Lu’u Lu’u 41

Awa d’aya suka d’auka kafik daga bisani tayi wanda da zallar sabulu na zuma da madara, tana fitowa Bilkees ta bata madarar da aka dama da kauri da sanyi kad’an ta shanye tas, mai ta shafa wanda shi ma duk cikin kayan da aka sako ne sannan ta saka sassauk’an riga ta gabatar da sallah la’asar, bayan ida sallarta ne Kossam ke tambayarta abinda ta yi, nan Juman da Bilkees suka fayyace mata komai game da addinin har saida ta ji sha’awar shi ga ita ma.
Ko da duhu ya fara shigowa masarautar Khazira ta d’auki harami ta kuma canza kala, dan kuwa ma’aikata daga kampani na musamman a wajen tsara wajen taro aka d’auko suka k’awata gidan, walwali mai d’aukar ido da kayan ado da alatu ta ko ina aka zagaye gidan kamar ba shi safiyar yau yayi gobara ba, shiga da fita kawai hadimai ke yi suna ta harkoki na k’ayata wajen bak’i da abubuwan ci da shi, haka ma babban tureburin da amarya da ango za su zauna.
A d’aki kuma masu kwalliya na musamman aka kawo wanda kafin su shiga saida aka cajesu da akwatin kwalliyarsu, mai gyaran kai tana aikinta cike da k’warewa, haka mai wankin k’afafu da yanke farce, sannan aka mata gyaran farce na hannu aka shafa mata verni kalar fari da ba’a cika shaida an saka ba.
Duk da har yanzu gashinta bai yi tsayi ba, amma da aka mishi wani irin gyara mai murd’ewa sai wanda zai ganta a lokacin ya d’auka tsayin gashin ne yasa aka mummurd’eshi hakanan, gashi an bar mata shi a yanda yake kalarshi ta asali maroon da tsili tsilin yellow yellow. Saida aka d’auki minti talatin ana gyara mata girarta da girar idonta, yanda ake so su tsaya cak ba tare da sun rabe da juna ba sannan su mik’e kuma su lank’wasa, daga haka aka ci gaba da mata saukakk’an kwalliya wacce ita kanta ta zuba ido take so ta ga yanda fuskarta za ta yi da kwalliya abar da bata tab’a yi ba.
*Alhamdulillah.*
The post Lu’u Lu’u 41 first appeared on 2gNovels.com.ng.
[ad_2]