Hausa Novels

Lu’u Lu’u 39

Hararanta Juman tayi tace “Kin manta kin bani labarin Umad ya kaiki wajensu? To ta ya ba zasu sani ba.”

Turo baki tayi ta d’ora kanta a kafad’ar sarki Abdallah, a tausashe ya saki murmushi cikin kamala ya fara magana a nutse “Na samu labarin abinda ke faruwa ne a tv a labarai safiya, ai abinda ya faru ya fi k’arfin yan jaridu da gwamnati suyi shiru, maganar aurenki kuma ai tun ranar da ku ka je ya fad’a mana.”

Jinjina kai duk sukayi sai Ayam data turo baki ta sake langab’ewa jikin sarki tace” Grand Pah, ni dai ku fad’a masa ban yarda ba, kawai ya auri yar uwata Zafreen, dan ita ce take son shi ba ni ba.”

Yar dariya sarki yayi tare da maida hankalinshi kan Juman dake fad’in” Baki isa ba yarinya, tunda mahaifinki ma ya amince to an wuce wajen.”

Yanda Bukhatir ke ta rarraba ido yana kallonsu ne yasa sarki Abdallah fad’in” Yawwa Bukhatir, ka san dalilin da ya sa tafiyar nan na ce sai da kai?”

A ladabce ya kalleshi cike da son b’oye damuwarsa yace” A’a ranka shi dad’e.”

A nutse yace” Na kiraka ne saboda ina so ka ganewa idonka, sannan ka rarrashi zuciyarka tayi hak’uri da abinda take so, sannan ka tuna da mahallicinka wanda shi ya k’addara faruwar hakan.”

D’agowa yayi ya kalleshi da kyau yana son k’arin bayani, a hankali sarki Abdallah ya jinjina masa kai alamar e sannan yace” Na san komai Bukhatir, na san dayawa daga abinda ka ke b’oyewa, tsananin son Ayam da ka ke da burin ganin ka mallaketa, idan da Allah ya rubuta matarka ce tabbas da mun yi farin ciki da haka, saidai Allah bai rubuta za ta zama ta ka ba, ka yi hak’uri da hakan ka d’aukeshi a matsayin k’addararka.”

Nunfasawa yayi sannan yace” Sai kuma soyayyar da ka ke wa kujerata, Bukhatir kai ne magajin wannan kujerar tun fil’azal, duba da ban da magaji ko magajiya, ina so in shaida maka daga yanzu da nake maganar nan na bar maka sarautar k’asar Egypt, ka zama sarki daga yau nad’aka kawai ya rage, saidai kafin hakan ta kasance sai ka min wani alk’awari guda d’aya a gaban duka mutanen dake wajen nan.”

Sadda kai Bukhatir yayi yana jin gaba d’aya tunaninsa ya tsaya cak, ya rasa da wanne zai ji, shin zai yi bak’in ciki da rashin Ayam ne? Ko kuma murnar samun wannan kujera da duk abinda yake dan ita yake yi? Duba da dama yana son samun Ayam dan ya yi alfahari da shi ya samu zab’abb’iyar, sannan ya buga k’irji a gaban sarki Musail yayin da zai nunashi da yatsa yace ya auri ‘yarsa da yake burin kashewa, sannan ya bata matakkan tsaro su zuba ido har su ga lokacin da’ yar zata kassara uban.

Mamakin kalaman sarki Abdallah yasa Juman kallonshi da mamaki tace “Pah, wai dama Bukhatir Ayam yake so?”

D’an murmushi kawai yayi bai ce komai ba, maida hankalinshi yayi ga Bukhatir yace “Ba ka ce komai ba Bukhatir?”

Sake d’aga kanshi yayi a sanyaye yace “Nagode ranka shi dad’e, wannan karamci a gareni, Allah dad’a girma da lafiya.”

A hankali Umad ya kalli sarki Abdallah yace “Ranka shi dad’e, kafin ya d’auki wannan alk’awarin zan so sanin wani abu daga gareshi.”

Lumshe masa ido yayi dake nuna ba damuwa, kallon ju’a sukayi wanda hakan yasa Bukhatir had’e fuska yana jin tsanar Umad d’in har k’asan zuciyarshi, Umad kam ko a jikinshi duk da mugun kallon da yake masa, cike da dagiya da rashin tsoro yace” Bayan duk abubuwan da ka yi zamu iya cewa an yafe maka, amma laifin da yanzun kuka aikata babba ne, wanda yayi sanadiyar jikkatar wasu mutanen, tambayar a nan ita ce, shin ka yi hakane dan ka taimaki Zafreen ta cimma burinta? Ko kuma dai yarjejeniya ce a tsakaninku ta kowa zai cika burinsa dalilin hakan?”

