Lu’u Lu’u 42

Turo baki tayi ta sake kai bakin tana sha, saida ta shanye tas sannan ta d’auke mata kofin daga bakinta, mayar da kofin tayi ta aje kan farantin sannan ta d’auki wata dunk’ulalliyar madara wacce had’i ne na musamman ake ba wa amarya a wannan lokacin, shi ma a baki ta saka mata ta b’antara ta taune sannan ta cinye sauran ragowar, shi ma dai tana cinyewa yar k’aramar tasa ta d’auke mai d’auke da zuma a ciki farar saka ta saka k’aramin cokali ta dinga ba ta har sau uku sannan ta aje.
Gyara tsayuwarta tayi ta fuskancesu gaba d’aya, akan farantin ta d’auki wata k’aramar kwalbar turare ta mik’awa Umad tace “Sai ka fesa mata.”
Karb’a yayi ya bud’e murfin ya fesa mata a jiki, lumshe ido dukansu sukayi saboda tasirin turaren, sai dukansu suka daure ta hanyar bud’e idonsu kamar babu wani abu da ya faru.
Aje kwalbar ta yi sannan ta d’auki zoben azurfa ta mik’awa Ayam tace” Ki saka mishi a yatsar data miki.”
A sanyaye ta amsa tana kallonshi shi ma kuma kallonta yake, hannunshi na hagu ya mik’a mata wanda yake sanye da wani zoben a yatsar kusa da k’arama, kallon yatsun na shi tayi da kyau, a hankali ta kai yatsunta biyu ta cire mi shi wannan zoben sannan ta saka mishi na hannunta, kallonta yayi sosai murya kasa k’asa yace “Wannan fa mai daraja ne.”
Ba tare data boye muryarta ba ta amsa mishi a yaren Italy tace “Shi ma mai darajar ne.”
Tana gama fad’a ta kalli iyayensu da suma ke kallonsu suna murmushi duk da basu ji me ta ce ba ita, amma zoben na shi d ta saka a yatsarta babba ya k’ara basu sha’awa da dariya, wanda shi ma kuma hakan ya masa dad’i.
Da haka Juman ta dinga gabatar da al’adarta har ta ida sannan suka ba wa bak’i damar zaunawa a mazaunansu dan su ci abinci, sosai d’akin taron yayi shiru dayawa saboda kowa mai ji da kan sa ne, bayan k’arar cokula da takalmin hadimai dake yawon raba abinci da kowane teburi babu wata hayaniyar, sai magana k’asa k’asa kawai da hirar mutane ke tashi.
Ganin hankalin mutane baya kansu yasa Ayam yunk’urawa tare da fad’in “Ya Allah.” Ta mik’e, takawa tayi zata sauka daga matakalar d’aya yace “Ina za ki je?”
Juyowa tayi ta turo bakinta gaba tana jujjuyashi tace “To ai ban san an d’ora dokar hana d’aya daga cikinmu tashi a nan ba.”
Tana fad’a ta juya ta ci gaba da tafiyar ba tare da ta ji daga gareshi ba, da kallo ya bita yana murmushin gefen labb’a, tafin hannunshi yasa ya kama gemunshi dake ta k’yalli yana wasa da shi a ranshi ya ayyana” Rigima ko? To ai na bayar da hak’uri, kuma ma ai halalina ne.”
Wani murmushin ya kuma saki ya bi d’an k’ugunta da kallo, cije leb’en k’asa yayi ya d’an kawar da idonshi kad’an daga kanta yana tuno yar gajeruwar had’uwarsu da ita.
Sake maida idonshi yayi kan ta dan baya jin zai iya kawar da gani gareta na sakan biyu, saidai abinda ya gani yasa ya zaro ido har ya furta “Iyeeeh!”
Bai ankara da ya mik’e tsaye ba saida ya ji ya d’aga kafarsa ya taka k’asa, da sauri ya shiga takawa da gaggawa ya isa gareta, yana zuwa yay karaf ya karb’e kofin kwalbar mai shak’e da ice cream dan bak’in wanda take daf da kai wa bakinta da d’an cokalin k’arami.
