Hausa Novels

Lu’u Lu’u 41

K’uri ta zuba mata ido tare da jin dokawar k’irjinta, kasa cewa komai tayi sannu sannu har ta samu ta sunkuyar da kanta k’asa, yanda falon yayi shiru Juman kuma ta d’aga labb’anta za ta yi magana sarki Abdallah ya mata alama da ido tayi shiru, hakan yasa d’akin ya d’auki shiru na wasu mintoci, kamar an tsikani Ayam ta d’aga kanta tana murmushi tace “Mah, na yi farin ciki da kika samu lafiya, zan iya zama ‘yarki mana…ko ma na ce na za…ma.”

Ta k’arashe tana kallon inda Umad ke tsaye wanda ya zuba mata ido yana kallo, da fara’a sarauniya Kossam tace “Da gaske za ki zama ‘yata? Sirikata?”

Da ido ta mata alamar e, hakan yasa Kossam fad’ad’a murmushinta ta kalli hadiman dake bayansu, mik’a musu hannu tayi d’aya daga cikinsu ta bata kwandon hannunta, tallabo kwandon tayi daga k’asa sannan ta juyo ta kalli Ayam, Musail da Juman dake bayan Ayam su ma ta kalla tace “Ina neman izininku da ku ba wa d’ana Umad auren ‘yarku Zafeera?”

Musail da Juman kallon juna sukayi, a k’ayace Musail ya saki murmushi Juman kuma ta b’oye dariyarta, sarki Abdallah ma haka tare da kusan wanda ke wajen.

Da mamaki suke kallonsu ta ya suke musu dariya daga wannan maganar, da sauri Umad ya matso kusan Kossam cikin rad’a d yarensu na Gallois yace mata “Mahh…kiyi shiru mana, ki zo zamuyi magana a wane.”

Kallonshi tayi ta kyab’e fuska kamar zatayi kuka tace “Me na yi da suke min dariya? Sai ka ce na nema maka auren matarka?”

Bai san sanda ya tintsere da dariya shi kan shi, abar da ya jima bai yi ba sai gashi yana k’yak’yatawa sosai duk da k’ok’arinshi na son rik’eta, cije leb’en k’asa tayi ta sake yin takwaf takwaf da fuska, da sauri ta mik’awa Ayam kwandon dake hannunta ta d’aga hannaye za ta daki Umad, da gudu cike da nishad’i ya lab’e bayan Wudar ya ruk’umk’umeshi yana fad’in “Pah ka gani fa, yanzu hakane ya dace mu yi farin cikin samun lafiyar Mah?”

Ita kam k’ok’arin sai ta dakeshi take tana cewa “Ja’iri kawai, ta ya kai ma za ka dinga min dariya daga magana, me na fad’a ba daidai ba? Zaka zo nan ko sai na…”

Cikin sa’a ta rik’o wuyan rigarshi ta jawoshi gabanta, fad’awa yayi jikinta yana ci gaba da k’yalk’yala dariya yace “Yi hak’uri Mah, zan fad’a miki wani abu to.”

Duk da Juman na jin kunyarta dan k’iris ya rage su zama surukanta, amma gashi ‘yarta ta zama surukarsu, cikin ladabi tunda suna sama da ita tace “Yar uwa, ki rabu da shi haka mana, dole ne fa a miki dariya saboda abinda kika zo d shi.”

Dakatawa tayi ta kallet tace “To me ya sa za’ a min dariyar?”

Cikin danne dariya saboda yanda tayi maganar tace “To ai matarsa ce kike nema masa aurenta, kinga kuwa dole mu yi dariya.”

Zaro ido tayi ta kalli Ayam ta kalli Juman, sannu sannu sai ta dinga juyawa tana kallon mutanen wurin dake ta sakin murmushi ban da Bukhatir kawai.

Da mamaki tace “Amma….” Bata fad’a ba ta dakata saboda wata damk’a da Wudar ya ma hannunta da k’arfin gaske, da sauri ta juya ta kalleshi.

Gaba d’aya fuskarshi da yanayinshi ya nuna ya shiga wani hali ne na tashin hankali da kid’ima, yanda ya kakkafe idonshi kan fuskar Juman da ta yi maganar, ga kuma d’aya hannunshi dake kan saitin zuciyarshi baki bud’e kamar zai yi magana amma kuma maganar ta mak’ale.

