Lu’u Lu’u 40

A gadarance ya k’arasa ya ja kujerar sannan ya ciro k’aramar bindiga daga k’ugunshi ya ajiye, zaune yayi ya rumgume hannaye ya jingina a kujera yana zuba mata idonshi da ba wani girma ne da su ba sai tarin kwarjini kamar na damisa, murya a dak’ile kamar saukan aradu yace “Magana ce za mu yi ba wasa ba, kuma duk abinda zai fito daga bakinki ya zama gaskiya, idan ba haka ba zan manta da wacece ke a gare ni na d’auki tsatsauran mataki a kan ki.”
D’ora hannayenshi yayi a kan teburin ya d’ag girarshi ta hagu sama yace “Kin fahimta?”
A hassale tace “Kai wane irin d’a ne? Ni fa k’anwar mahaifiyarka ce, Umad me na yi da za ka kawo ni nan?”
Had’e yawu yayi tare da sake tsura mata ido yace “Khatar ya fad’a mana kina da alak’a da harin da aka kai masarautar Egypt shekarun da suka wuce, me zaki ce a kai?”
Zazzaro ido tayi na mamakin ya kuma wannan maganar ta fito? Khatar? Ya aka yi Umad kuma ya san shi? Duburburcewa tayi ta kalleshi tace “Ka ga Umad ba zan yi magana ba, ina son ganin lauya na sannan.”
Wani jan kallo ya mata da yasa ta sadda kanta k’asa cikin dakakkiyar murya yace “Tunda kika ga na zo da ke nan kai tsaye, kuma na d’auko miki gundarin zancen a take, ke kinsan ba wasa ba ce ta kawoni, Joyran…”
Ya kira sunanta ya nunata da yatsa kafin yace “Ki bani amsar tambayata kafin na turo jami’ar da za ta bincika min ke yanda ya kamata.”
D’aga hannayenta tayi dake d’aure tace “Shikenan na ji, zan fad’a ma ka Umad, amma…”
Marairaicewa tayi tace “Kar ka bari kowa ya ji maganar nan Umad, ka ji?”
Jajayen idonshi kawai ya zuba mata yana kallo, cikin shashek’ar kuka na munafurci ta fara fad’in “Tabbas da taimako na a cikin kai harin nan, sai dai ba da makami ba ko wata hanya ta daban, mun kasance muna soyayya ni da Khatar tun a makaranta, sanda yaya Kossam ke d’aukar nauyin karatuna da duk wasu buk’atuna, sai na fara jin kishi a kan ta ina jin haushin me yasa ba ni ba ce a matsayinta? Wata rana na zo hutu Giobarh sai mahaifinka ya umarci da mu shirya za’a yi taro a k’asar Egypt, mun tafi cikin farin ciki tare da ku da kuma yaya Kossam, a Egypt sai muka had’u da Khatar shi ma ya aje a lokacin ba’a masa wazirin sarkin Khazira ba, duk sanda k’afa ta d’auke ni da shi muna tare muna soyayyarmu, a nan ne har na samu damar fad’a masa abinda na ke ji a zuciyata game da yar uwata, tambayar da ya min ita ce *”Me ki ke so a yi kenan?”*
“Sai na fad’a masa ina so na zama sarauniyar Giobarh, na zama mai fad’a a ji a masarautar, da fari ya nuna min kishinsa saboda mun yi alk’awarin aure da shi, amma washe gari sai ya zo min da maganar wai zai cika min buri na, da na matsa masa me zai yi ne sai ya ce min *”Sarki Musail ne ya nuna sha’awarsa ga ‘yar sarkin Egypt, saidai ita ta nuna bata son shi d’an yar uwarki (Urab) take so, kuma sarki Musail ya bani wuk’a da nama na yi duk abinda ya dace dan ganin ya sameta, dan haka zan jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya.”*
” Na tambayeshi ban gane me ya ke nufi ba, sai ya ce min *”Yau da dare zan sa a kashe min d’an yar uwarki, hakan zai sa sarkina ya samu Juman, daga baya zamu bar duk shaidar da zata nuna sarki Musail ne yasa a yi wannan aika aika, kinga kenan mun haddasa gaba mai tsanani tsakanin masarautar Giobarh da masarautar Khazira, hakan zai sa sarki Wudar ya nemi d’aukar fansa ko ta ya ya, idan aka yi nasarar cin Giobarh da yak’i, a k’arshe za’a kafa sabuwar daula a Giobarh kuma ke zaki zama sarauniyarta, idan kuma aka yi nasara akan Khazira…”*
“Da sauri na tambayeshi to me zai faru? Sai ya ce *” Zan zama sarkin Khazira, ke kuma sarauniyar gaba d’aya Bussam, ya kika gani ?*”
