace” To amma me yasa? Me yasa ka rabata da ‘yar da ta sha wahala ta haifa? Ka san rad’ad’in da uwa take ji idan ta rasa abinda ta

haifa?”

A sanyaye Umad ya kalleta yace” Saboda soyayyarki ne sarauniya, a duk mutanen da na zanta da su abu d’aya suke fad’a min, sarki yana son sarauniyarsa fiye da komai.”

Cikin k’unar zuci da tsana Zafreen ta fara kuka tana kallon Musail tace” Kai mugu ne azzalumi, ka rabani da mahaifiyata saboda farin cikin matarka, kun banzatar da ni kun wulak’antani saboda son zuciyarku, ba zan tab’a yafe muku ba.”

K’ank’ance ido Musail yayi yana kallonta yace” Kenan saboda haka kike son kasheni?”

A harzuk’e kamar zata kai masa duka tace” Ba ma kai kad’ai ba, har da su duka iyalinka, dukanku na so kashewa, kuma sai hakan ya tabbata.”

A hassale Musail ma ya mik’e tsaye yace” Saboda me za ki had’a da su, ni ne na miki laifi, me yasa su zasu fuskanci hukuncin?”

Cikin fitar hayyaci tace” Saboda dalilinsu ka wulak’anta mahaifiyata, a da ina ganin kulawarka, amma daga ranar da aka haifi wannan…”

Ta fad’a tana nuna Ayam sannan ta d’ora da” Sai ka canza min, na d’auka kana son samunta ne dan ka cutar da ita, shiyasa har na yi yunk’urin taimaka maka, amma kwanaki kad’an da suka wuce na fahimci ba gaskiya ba ne, hasalima na gano kai ne ka ke bata kariya da kulawa.”

Kallon tuhuma da neman k’arin bayani ya mata, hakan yasa ta yin murmushin yak’e tace” E, na gano komai ai, ka tuna *Ahmad*?”

Rarraba ido yayi yana kallon k’asa, wata dariyar ta kuma yi tana fad’in” E mana, Ahmad ba, wanda yake isar da sak’onka a wajen su Habbee, na ganshi kuma ya fad’a min komai dake faruwa.”

Dafe k’irji Juman tayi ta mik’e tsaye tace” Me kike fad’a haka Zafreen? Me ya sako su Habbee a cikin wannan maganar?”

Wani kallo ta mata tace” Saboda ba ke kad’ai su ke wa aiki ba, har da shi ma Musail d’in.”

Da sauri Juman ta kalleshi tace” Da gaske hakane?”

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace” Hakane Juman, lokacin da aka nemi Zafeera aka rasa hankali ya tashi matuk’a, dan yanda na shirya bata kariya ban shirya da b’atanta ba, sai nayi tunanin masu nemanta ne suka sameta, a kwana biyu tak aka nemo min inda su Habbee suke da yarinyata, dan na bata kariyae data dace haka na sa Adah ya kashe abokan tafiyarsa su uku sannan ya dawo min da labarin Ayam tana cikin k’oshin lafiya, daga lokacin na canza musu gari daga k’auye zuwa Larhjadin, wanda mak’iya da dama tunaninsu bai basu wanda suka sace Ayam za ta zauna gari kusa da Khazira ba, da wannan na samu nasarar saka ido a kan duk wani motsin Ayam, sannan na ke sa wa ana k’ara bincika min haka lokaci zuwa lokaci.”

Wasu hawaye Juman ta sako masu zafin gaske tace ” *Abban Ayam* kasan da haka me ya sa baka tab’a fad’a min ba ko sau d’aya? Me ya sa baka fad’a min kai ma so ka ke ka ceci rayuwar ‘yarmu ba?”

Girgiza mata kai yayi yana matso yar k’wallar data taru a kurmin idonshi yace “Ta ya zan fad’a miki a lokacin ki yarda Juman? Ba kya saurarata sannan kin tsaneni, bugu da k’ari kina kallona a matsayin wanda ke son kashe ‘yarmu.”

Numfashi ya sauke a nutse yana kallon k’asa yace “Bayan Dhurani ya sanar da ke fassarar mafarkinki, ni ma ya had’u da ni ya sanar da ni, saidai ya k’ara da fad’in wannan yarinyar da za’a haifa za ta zama tashin hankalina ce, ita ce mafarin rugujewata da kawo k’arshen mulkina, sannan ya fad’a min tabbas ita ce za ta zama silar mutuwa sannan ta kawo k’arshen mulkin zalincina, na ji ba dad’i sosai a lokacin sannan na shiga firgici na abubuwan daya fad’a min, sannu sannu na fara shiga damuwa na abinda ya fad’a min, haka na fara rasa nutsuwata saboda tunanin mutuwata, wata rana da yamma sai kawai na je fadar abun bauta Ghira dan na samu mafita a wajen Dhurani, a wannan lokacin ne na san komai na kuma fahimci komai, na samu malami Dhurani da waziri Khatar da biyu daga cikin fadawa na suna tattaunawa a kai na, kasancewata sarki ya sa masu gadin k’ofar kai tsaye suka bud’e min, shiyasa ba su tunanin wani zai iya shigo musu ba tare da izininsu ba, abinda na ji ya gigita ni, na shiga tsananin firgicin da ya fi wanda na zo da shi.”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button