MADADI 1-END

MADADI Page 11 to 20

Tana tashi da asubah ko sallah ba tayi ba ta dauki wayarta ta kunna ta shiga dubawa wai ko ya turo mata da amsa, wayar ta kai minti goma a hannunta tana jiran shigowar replay dinshi bai shigo ba, a sanyaye ta mike ta fita domun daura alwala, tana shigowa dakin ta sake daukar wayar tana dubawa, ganin alamun shigowar sa’ko yasa hannu na rawa ta bud’e! tsaki! mai ‘karfi taja ganin messege din daga *Mtn* ne, jefar da wayar tayi kan katifa, idanunta na kokarin kawo ruwa ta shiga tayar dasu Saddiqa daga baccin da suke………

Suna bude ido tace”Ku tashi kuyi alwala kuyi sallah.” Saddiqa ta sauko da sauri ta bude akwatin kayansu makilin da brush ta dauka ta fita domin daura alwala…..Cikin tsawa ta kalli Mussadiq kamar shi yayi mata laifin tace”Kai ba zaka tashi ba sai na gaggaura maka mari ko.”! Yaron ya tashi a furgice yana kallonta! da hannu ta nuna masa ‘kofar fita tace”Kaje kayi alwala gari ya waye.” sakkowa yayi daga katifar shima ya dauki abun wanke baki ya fita.

Hijab ta zura ta gyara dadduma ta tayar da sallah, Tana idarwa ba tayi wata adduar kirki ba ta sake daukar wayar tana dubawa, har yanzu dai babu amsa! Tsaki ta dinga ja zuciyarta na wani irin tafarfasa! babu shakka Abbah Abbas da gaske yake! tasan yaga text d’inta kunya ta hana shi bata amsa shiyasa ya shareta.

Numbar Salim ta laluba ta shiga kira. sai dai wayar a kashe take dan bai tashi ba ballanta ya kunna wayar……Mi’kewa tayi ta koma bakin katifar ta zauna had’e da cire hijab din jikinta, Numbar Abbah Abbas din ta sake nema ta ‘kara tura masa wani text in kamar haka.

_Abba ina jiran amsa nasan dai kaga text d’ina dan Allah ka bani amsa shin kaine ka nemi aure na? ko kuma su Baba malam ne suka baka ni.”?_

Tura masa tayi ta tsirawa wayar ido tana adduar Allah yasa yayi mata magana………….Shi kuwa Abbah Abbas yana kwance Halisa na matsa masa a jikinsa yana lumshe ido baccin da ya tara kwana da kwanaki ne yake damunsa, tinda Halimatu ta rasu bacci da nutsuwa suka ‘kaurace masa, mutuwar Halimatu babban gi’bi tayiwa rayuwarsa, gani yake ma ba zai ta’ba samun mace tagari kamar ta ba, Yayi yun’kurin auran Naja’atu ne ba dan komai ba sai dan yasan ita d’in tarbiyyar Halimatu ce yana kwadayin ta zama matarsa domin hausawa suna cewa gida bai ‘koshi ba to ba za’a bawa dawa ba, bayan haka kuma yana tausayawa ‘yan ‘ya’yansa sosai saboda yanxu suna bukatar mai kula dasu sun saba da mamansu sosai dole idan suka dawo gidan suka ga babu ita su shiga damuwa, amma duk rintsi idan suna kallon Naja’atu a gidan kuma a matsayin matarsa to zasu samu sassauci a tare dasu. 

Babban abinda yake d’aga masa hankali acikin al’amarin shine! yanda zai tunkare su da maganar! Salim da Naja’atu gabadayan su bai san abinda zai ce musu ba, Salim bashi da Uban da yafi shi, hakan nan itama Naja’atu bata da uban da yafi shi, tabbas da zai iya hakura da ya hakura ya kyalesu sunyi auransu, amma ba yajin zai iya janye kudirinsa ba dan komai ba sai dan samun walwala da farin cikin ‘yayansa guda biyu, saboda ya riga ya sani cewar babu wata mace da zai aura ta ri’ke masa su tsakani da Allah! shiyasa yake ganin auran Naja’atun shine yafi alkairi a garesu baki daya.

