Hausa Novels

Lu’u Lu’u 41

Bismillahir rahamanir rahim_

*41*

 

Babban teburin falon b’angaren sarauniya Juman aka zauna cin abinci, wanda sarauniyar ta sa aka gayyaci kowa zuwa nan, bayan cokula babu abinda ka ke jin k’ararshi, saidai kallon juna da ake kawai da ido, wani kallon mai ma’anoni da fassara, wani kallon kuma na katari ne kawai ido su sark’e da juna.

Gyaran murya sarki Musail yayi ya aje cokalin hannunshi mai yatsu sannan ya had’e tafukan hannayen ya kalli sarki Abdallah da ke kujerar dake fuskantar ta Musail, duk da suna da d’an nisa haka ya d’aga muryarshi amma a tausashe yace “Ranka shi dad’e, ina ga tunda gaba d’ayanmu mun taru, me zai hana na fad’i abinda ya ke raina?”

Cike da karammawa ya lumshe ido shi ma ya aje cokalin hannunshi yace “Me kuwa zai hana, bismillah fad’i.”

Ayam ya kalla dake kujerar daf da shi wacce take kallonshi tana tsakurar abincin saboda kallon da Umad ke mata wanda ke kurar dake fuskantar ta, murmushi ya sakar mata yace “Da ma ina so ne na mik’a mulkin Khazira ga me abun, ma’ana Ayam.”

Waro ido tayi tace “Kyu (Me)?”

Da mamaki suka kalleta na sabon yaren da tayi inda Umad ya rumgume hannaye a ranshi ya furta “Wata sabuwa.”

Da sauri ta kalli inda sarki Abdallah yake tace “Grand Pah, ka ji me Pah ya ke fad’i? Gaskiya ni a’a.”

A sanyaye Juman ta kalli sarki Musail tace “Abban Ayam, ina ganin me zai hana idan ma mulkin zaka bayar ka ba wa mai buk’ata Zafreen, tunda ita ma ai ‘yarka ce kuma babba.”

Kallonta yayi a tausashe yace “A gaskiya bana so na sake aikata wani kuskuren, Zafreen hali na gareta babu abinda ta rage, talakawan Khazira sun sha wahala a a hannuna, bana so na sake saka su uku.”

Marairaicewa Ayam tayi tace “Gaskiya ne Mah, ni kinga bana son wannan hayaniyar, idan so samu na ne na samu wani keb’antaccen daji mai d’auke da nau’in kowace dabba, na zauna tare da su na rayu da su cikin farin ciki.”

Wata basarakiyar dariya sarki Abdallah da Musail sukayi, haka ma sauran mutanen saida suka dara, inda Bukhatir ya narke ido yana kallon Ayam kamar ya sumbaci bakinta sanda take maganar, Juman ma cikin dariya ta kalleta tace” Ke burinki kenan a duniya? Rayuwa da dabbobi?”

A hankali ta jinjina kai alamar e, maida kallonta tayi niyyar yi ga plate, sai kawai a tsautsayi suka had’a ido da Umad dake kallonta yana sakin b’oyayyan murmushi, suna had’a ido ta d’auke kai ta d’auki cokalinta, ajiyar zuciya ya sauke ya kalli sarki Abdallah yana d’aukar na shi cokalin shi ma a ladabce yace “Yallab’ai, ai ita d’in sarauniyar jeji ce, ina ga dalilinta kenan na shiga karatun gandun daji, kuma da alama wannan foresti猫re d’in za ta zama sarauniyar dabbobi.”

Da fara’a sarki Abdallah yace “Da gaske Umad?”

Jinjina masa kai yayi yace “Baka gani ba sanda suke hira da zaki, abun kamar al’amara.”

Waro ido tayi ta bud’e baki tace “Kai kai kai, ni d’in? Yaushe?”

Kallon Juman tayi da ke k’yalk’yala dariya tace “Hakane ko Mah?”

A nutse Musail yace “Ayam, maganar gaskiya nake fad’a miki, ki shirya zama sarauniyar Khazira.”

Turo baki tayi gaba tace “Pah, a gaskiya ban shirya ma hakan ba, sannan ka ga ina so na kammala karatu na, burina shine na zama major, sannan ni ban san komai a harkar siyasa ko sarauta ba, i can’t take this risk Father.”

