Lu’u Lu’u 38

Numfasawa yayi sosai sannan ya d’ago ya kalli Juman dake ta shashek’ar kuka Ayam na durkushe gabanta tana rarrashi yace” A nan na ji duk shirin da suke na ganin bayana ne, suna shirin kashe ni dan su maye kujerar mulki na, sannan su d’auki fansa akan laifin da ni ban san ya faru ba sai a tarihi, amma sai gashi da taimakonsu suna tunzurani ina aikata abinda al’ummata zasu k’i ni su kuma kirani da azzalumin sarki, juyawa na yi a wannan lokacin na koma saboda kaina daya fara sarawa, saboda abinda na ji malam Dhurani ya fad’a, cewa ya fad’a min k’arya akan yar cikina da za’a haifa, tabbas baiwarta gaskiya ce, saidai batu na zata kasheni ta ruguza mulkina k’arya ne, shirinshi ne kawai saboda yana so na kasheta da hannu na dan kar ta kawo masa targand’a a cikin lamuransu, na jima da jimamin wannan lamarin a rayuwata, daga baya kuma bayan tattaunawa da zuciyata da kuma shawarar da amintacce na wato Adah ya bani, sai muka fara buga wasar daidai da na su, inda a zahiri na ke nuna musu na tsani Zafeera kuma kasheta shine burin rayuwata, amma a bad’ini ina kulawa da matata da kuma abinda yake cikinta, wanda wasu lokuta da gangan na ke fad’in magana marar dad’i duk dan tunanin abinda zai je ya dawo.”
Sosai Juman ke kuka haka ma Ayam data girgiza kanta tana hawaye tace” Ban tab’a yarda ba har zuciyata cewa wai mahaifina zai kashe ni, duk da ban san shi ba kuma ban tab’a ganinshi ba, amma dai na ji a zuciyata ban gamsu ba, ashe duk makirci ne, kuma aka yi sa’a ya mamaye duniya har kowa ya yarda da hakan.”
Yanda jikin Dhurani ke rawa ne yasa shi yin zaune k’asa d’abas kamar an hankad’ashi, zufa yake sosai yana ta zazzare ido, cikin magiya da rawar murya yace” Ran…ranka shi…dad’e, ka min…rai, na tuna.”
Girgiza kai Musail yayi yace” Ba na kiraka nan dan na yafe maka ba ne, dole ka fuskanci mutuwa Dhurani, zunubinka babba ne.”
Kallon Zafreen yayi yace” Abinda ya faru tsakani na da Nanna ba abu bane da kowa ya sani, ta ya kika san labarin mahaifiyarki?”
Kafin ta yi magana Umad dake k’are mata kallo a lalace yace” Dhurani ne, gashi nan gabanka, shi ne ya busawa labarin rai, saboda yayi anfani da ita ta yanda zata zama barazana a gareka, kuma yayi nasarar samun haka tunda har yanzu burinta bai wuce ta kasheku ba sannan ta maye abinda take ganin na ta ne.”
A hankali Musail ya kuma kallon Dhurani yana jinjina kai, murmushin yak’e yayi yace” Kun k’irk’iri labari, sannan kun aiwatar da wasan, ku kuka samar wa da kowane jarumi rawar da zai taka, sannan a bayan fage ku kuke taka taku rawar.”
Cikin takaici da hargagi Juman ta nunashi da yatsa tace” Amma Dhurani Allah ya isa tsakani na da kai, ba zan tab’a yafe maka ba bak’in munafiki, dama abinda ka shirya mana kenan? Ka tunzura mijina da labarinka na k’arya hakan yasa na dinga jin haushinsa ina wasan b’uya tsakani na da shi.”
Jan majina tayi ta kalli Musail tace” Indai har abubuwan da suka faru sa saninka, kenan ka san da zuwana a lokacin da kuke tattaunawa kan yanda zaku kashe Zafeera bayan na haifeta?”
A hankali ya gyad’a mata kai alamar e tare da fad’in” Ina sane na tura jakadiya ta turo min ke, saida na tabbatar na ji takon tafiyarku sannan na fara magana tsakanina da Dhurani, na kusan kinji saboda yanda kika canza min daga lokacin, saidai ban san me kike shiryawa ba har sai ranar da na ji daga su Habbee cewa ke kika saka su.”
