MADADI Page 21 to 30

Jin tana nema ta ‘ballo mata ruwa yasa ta shiga kicin din tana d’ura mata ashar! tana ingizata wai sai ta fita, Naja’atu ‘yar taurin kai tace” Wallahi ba zata fita sai ta gama abinda take.
Saddiqa ganin abin na neman ca’bewa sai ta fita daga kicin din tana share hawaye kai tsaye dakin Abbansu ta nufa tana kuka……….”Dan abu takazan ki a gidan ubanki muka goya d’an shege kinji yarinya da sharri.” Halisa tafada tana kokarin doke mata baki, ita kuwa fizgewa tayi ta matsa gefe tana gyara wuyan rigarta tace”Haba anti Halisa komai ‘boye-‘boyen ku mun sani Wannan Shamsiyyar sai da tayi cikin shege kafin ayi mata aure yanzu haka d’an data haifa yana gidanku gurin mahaif….Kafin ta ‘karasa halisa ta kaiwa bakinta duka! ta kauce da sauri tana fad’in “Allah ya isa wallahi.”! Karaf! a kunnansa lokacin da yake kokarin shigowa kicin din shida saddiqa, Halisa na ganinsa ta fashe da kuka tace” Yanzu Naja’atu ni kikewa Allah ya isa me nayi miki kawai daga na shigo kicin inayi muku sannu da aiki ashe zaki iya zagin Halimatu.”? Abbah Abbas ya dinga kallonta da ‘bacin rai a tare dashi yace.”Rashin kunyar taki ashe har ta kai haka? Yanzu baki duba girmanta ba kike zaginta wato kin manta maganar mu dake ko.”
Kuka tasa tace”Wallahi ba haka bane dik abinda ta fad’a ‘karya takeyi ai ga Saddiqa nan a gabanta akayi komai kuma ka tambaye ta kaji, haka kawai muna aikinmu ta shigo tana zagin mu wai bamu iya komai ba mu fita mu bar mata kicin dinta, shine nace ta bari mu ‘karasa ta’ki bari tazo tana dukana.” Itama ta ‘karashe maganar tana kuka had’e da ri’ke bakinta.
Abbah Abbas dik sai ya rasa ma maganar wa zai dauka, Halisa ta goge hawaye kamar gaske tace”Tunda fitina da sharri zaki dinga yi min a gida to zaki bar min gidana dama ni kikazo kika samu a gidan, dan bazan zauna dake ba watarana kisa hannu ki dake ni da girma da komai ni ba’sa’ar ki bace ballanta na nayi kishi dake, Halimatu ce dai-dai dani, dan haka ni a matsayin kanwa na dauke ki ba kishiyasa ba to tunda abin ya zama haka zaki bar min gida ki tafi naki ko kuma ni na bar miki gidan.”
Tana gama maganarta ta fita daga kicin din tana goge fuskarta
Halisa na fita ya juyo kanta tana rab’e jikin bango (garu) tana matse fuskarta, fad’a ya shiga yi mata wanda yake nuna mata cewar ya yarda da duk maganganun da Halisa ta fad’a tunda gashi da kunnansa yaji lokacin da take yi mata Allah ya isa! Sunkuyar da kanta ‘kasa tayi tana hawaye tana jinsa sai fad’a yake mata wai lallai idan tana son zama dashi to ta zauna lafiya da kowa a gidansa, taji kamar tace masa ai dama ba sonsa take ba da zaiyi wannan maganar ko yanzu akan ‘kaya take ya saketa ai babu dole, kwarjinsa ya hanata cewa komai kawai sai ta fita daga kicin din da gudu ta nufi dakin su Saddiqa tana kuka! Ya bita da kallo mamaki wato yana mata fada ta mai dashi soko ta barshi a tsaye, girgiza kansa yayi ya nufi palon….Ita kuwa Halisa taga lokacin da Naja’atun ta shigo palon tana kuka, sai farin ciki ya cika mata zuciya dama tasan da wuya ya’ki daukar maganar da tayi, Gani yayi duk yaran sun shirya cikin uniform ya kalli Saddiqa yace.” Yi sauri ki fito muku da bresk fast di n kafin Salim din yazo.” Saddiqa da Mufida suka nufi kicin din da sauri sune suka shirya gurin cin abincin tsaf! yaje ya zauna gurin cin abincin tare da yaransa, Saddiqa ta had’a masa tea ta zuba masa doya wacce zata isheshi, Albarka yasa mata ya dauki cup din tea yana sha, yana neman numbar Salim a wayarsa.