Sarki Abdallah ne ya kalleta yace “Pourquoi pas ma cher?”

Yatsina fuska tayi tace “Haka kawai ba zan iya ba.”

Kallon sarki Musail yayi ya d’an masa hira da ido irin ta su ta manya, jinjina kai yayi irin na fahimta sannan ya ci gaba da cin abincinshi.

Suna tsaka da cin abincin wani bafade ya shigo tare da sunkuyawa alamar girmamawa yace” Sarki na, bak’i daga Giobarh sun iso.”

Zaro ido Umad yayi ya kalli bafaden yace” Giobarh?”

Da mamaki Musail ya kalli bafaden shi ma yace” Giobarh? Su wa ye haka?”

A ladabce yace” Sarki Wudar ne da kuma sarauniyarsa.”

D’an zaro ido Musail yayi yace” Manyan bak’i haka? M yake shirin faruwa kuma?”

Kallon bafaden yayi yace” Shikenan, ka musu iso.”

Sunkuyawa yayi sannan ya juya ya fita, Musail kuma mik’ewa yayi yana kallon Umad da yake kallon k’ofa yace” Ina fata ba maganar d’aukar fansa ba ne?”

Kallon Musail d’in yayi sai kuma ya mik’e tsaye shi ma yace” Ba wannan yallab’ai.”

Hadimai ne suka fara shigowa mata d’auke da manyan kwando na roba mai kyau tamkar wanda aka sak’a da kaba, an musu kwalliya lullub’e da yadi mai k’yalli.

Layawa sukayi su goma duk rik’e da kayayyaki a hannunsu, a nutse sarauniya Kossam da sarki Wudar suka shigo, kayansu kusan kala d’aya ne har kalarsu ne, kalar shud’in ta musu kyau ga ratsin fari da k’yalli k’yalli, inda duka rigunan na su ke jan k’asa musamman ma gyalen Kossam.

Duk mik’ewa mutanen teburin sukayi suka tunkaresu a nutse, cike da girmama juna da karramawa suka dinga gaisawa, suma a ladabce suka sunkuya suna gaishe da sarki Abdallah wanda suka ganeshi sosai duk da dai shekaru sun ja sosai.

Ayam dake bayan Musail tana hangen Kossam, sai yanzu ne take tuna lallai fuskar matar nan ce a hoton data gani d’akin Umad zuwanshi makarantarsu, dan yanzu fuskarta ta fi fitowa da kyau saboda an sha gyaran jiki da na kai, duk da ba kwalliya a fuskarta amma dai hoda da man leb’en data shafa kalar leb’en na ta sun sa ta k’ara kyau.

Ta shagala da kallonta sosai ta ji murya kamar daga sama an ce “Zo nan ‘yata, gujajjiya daga mahaifiyarta.”

Dariya mutanen d’akin sukayi sai ita data zabura ta sake kallon matar, hannun Kossam d’in ta kalla data mik’o mata, a hankali ta mik’a mata hannun sannan ta taka zuwa gareta, kallon juna sukayi sai kuma Ayam ta sunkuyar da kanta k’asa cike da kunya tace “Mah…”

Hancinta Kossam ta ja tace “Shine dan kinga bana iya magana a lokacin kika gudu kika barni.”

D’aga kai tayi ta kalli k’wayar idonta, cikin dubara Kossam ta janye na ta idon saboda gagara da tayi wajen kallon idon Ayam d’in, d’an giggilma idon tayi tana kallon gefe gefe, lura da haka yasa Ayam sauke idonta k’asa tace” Ki yi hak’uri Mah…gani yanzu.”

Kallon fuskarta tayi da murmushi a fuskarta tace” Ba zaki sake guduwa ba?”

Girgiza kai tayi tace” A’a Mah, can ma na gudu ne saboda ina so zan ga iyayena.”

Kyab’e fuska Kossam tayi tace” Dan haka zaki sake min nisa? Nasan haka zai faru, shiyasa na zo da shirina dan na wa tubkar hanci.”

D’an d’aga ido tayi ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kai, a nutse ta tallabo hab’arta ta zubawa fuskarta ido, cikin sanyayyar murya tace” Zafeera, za ki zama ‘yata ta hanyar auren d’ana Umad?”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button