Gyara tsayuwarta tayi cikin rad’a ta dafa d’aya hannunshi daya rik’e na ta tace “Sarki na, lafiya? Me ya ke damunka ne?”

D’aga baki ya sake yi da kyau yana so sai yayi magana, amma sai ya fara sauke wani irin numfashi kamar yana fizgoshi ne da k’arfi saboda barazanar barinshi da yake, idonshi da ya kafe kan Juman ne suka d’an motsa da k’arfi sai kuma suka rufe ruf, gagggaf jikinshi ya d’auki rawa haka yasa k’afafunshi ma suka kasa d’aukarsa, luuuuu ya tafi zai fad’i Umad yayi caraf ya tallabeshi.

Saidai dake gaba d’aya ya saki jikinshi sai Umad d’in ya d’an motsa kamar zai fad’i shi ma, da azama Haman ya kama mi shi suka rik’eshi da kyau, hankali tashe suka rufa a kanshi wasu na firfita d’aya a cikin k’annan Bukhatir ta kawo ruwa aka shafa masa, shiru bai dawo hannaycinsa ba kuma Umad ya saurari harbawar jijiyar wuyarshi, kawai dai rud’u ne da tashin hankali ya ziyarce shi lokaci d’aya.

Musail ne yace “Ku kaishi d’aki ku kwantar, bari a kira likitan cikin gida sai ya dubashi.”

Cire masa kambun kanshi Kossam tayi sannan su Umad suka ja shi zuwa d’akin Umad d’in da ya sauka. Inda Musail ya kira babban likitan ya kuma ce yana zuwa yanzu.

Kossam dake tsaye juyowa tayi kan Juman da mamakin da har yanzu bai barta ba tace “Yar uwa, garin ya haka ta faru? Yarinyar da nake mafarkin ta zama sirikata, sai ku ku tabbatar min da mafarkin.”

Kama hannunta Juman tayi tace “Muje ciki sai na fad’a miki komai.”

Zasu wuce Juman ta sake juyowa ta kalli hadiman gidan tace “Dan Allah ku samawa kowa masaukin da ya dace da shi, sannan kayan nan babbar tsaraba ce daga surukanmu, dan haka ku adana su waje mai kyau, anjima zan zo na duba.”

Ciki suka shige hadiman kuma suka shiga yin abinda ta umarcesu, Ayam kuma mik’awa wata hadimar kwandon hannunta tayi sannan ta kama hannun sarauniya Bilkees suka nufi hanyar d’akinta, juyowa tayi ta kalli k’annan Bukhatir tace” Ku zo mu je.”

Bin bayansu sukayi su ma suka yada zango a d’akinta.

*Wudar* ma cikin gaggawa likita ya zo ya duba shi, jininshi ne yayi mugun hawa sosai hakan yasa aka masa allurar bacci mai nauyin gaske, Umad da Haman barinshi sukayi a d’akin, inda Umad ke cike da mamakin abinda ya jawo wa mahaifinshi shiga wannan halin, shin soyayyar da ya ke wa Ayam ce ta kai wannan matakin? Ko kuma dai ya shirya wani gagarumin abu ne ga auren d’an daya rage masa? hakan yasa jin yayi auren ya jefashi a wannan halin? Ko kuma dai alhakin mahaifiyarsa ne Allah zai fara cire mata hakk’inta dalilin Ayam?

*A gurguje*

 

A al’adar k’asashen dama idan har an amince da neman izinin auren, to a cikin kayayyakin da iyayen miji ke kawowa har da kayan gyaran jiki, dan haka Juman bata tsaya b’ata lokaci ba wajen duba kayan nan ta d’auki duk abun buk’ata wanda ya shafi dukhan, dilka, madara, zuma, kurkum, haska amarya, man ja mai kyau. Hankali kwance a nutse suka sakata tsakiya ana ta darjewa a nutse, jakadiyar Juman da ita kanta Juman d’in, ga kuma Kossam da ta aje surukantaka a gefe tana shafawa Ayam d’in dilka da kan ta, ga kuma sarauniya Bilkees dake zaune tana taimaka musu da wasu abubuwa.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button