A hankali Umad ya kalli Musail d’in yace” Shiyasa ka san komai kenan? Hatta da aurena da… Ayam?”
K’uri kowa ya masa da ido yana kallo kamar wanda ya fad’i wani mugun abu ban da Musail kawai, shi ma Umad bai yarda ya kalli kowa ba sai dakewa da yayi ya buga fuska, a sauk’ak’e Musail ya jinjina masa kai alamar e, sannan ya gyara zamansa ya kalli Adah, nuna masa Dhurani yayi yace “Ka kai min shi kurkukun Sabah.”
Da sauri Dhurani ya mik’e yana fad’in “Ba zai yiwu na Musail, akan me zaka k’ask’anta ni haka? Ka sani wasa kake da wuta kuma zata k’ona ka.”
A hassale ya kalleshi yace “Na yarda Dhurani, amma dole ka fuskanci k’ask’anci a rayuwarka kafin ka mutu.”
Cikin fitar hayyaci ya fara fizge fizge saboda rik’eshi da Adah yayi yana fad’in “Musail sai na kasheka, sai na kasheka zan ji sauk’i a cikin zuciyata, kamar yanda babanka ya kashe min kakana, dole kai ma ka mutu mutuwar wulak’anci.”
Da kallo suka bishi har Adah da wasu dogaran suka d’auki suka fice da shi, da mamaki Ayam ta kalli Musail tace” Pah, me yake magana a kai ne wai? Wacz d’aukar fansa?”
A tsaanake ya kalleta yace” Mahaifina ya kashe kakansa lokacin da kakanshi Allah ya masa baiwa kwatankwacin ta ki wacce ake alfahari da hakan, saidai kakan na shi yayi anfani da haka ta hanya marar kyau, a wasu k’auyukan talakawa na fama da matsalar ruwa, mahaifina ya rok’i alfarmarsa ya bayar da wani filinsa da bincike ya tabbatar za’a samu ruwan da gaba d’aya gari zai sha ya wadatu, amma ya k’i a lokacin, saida mahaifina ya siyi filin da manyan kud’ad’en da suka wuce k’a’ida, sun yi hakan a sirrance kamar yanda mahaifina ya buk’ata, sannan ya aje takardun filin na k’warai a hannunshi bayan sun saka hannu, hakan yasa har yanzu mutane ke ganin kamar kakan Dhurani shi ne ya zamar musu silar samuwan wannan ruwan, inda suka girmamashi suka d’aukakashi ya zama waliyinsu, hakan da ya faru shi ne mafarin matsalar da ta sa mahaifina ya kashe shi, saboda mahaifina yana da adalci ba kamar ni ba da zalinci ya fi yawa a mulkina.”
Numfasawa yayi sannan ya cigaba da fad’in” Lokacin da mutane suke girmama suke zuwa da matsalarsu dan ya magance musu, lokacin ne k’anwar mahaifina ita ma ta je dan ya mata addu’a a gaban bak’in gunkin da suke bautawa dan ta samu miji tayi aure, saboda tun bayan mutuwar mijinta tana zaune gida babu aure, saidai madadin ya mata addu’a sai ya mata fyad’e, sannan ya tsorata da fad’in idan ta fad’a abun bauta zai la’anceta ba kuma zata ga biyan buk’ata ba, k’anwar mahaifina ba lusarar mace ba ce, dan haka ta tureshi daga jikinta sannan ta tabbatar masa zata fad’a dan mahaifina ya k’watar mata ‘yancinta, jin haka sai ya tsorata ya kamata ya kuma shak’e wuyanta, bai saketa ba saida ya ga ta daina shurawa kad’ai alamar ranta ya bar gangar jikinta, da taimakon yaronsa na hannun damansa suka binneta a gonar wani manomi, saidai da ubangiji ya tashi kawo k’arshenshi, a sauk’ak’e aka tono gawarta saboda mammalakin gonar da ya ga abinda bai tab’a gani ba kuma ba shi yayi ba, bayan an tonone aka ga gawarta wacce lokacin hankalin masarauta ya tashi ana ta nemanta, wannan dalilin ne ya hassala mahaifina ya sa jami’ai a cikin lamarin, to fa shine da aka gano gaskiyar maganar ta hanyar amintaccen yaronsa kawai mahaifina ya cire masa kai ba tare daya jira hukuma ta d’auki matakin daya dace a kan shi ba.”