Lu’u Lu’u 40

*40*
Umad a fita daga nan d’akinshi ya nufa, iya abinda zai buk’ata kawai ya d’auka na daga kud’i da passeport d’inshi da kuma babbar wayarsa, fitowa yayi ya sa dreban gidan ya kai shi filin jirgi, yana shiga ciki dan samun izinin tafiya sai ga Joyran na jan k’aramar jakarta da sauri, da mamaki ya kuma dubawa da kyau dan ya tabbatar ita ce ya gani? Ko kula dai tsabar son had’uwa da ita yanzun ne yasa yake ma wasu matan kallonta?
Har ta d’an gitta ta gabanshi ta wuce sai k’amshin turarenta mai k’arfin gaske ya shaida masa tabbas ita ce dai wacce zaka tafi yanzu dominta, to amma me ya kawota nan? Kafin ya samu amsar ya taho sukwane yace “Aunty.”
Bata juyo ba saboda tunanin wa zai kirata da haka a nan d’in, saida ya matsa daf da ita yace “Aunty Joy.”
Da sauri ta juyo saboda d’aukar muryarshi da kuma tabbatarwa da ita dai a ke, suna had’a ido duk da hular dake kanta (hana sallah) da bak’in gilashi k’ato data saka saida ta ji gabanta ya fad’i har ta furta a k’asan mak’oshi “Umad kuma?”
Bai yi mamakin ganinta a wannan lokacin ba, saidai mamakin da ya ke shi ne hala bata san gogan na ta ya bar duniya ba?
Da mamaki da kuma rawar murya tace “Amm..Umad, me…kuma ka ke y…a nan? Ina nufin me ya kawo ka nan?”
Murmushi ya sakar mata tare da sunkuyawa yace “Ina kwana auntyna.”
Wani murmushi ta saki wanda kai tsaye daga zuciyarta ya fito sakamakon ganin ya gaisheta kamar yanda yake yi a da, kafin zuwa shed’aniyar nan ta lalata mata komai, damtsenshi ta dafa tace “Lafiya lau Umad, baka amsa min tambayata.”
Kallon k’wayar idonta yayi sannan yace “Aunty mun zo shak’atawa ne tare da abokaina, yanzu ma wani malaminmu ne ya zai zo saboda zamuyi yawan bud’a ido da shi, shiyasa na zo nan.”
Dariya tayi tace “Masha Allah, Umad kai dai baka son zama wuri d’aya.”
Wani malalacin murmushi ya mata bai ce komai na, rik’o jakarta yayi yana kallon fuskarta yace “Aunty ke fa? Me ya kawoki Khazira?”
Cikin kame kame tace “Uhmm..ka gane, ni ma dai na zo had’uwa da wata k’awata ne da mukayi karatu tare, tayi aure kuma ban samu na zo ba saboda hidimar kula da aunty (Kossam), shine yanzu na zo na mata murna.”
Jinjina kai yayi yace “Yayi kyau hakan, amma kafin nan aunty mu je na kaiki masaukinmu, dan kinga bai kamata ki d’ora mata nauyi ba ko?”
Da sauri tace “A’a a’a Umad, ai mun yi da ita zan sauka a gidanta, ka ga ba zata ji dad’i ba, kuma m ai zata turo drebanta ne ya d’aukeni.”
Cewa yayi “Duk da haka aunty na, mu je mu jira dreban, idan ya zo sai ya saukemu a masaukin.”
Yanda yayi gaba da jakarta yasa bata da wani zab’i sai bin bayanshi, gasu tsaye mutane na ta barin wajen amma su suna nan, tana son sanin ta yanda zata ribace shi ya bar wajen sannan ta shige taxi, amma ya gagara hakan, hatta ruwa da ta ce ya kawo mata da jakar ta ta ya tafi ya siyo ya dawo, k’arshe dai kallonta yayi yace “Aunty na, anya kuwa dreban nan zai zo?”
Dariyar yak’e tayi tace “To gashi dai shiru, amma zai zo, zai zo na sani.”
Girgiza kai yayi tare da tare taxi yace “Ba zai zo aunty, idan har tana ganinki da daraja ba zata yarda ta kasa turo mai d’aukarki kafin saukar jirginki ba, ni kuma ba zan tafi na bar nan ba na bar ki a tsaye.”
Tura jakarta yayi a boot ya bud’e mata gidan baya yace “Shiga aunty.”
Kamar zata fashe da kuka ta kalleshi amma haka ta shiga a dole saboda tana jin nauyin yi masa gardama, shiga tayi ta zauna ya rufe sannan ya shiga mazaunin gaba dreban taxi ya ja su zuwa titin da Umad d’in ya fad’a.