‘Dan juyawa yayi ya d’auki wayarsa ya bud’e text din ya sake bud’awa domin ya sake karanta sai yaga wani ya sake shigowa, Ya bude idonsa sosai yana karantawa! Murmushi yayi wanda yasa Halisa kallonsa da sauri tace”Allah yasa alkairi ne naga kana murmushi.” Kallonta yayi yana kokarin rufe wayar dan ganin tana le’ko da kanta tana so ta ga abinda yakewa murmushin, a hankali yace.”Alkairi ne insha Allahu.” Tace”To Allah ya tabbatar mana dashi, mikewa tayi ta fita daga dakin tana fad’in “Bari na shiga kicin na shirya abin karin kummalo.” Ya bita da kallo Ba tare da yace mata komai ba, ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar ta daga d’akin, tabbas idan Halisa taji wannan babban al’amarin akwai tashin hankali! ya riga yasan halinta da mugun kishin tsiya! uwa uba kuma tsakaninta da Yarinyar basa jituwa ko kadan yanzu yanda zai tunkareta da maganar yake tunani…….Kira ya shigo wayar dake hannunsa, koda ya duba numbar Naja’atun ce yayi serving da My doghtar! kamar kada ya daga sai kawai yayi ‘kundumbala ya d’aga wayar yana d’an gyaran murya, kafin ma yace wani abu yaji shashshekar kunanta a kunnasa.

Jikinsa ne yayi sanyi ya sassauta murya irin yanda yake mata idan tana irin wannan kukan yace.”Dota ya akayi kuka da sassafe kiyi shuru muyi magana ko.”!! hanci ta sha’ka! zuciyarta sai tafarfasa take tace”Abba tun jiya na turo maka da text baka bani amsa ba kuma nasan ka gani dan girman Allah ka bani amsar abinda na tambayeka ko na samu zuciyata tayi sanyi.”””” Jim yayi kafin yace.”Kinga ni ban ga text d’inki ba ballanta na baki amsa amma kome kika rubuta min a text din ina sauraranki yanzu ki fad’a min.”

Cikin rawar baki tace”Jiya bayan kasa Salim ya kawo mu gidan Baba Malam shine naji suna wata magana wacce tasa raina ya kusa futa daga jikina, ashe wai kai ba kaine ka haifeni ba , sannan babban abinda ya furgita ni yasa na shiga cikin halin damuwa da tashin hankali wai kaine da bakin ka kace musu su baka ni na zama *MADADIN* matarka da ta rasu, shine nake ganin kamar sune suke so suyi wannan had’in da bai dace ba! ai abun kunya ne ace wanda nake amfani da sunansa ako ina a matsayin mahaifina aji shine kuma zai aureni ina zan saka raina idan hakan ya tabbata.”!! Cikin sar’kewar murya ta ‘karasa maganar……..Shuru yayi kawai yana jin saukar numfashinta a kunnansa bakinsa yayi masa nauyi gabad’aya ma ya rasa me zai ce mata.

Murya na rawa tace”Abbah wannan shurun da kayi yana nuna min cewar da gaske ne maganar daga bakin ka ta fito!!! Innalilihi wa’ina ilahi raji’un! kaico da wannan furucin naka! Abbah! dan girman Allah ka janye wannan maganar da kayi, na rantse da Allah ba zan iya zaman aure da kai ba ni a matsayin Uba na dauke ka.”

Tana wani irin kuka take masa maganar, Yaji jikinsa duk ya mutu! Gumi ne ma yake tsatstsafo masa kamar ba safiya ba, da kyar ya iya cewa” To naji maganar ki zanyi shawara a kai idan da akwai yuwuwar na hakura dake zan samu su malam d’in na fad’a musu duk shawarar dana yake, ki daina kuka haka kada ki janyowa kanki wani ciwon na daban.” Tace”To Abbah ni da daina kuka ai sai naji maganar wannan auran ta rushe sannan zan daina kuka.”!! Mamaki ya kama shi, da jin maganarta sai ma ta bashi dariya yayi kad’an kafin yace.”Naja’atu me yasa bakya son na zama abokin rayuwarki.”? Taji wani irin fad’uwar gaba jin abinda yace. Tace.”Abbah Please ba girman ka bane dan Allah kada ka ‘kara yi min wannan maganar kai ubana ne *Salim* kuma shine abokin rayuwata.” Kishi ne ya kama shi jin abinda tace kawai sai ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan kashe wayar tasa, ta juya tana kallon Bayanta, Saddiqa da Mussadiq sun futa daga dakin tun d’azu! taji dad’in hakan, sai ta mike itama tabi bayansu dakin Baba Talatu.

Suna zaune a kusa da Baba Malam suna karyawa da kunu da kosai ta shiga da sallama a bakinta, a hankali ta tsuguna kusa da Baba Malam tana gaishe shi ya amsa cike da kulawa yana d’an nazarinta ganin idanunta sunyi jawur! yasa yace.”Ya kwanan kuka.”? 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button