Da sauri ta kalleshi suna had’a ido ta kyab’e fuska tace “Sha zan yi fa, kai ma ka d’auki na ka mana.”
Hannunta ya rik’e gam a cikin na shi ya d’ora kofin kan wani tebur sannan ya jata zuwa wani corridor da babu kowa sai masu wucewa.
Neman fizgewa take saida ya kai ta inda yake da buk’ata kad’ai ya dakata tare da mannata da bangon, saida ya mata runfa da k’irjinshi kamar zai fad’a mata sannan ya k’urawa fuskarta ido, hakan ya haifar da kusanci sosai a tsakaninsu ta yanda numfashinsu ke gauraya, k’asa ta sauke idonta tana wasa da hannayenta wanda bai ko bata damar had’esu wuri d’aya ba, cikin narkakkiyar murya a sanyaye yace “Kar ki sha sanyi kin ji…*Sajeeda*.”
D’aga idonta tayi ta kalleshi sai kuma tayi saurin sadda kanta k’asa, a hankali yasa yatsanshi ya tallabo hab’arta ya tilasta mata kallon fuskarshi, k’asa tayi da idonta sosai yanda sam bata kallonshi, daf da fuskarta ya sake matsawa yace” Me ye?”
A hankali ta girgiza kai cikin gargadar murya kamar zata b’alle da kuka tace” Ka…wai dai…na ji..ka kira…fassarar suna na ne da yarenku.”
Mamaki ne ya bayyana a fuskarshi yace” Kenan kinsan Ayam yana nufin Sajeeda ne?”
A hankali cikin dubara ta d’aga kai tare da fad’in” E.”
Gyara tsayuwarshi yayi sosai ya sake babbaketa ta yanda ba zata motsa ba yace” Kenan ni ma kinsan fassarar na wa sunan?”
Shiru tayi bata amsa mishi ba sai k’ok’arin kawar da kanta da take, sake cewa yayi” Uhum! Ina jinki.”
Kallon k’wayar idon shi tayi da sauri tace” *Faruk* mana, na sani ai.”
Murmusawa yayi tare da sake tallabo hab’arta yace” To e ye na hassalar? Ki bani amsa mana da girmamawa.”
Cikin fad’a ta ture hannunshi tace” Ni ka matsa zan wuce.”
Har zata rab’ashi ta wuce ya rik’o hannunta hakan yasa ta tsaya cak, juyawa tayi suka kalli juna, cike da sigar tsokana yace” Ba kya tsoron abinda zan miki idan aka ware mana d’aki ne?”
Da mamaki ta kalleshi tace” Ware mana d’aki kuma? Haka ka ke tunani?”
Gyara tsayuwarta tayi tace” Yallab’ai, ka ga dai ai ina jin kunyarka ko? Kuma ina ganin kimarka da darajarka, to me yasa ba ka ji kunyar abinda ka yi ba?”
Cike da danne dariyarshi duba da yanda take maganar yace” Amma ai na baki hak’uri ko? Kuma na ce zan dinga fara bayar da hak’urin kafin na yi yanzu.”
Hawayen data rik’e tun sanda ya matse mata wuri ne ta ji sun taho mata masu zafin gaske, nunashi tayi da yatsa tace” Dama can da nufi ka yi na farko? To ka sani ni ma n san ‘yancin kai na kuma zan k’waci.’yancina.”
Yatsar da take nunashi da ita ya jawo da k’arfi hakan yasa ta fad’o jikinshi bata shirya ba, matseta yayi a jikinshi sosai ya kuma had’ata da bangon nan, k’ure fuskarta yayi da kallo har ya had’a hancinsu wuri d’aya, cikin taushin murya numfashinsu na gauraya yace “…
*Nagode sosai yan uwa da uzurinku gare ni, Alhamdulillah mun gama sabga lafiya.*
*Alhamdulillah*
[ad_2]