Da k’aramar wayarshi yake ta latse latse har suka yi nisa, Joy kam daga baya kamar zata fashe saboda takaici, k’eyarshi kawai take zabgawa harara kamar ta kashe shi, ga haushin da uwarshi ta k’unsa mata yau d’in, kawai ta sa hadimai na ta mata wani shirye shirye, data tambayeta ko lafiya ta ce zatayi tafiya ne, data tambaya zuwa ina sai cewa tayi “Bai dameki ba.”
Haka shi ma Wudar shirin ya gama tsaf ya ce ai tare zasu tafi, duk da ya yi tambayar har ya gaji cewa ta fad’a masa ina za ta je, sai kawai ta ce wajen d’anta Umad, yin me? Yana ina? Duk ta k’i amsa mi shi, hakan yasa yanzu dai kafin ta baro gidan ta baro hadimai na ta loda kayayyaki a moto wanda duk mai hankali ya gani zaka san neman aure ne za’a je yi, sai dai na wa? Kuma a ina? Bata sani ba, cikin wannan hada hadar ta kutso kai ta badd’a kama ta fita abinta.
Akan babban titin dake bayan filin jirgi motoci na police guda biyu suka tari gabansu, dole ta sa dreban tsayawa da tunanin laifin me ya yi kuma? Wace dokar ya taka ne haka mai girma a cikin tuk’i? Jami’ai hud’u ne suka fito daga motocin, sai jami’a mace d’aya data fito, cike da izza Umad ya fita ya bjd’e murfin da Joy ke zaune tana kallon me ke faruwa, amma sam hankalinta bai tashi na saboda bata ga abinda tayi ba.
Suna k’arasowa dukansu suka sara masa da girmamawa, da mamaki Joy ta kalli jami’an sannan ta kalli Umad da tunanin wa ye shi kuma a gwamnatance, hannunta Umad ya kamo sanda jami’ar ta k’araso ya karb’i ankwan hannunta, ba zato ba tammani ya mata awarwaro da ankwar nan a hannayenta, mamaki ne ya hanata katab’us sai kallonshi tana fad’in “Kai Umad, lafiya? Me na yi kuma? Me ye haka wai? Ka manta ko ni wacece?”
K’ala bai ce mata ba sai jan hannayenta da yayi saida ya sadata da motocin jami’ai ya dannata baya ta zauna sannan ya mayar ya rufe, gilashi ya ciro bak’i daga aljihunshi ya manna a idonshi, juyawa yayi zai shiga mazaunin mai zaman banza ya ji tana jijjiga tana fad’in “Kaiiiii! Umad, ka kunce min abar nan, me na maka ne wai?”
Shiga motar yayi ya ja wata raga dake tsakanin kujerar baya da kujerun gaba saboda baya da buk’atar hayaniyarta, saidai yana jin yanda take ta bubbuga motar tana hargagi, bai kulata ba saidai yana kallon wani jami’i da ya d’auko jakar Joy d’in a bayan taxin nan sannan ya biya mai taxin suka taho, tayar da motocin suka yi har da jiniya irin ta yan sanda sannan suka nufi babbar headquarter jami’an bincike na k’asa.
D’akin bincike suka ajiye ta, kalle kalle ta shiga yi tana ta jujjuyawa, d’akin studio ce ta musamman, dan iya maganarka kawai zaka ji sai wanda ke kusanka, amma ko iska bata shigowa daga waje bare ta fita, lullub’e yake da bak’in yadi mai kaurin gaske, sai wata faffad’ar taga wacce ita daga ciki kanta take gani ma’ana madubi, saidai daga waje jami’ai ne na musamman da na’urori a gabansu, inda daga nan suke iya sauraren duk abinda ke faruwa ko zai faru a ciki.
Kujera biyu ce wacce take zaune a kai sai wacce ke fuskantarta, inda k’akk’arfan teburin dakz gabanta aka d’aure hannayenta da ankwa mai d’an tsayi wacce ta fi wacce aka saka mata da farko.
Cikin hargagi ta fizgi hannayenta tana kwaroroton fad’in “Wai babu kowa a nan ne? Me na yi ne? Akan wane dalili zaku kawo ni nan ku a je? Ina buk’atar ku kira min lauyana.”
Shirun da yayi yawa babu mai kulata ne yasa ta sake fizgar hannayenta har saida kujerar da take zaune ta motsa tare da fad’in “Banzaye kawai, sai kun yi nadamar ajiye ni a nan da ku ka y….”
Cak maganarta ta tsaya saboda k’ofar da aka bud’e aka shigo, Umad ne fuska kici kicin saidai akan bak’ak’en kayanshi ya d’ora wata bak’ar jacket mai d’an ratsin fari sai daga baya an rubuta Police da manyan harufa.