Kallon Umad duka mutanen wurin sukeyi sai Bukhatir dake neman rikicewa a zaunen nan da yake, wuk’il wuk’il yake da ido yana son satar kallon mutanen wurin amma ya kasa, cike da borin kunya yace” Me kake fad’a ne haka? Ban san akan me kake magana ba.”

Wani murmushin rainin hankali Umad yayi ya d’auke kansa bai ce uffan ba, sarki Musail ne ya kalleshi yace” Umad, me kake son fad’a ne?”

Kallon Musail d’in yayi yace” Yallab’ai, kwana biyun da mukayi a nan na saka ido akan Zafreen sosai, hakan yasa na gano wata alak’a data k’ullu tsakaninsu su biyun nan, farmakin da aka kai wa Ayam a d’akinta wanda aka yanketa ma Zafreen ce ta yi, sannan harin da aka kawo yau ma, Dhurani da Zafreen da kuma shi Bukhatir ne suka d’auki nauyin maharan.”

Babu wanda bai kalli Bukhatir da mamaki da kuma jijjiga ba, inda mahaifiyarshi ta rabka salati tana fashewa da kuka, dafe k’irjinta tayi tana fad’in” Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un! Bukhatir wace riba za ka ci a cikin aikata hakan?”

Wuru wuru ya fara da ido yace” Nifa ban san akan me yake magana ba, ta ya ma zan iya aikata dan Allah?”

Shiru falon ya d’auka sai kallonshi kawai suke, a saib’ance Umad ya kalli Haman dake gefenshi, kallon da ya masa yasa gaba d’aya Haman ya ji fitsari na neman kubto masa ya zubo, hakan yasa ya bi Umad da kallo irin na ka taimake ni, idan ka san wani abu kar kayi magana a nan ka jira mu bar nan sannan.

A hankali Umad ya girgiza kan shi sannan ya kalli Zeyfi ita ma a daidai lokacin shi take kallo saboda yanda ta kula yana kallon Haman, suna had’a ido tayi k’asa da na ta tana jujjuya jakarta dake gabanta, sai kuma ya juya ya kalli Haman yace “Da ka fad’a ita d’in yayarka ce ai, ba wani abu ba ne dan kana son taimakon ‘yar uwar ka, ni kaina duk abinda na ke saboda d’an uwa na nake yi.”

Kallonsu aka fara yi suma har Bukhatir da ya kalli Umad yace “Waye d’an uwan na ta?”

Banza Umad ya masa dan shi ma haushinsa yake ji saboda soyayyar da yake ma Ayam, maida kallonshi yayi ga Zeyfi yace “Ke me ye had’inki da wannan?”

Cikin turo baki gaba tana sissine kai tace “D’an uwa na ne.”

Da sauri ya kalli Haman sannan ya kalli mahaifiyarshi yace “Mah, dama tana da d’an uwa da ban sani ba?”

Tab’e baki mahaifiyarshi tayi tace “Ban sani ba nima sai yanzu, ai ba ni na had’a aurenka da ita ba, mahifinka ne kuma baya raye.”

Da mamaki yace “Amma ai Pah ya fad’a min kafin ya rasu cewa na rik’eta amana ni kad’aita gareta tunda iyayenta suka rasu.”

A sanyaye Zeyfi tace “Ya fad’a maka hakane saboda haka d’in ne, Haman tun yana yaro ya bar gida saboda basa shiri da mahaifinmu, kullum cikin fad’a suke akan sab’anin ra’ayi, dan haka wata rana ya ce zai bar gida su manta da shi, cikin hushi mahaifinmu ya ce ya fi ruwa gudu, sannan shi ma ya sa a ranshi kamar bai tab’a haihuwar d’a namiji ba, wannan dalilin yasa nake ni kad’aita, saidai ni ban yada zumuncin dake tsakani na da d’an uwana ba, muna had’uwa a kai a kai sannan muna waya ma, saidai mahaifinmu ne sam ya k’i hak’ura, amma mahaifiyarmu ma sukan gaisa da shi ta waya, har ta rasu tana binsa da addu’ar alkairi, sab’anin mahaifinmu da ya rasu yana hushi da shi.”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button