” Na ji dad’i sosai har cikin zuciyata, hakan yasa na yi dogon tunani a lokacin sannan na bashi ta wa shawarar na ce *”Madadin ka sa a kashe Umad shi kad’ai, me zai hana ku d’auki hayar mahara da dama su kawo hari aasarautar nan yau cikin dare?*”
“Tambaya ta ya yie ye anfanin yin haka? Sai na ce masa *” Idan fa aka yi rashin sa’a aka kama wad’anda kuka turo, to shakka babu zaka kwana a ciki, dan gidan nan yanzu baibaye yake da hadimai da dogarai saboda yawan safakunan dake ciki, amma idan mutanen dayawa kuma kan mai uwa dawabi aka yi, to kai tsaye ba za’a zargi wani sarki ba, dukansu zasu dinga wa juna kallon kallo ne, a cikin hatsaniyar kuma sai a kashe Urab, ni kuma nasan mutuwar Urab daidai take da mutuwar Kossam, dan tana matuk’ar son yaron, kaga ni kuma ta wannan hanyar zan k’arasa kassara rayuwarta.*”
” Haka muka kwana da shirinmu, kuma mun yi nasarar aiwatar da abinda muka tsara, a hakane aka kashe Urab kisan wulak’anci, wanda sanadiyar haka mahaifiyarka ta yanki jiki ta fad’i, ba’a iya aiwatar da komai ba dan masarutu da dama sun rasa mutanensu a lokacin ko da kuwa hadimi ne, ni kuma daga lokacin sai…”
Fashewa tayi da kuka na gaske ta sunkuyar da kanta, wani wawan buga teburin yayi da yasa ta zabura kamar zata tashi tsaye, wanda hakan yasa fitsarin da take ji ya banko a guje ya taho mata daga zaunen da take, kwararararan da ya ji abu na zuba a k’asa yasa ya d’an yi jim yana saurarawa, a hankali ya tura kujerar da yake zaune baya sannan ya d’an lek’a, da sauri ya kalleta ya girgiza kai yace “Ina jinki.”
Yamutsa fuska tayi ta matse k’afafunta kanta k’asa saida ta gama tsiyaye fitsarin tas sannan ta d’ago a hankali ta kalleshi, a kausashe ya kuma fad’in “Ina saurarenki.”
Cikin sanyayyar murya tace “Wajen boka na kai yaya Kossam a India, nan ne aka bani maganin da kullum nake saka mata a abinci sannan nake shafa mata a jiki duk kwana uku, da wannan ne ta kasa anfanuwa tun daga waccen ranar sai jiya data tashi kamar a mafarki, kuma na samu abinda nake so, sai dai sarki Wudar bai aureni ba haka ma Khatar, sannan duk yanda na so na kashe mahaifiyar abun ya gagara, dan wani boka ma fad’a min yayi idan na matsa ni ce zan rasa raina, dan ita kam mutuwarta ba yanzu ba, amma dai ni da mahaifinka mun zama abu d’aya, a shekarun nan da aka d’auka ni da shi kamar mata da miji ne, saidai ban tab’a yarda shi ko Khatar da ke kawo min ziyara lokaci lokaci ba na d’auki cikin d’aya daga cikinsu, saboda ba wannan bane a gaba na, saida na fara gajiya da k’aryar da Khatar ke yi min a kullum cewa zai aure ni, sannan na dakata da d’aukar allura har na samu ciki da shi, sai kuma na yi k’ok’arin d’orawa Wudar saboda ina so abinda zan haifa ya zama magajin wannan masarautar, dan na fahimci Khatar ba zai tab’a zama fiye da waziri a masarautar Khazira ba, wannan shi ne abinda ya faru Umad, tunda na fad’a maka ka yafe min ka ji, kar ka hukunta ni dayawa.”
K’asa da sama ya harareta ya ture kujerar ya mik’e tsaye, bindigar ya d’auka ya sa a k’ugunshi yace” Mak’iyi na nesa ba wuya ka shawo kansa, amma mak’iyi na kusa ya fi kowane illa, shi mak’iyi zai iya dawowa masoyinka wata rana, amma mai maka hassada har abada baya tab’a canjawa, a haka za ki k’are Joyran, babu nan kuma babu can, doka ce za ta d’auki matakin daya dace a kan ki ba ni ba, dan waccen harin da kuka sa aka kai, yayi sanadiyar rayuka da dama, daga ciki kuwa har da yayana da nake matuk’ar so, sannan har da mahaifin shugaban hukumar nan ta mu, d’aya ne a cikin manyan bak’in da suka halarci taron.”