Salim na draving yaja tsaki kafin ya dauki wayar, Yace”Afuwa Kawu ganinan kan hanya.” Yace.”Okey kayi sauri kada kasa su makara ko.” Yace.”Insha Allah nan da mintina biyar zan karaso dan na shigo unguwar.” “Okey.” Yace ya kashe wayarsa ya maida hankalinsa gurun abincin dake gabansa…
Halisa ce ta fito daga daki tana wani salo-salo idanunta sunyi jawur! zama tayi kusa da kujerar Saddiqa ta dafa kanta cikin kissa tace”Sannu da aiki Saddiqa .” A dan tsorace ta amsa da “Yawwa Mommy.” Kallonta yayi yace.”Zamu fita tare yanzu za muje hospital mafi kusa a dubaki dan bana son zama da lalura.” Ta sake marairaicewa da fadin “Wallahi ba kaji yanda nake jin jiki ba gashi yarinyar nan ta ‘kara mun wani ‘bacin ran.”
Yace.”Ai laifin ki ne tunda kin san halinta me yasa zaki biye mata kuyi ta cacar baki a gaban yara duk ranar data zage ki a gaban yaran nan mutunci ki ya zube wallahi gwara ki kama kanki.”
Da sauri tace”Dan Allah ka bar wannan maganar da kake kamar baka san halinta ba kafin na fad’i d’aya ta fad’a min goma ni wallahi ban shiga kicin din da wata manufa kawai dai ta raina ni ne shiyasa bata ganin girmana amma yanzu na yanke hukunci kawai ta bar min gidana shi yafi amfani idan kuma lallai a gidan nan zata zauna to a gyara mata d’aya side din taje can ta ‘karata.”
Yace.”Sai an kwana biyu tukkuna abinda dai nake so dake anan shine ki cigaba da hakuri kuma kina kokarin ri’ke girmanki idan kin kama mutuncinki na tabbata komai rashin kunyarta ba zata zage ki ba…..Halisa shuru tayi tana jijjiga ‘kafafunta, Saddiqa ce ta had’a mata tea ta zuba mata soyayya doya da wainar ‘kawai akai tace “Mommy gashi kiyi break .” Cikin ya’ke tace”Nagode Saddiqa Allah yayi muku albarka.” Duka suka amsa da amin harda shi,
Salim ne yayi sallama ya shigo hannunsa rike da key na mota, Yaran ne duk suka mike suna gyara zaman jakar makarantarsu, Salim ya shiga rarraba ido a palon Naja’atu kawai yake so yayi tozali da ita, da bai ganta ba sai ya nufi dannig area d’in yana wani shafa kansa kai daka ganinsa kaga munafiki….Hannu ya mikawa Abba Abbas suka gaisawa yana wani risinawa kamar mutumin kirki! Ya gaishe da Halisa, tana washe baki ta amsa tana tambayarsa Yaya Ramlatu.
Abba Abbas ya mike hade da daukar wayoyinsa dake kan teble din, ya kalli Salim da fad’in “Ka kai yara skullu daga bisani sai ka biyo ni kasuwar daga baya zamuje hospital da Halisa bata jin dadi.” Salim yace.”Ayya Sannu Big Aunty ashe ba kiji dadi ba Allah ya sawwak’e yasa kaffara ne.” Halisa ta mi’ke tana dan ya mutsa fuska tace”Wallahi kuwa ” ameen ya rabbi idan ka koma gida ka gaishe min da Yaya.” Ya amsa da za taji insha Allahu………Gabadaya suka fita harabar gidan yaran suka nufi motarsu ta makaranta, shi kuma Salim din ya dan tsaya suna magana da Abba Abbas din kafin yaje ya shiga motar da sauri yaja motar ya fita daga gidan, Halisa ta kame a gidan gaba tana jira ya shigo kawai sai taga ya juya da nufin komawa cikin gidan, cike da mamaki take kallonsa, to me zai komar dashi kuma! ‘kwafa tayi ranta ya ‘baci babu shakka gurin yarinyar zaije, mtsssw! an girma kamar ba a girma ba a dinga abu irin na yara abinda ta fada kenan a fili tana jan tsaki!…….Ganinshi zai dawo cikin gidan yasa tayi saurin sakin labulan window din data la’be tana le’kensu, da sauri ta nufi toilet ta kulle kofa……Kai tsaye daya shigo d’akinsu Saddiqa ya nufa saboda yasan tana ciki…..Koda bai ganta a dakin ba, sai yayi tunanin tana toilet, ya karasa bakin toilet din yana k’wank’wasawa! da kiran sunanta, tana jinsa tayi masa shuru mugun haushinsa take ji shiyasa ma bata so ta kalli fuskarsa, Abbah Abbas haka ya ‘karaci buga kofar toilet din ya hakura, dan ya kai minti goma sha biyar yana tsaye yana aikin buga kofa da kiran sunanta bata saurareshi ba, ransa a ‘bace ya fita daga dakin…..Halisa kuwa cika tayi tai fam! ta dinga hura hanci takaici da bakin ciki kamar su kasheta, haka ita dashi sukayi tafiyar kowa ransa a ‘bace!