MADADI Page 21 to 30

*Littafin na kudi ne! Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kina so ki biya kudin littafin to ga yanda abin yake…..*
VIP #600
Normal #300
Accont:0542382124…Binta Umar gtbank..Idan katin waya zaki tura kiyi min magana ta whasap da wannan numbar
07084653262
*BINTA UMAR ABBALE*
BHRBN
*24*
Tana jin fitarsa daga dakin ta fito daga toilet din, zama tayi k’asan kafet ta had’a kai da gwiwa abin duniya duk ya isheta, ta kai minti ashirin a zaune tana sa’kawa da kwancewa kafin ta yanke shawarar mi’kewa ta dauki hijabinta tasa, hanyar fita ta nufa, Gidan Abbah Magaji za taje dan ba za tayi zaman kad’aici ba gabadaya gidan girma yayi mata ta dinga jin tsoro na shigarta…..Koda maigadi yaga zata fita baice mata komai ba dan shine ma ya bude mata karamar kofa ta fita yana yi mata adawo lafiya…..Tana kokarin shiga gidan Abbah Magaji Salim ya shigo da mota, tsayawa tayi har yayi parking ya le’ko da kansa yana d’aga mata hannu wai taje, dama sabida ita ya dawo gidan bayan ya ajiye yara a skull, cikin zumudi gami da farin cikin ganinsa ta nufi inda motar take, Ya bude mata ta shiga ta zauna kusa dashi tana fara’a da fadin “Wallahi naji dadin ganinka.”
Ya saki wani murmushi yana shafa sumarsa hade da yi mata shegen kallonsa yace.”Na shigo gidan tun dazu ina ta rarraba ido banga sanyin idaniya taba, shiyasa na kasa wucewa kasuwa kamar yanda mijinki ya bukata nace sai na dawo nayi tozali dake.” Tana murmushi tace”Ina dakin su Saddiqa ban san kazo gidan ba.”
Yace.”Ina fatan dai wani abu bai shiga tsakaninki da wannan dattijon ba.” Gabanta ne ya fadi ta kalleshi a sanyaye tace”Babu wani abu da ya shiga tsakaninmu ai nayi maka al’kawarin kai zan mallakawa kaina.” munafikin murmushi yayi yace.”Nagode Princess yanzu inaso ki d’an yi min abinda zai d’ebi min kewarki idan naje kasuwa.” Tace”Ban gane abinda kake nufi ba.” Kallon kasan ido yayi mata yace.”Haba baby sai nayi miki bayani dalla-dallah ashe har kin manta hirarmu ta jiya da irin amsar da kika bani, yanzu fa kika gama cewa jikin ki da komai naki nawa ne to inaso ki d’an fara gwada min soyayyar da kikeyi min a zahiri.” Cike da mamaki take kallonsa dan ta fahimci inda maganar sa ta dosa, shuru tayi ta kasa magana, kawai taji ya kama hannunta ya rike yana shafawa, Da sauri ta cire tana d’an hararasa tace”Idan sai na rungume ka ko nayi maka kiss sannan zaka gane kaunar da nake maka gaskiya ce, to kuwa sai dai kada ka yarda dani da son da nake maka koda nake cewa komai nawa naka ne ai ba ina nufin mu aikata haramci ba inaso bayan na rabu da wannan ‘kaddararran auran muyi aure da kai mu mori junanmu shine abinda nake nufi.” ‘Bata fuska yayi yace.”Dan kiyi kissing d’ina ko kin rungume ni ai ba wani abu bane amma tunda kince haka shikkenan.” Cikin rashin walwala ya ‘karasa maganar, Tace”Gaskiya kayi hakuri ba zan iya ba.” Cikin fusata yace.”Okey fita a motar nan na tafi inda zani dama duk karya ce ba wani sona kike ba da kina sona ba zaki tsaya jayayya dani ba.”
Ganin ya fusata! yasa jikinta yayi sanyi murya na rawa tace”Dan Allah kayi hakuri ka gane abinda nake nufi bana so ranka ya ‘baci.”! Yaja tsaki mai tsayi da fad’in “Bacin rai kuma wane iri ai raina ya gama ‘baci dake.”
Tace.”To kayi hakuri my love kada kayi fushi dani zuciyata zata shiga wani yanayi mutukar kana fushi da ita.”
Ta’be bakinsa yayi yace!.”Ai kin bani mamaki wallahi amma babu komai ina ganin zan hakura dake na fara duba ‘yan matan da suke sona sai na fitar da gwanata a cikinsu.” Jin ya fad’i haka sai hankalinta ya tashi murya na rawa tace”Dan Allah kada kayi min haka my Prince. ” Fuskarsa ya mi’ka mata da fadin” Okey oya kiss me idan kina sona.”
Ta dinga dawurwura kafin ta kai bakinta fuskarsa ta manna masa kissi da sauri ta cire bakinta tana jin nauyi da kunyar abinda tayi, murmushi yayi yana shafa gurin da tayi masa kiss din ya kalleta yana wani lumshe idonsa yace.”Allah ya nuna min ranar da zan had’a bakina da naki ina mutukar so naji ina tsotsar wannan lips din naki masu kyau da daukar hankali.” Yana kokarin kai hannusa kan le’bunanta yake maganar, ba ta bari ya kai hannunsa fuskarta ba ta bude motar da sauri ta fita daga ciki gabanta sai faduwa yake……Salim ya kalleta cike da mamaki! kamar xaiyi magana kuma sai yayi murmushi yana girgiza kansa ya kunna motar had’e da daga mata hannu da fadin “Zan kira ki a waya idan anjima akwai labarai masu dadi ina so ki tanadi amsar da zaki bani.”
Hannunta ta d’aga masa tana ya’ke tace”To shikkenan sai na jika.” Motar yaja ya bar gurin ita kuma da sauri ta nufi gidan Abba Magaji tana waiwayen bayanta kamar wata mara gaskiya…….Salim yana draving yana duba wayarsa yana sakin wani shegen murmushi ashe lokacin da take kiss d’insa ya saita camera……Hoton ya fita sosai kamar dama da son ranta hakan ya kasance fuskarsa da murmushi itama tata fuskarsa a sake duk wanda yaga hoton zai fahimci cewar masoya ne, ba tare da ‘bata lokaci ba ya d’ora hoton a fuskar wayarsa domin yana so Allah ya nunawa Kawun nasa hoton ya gani yasan dole ransa zai ‘baci ! idan ya tambaye shi shi kuma yana da amsar da zai bashi.
Aunty Maryam na zaune a palo ita kadai yaran duk sun tafi makaranta kawai taji sallamar Naja’atun, cike da mamaki take kallonta har ta ‘karaso inda take ta zauna kujerar kusa da ita tana gaisheta, Aunty Maryam ta amsa mata cike da kulawa tace”Naja’atu me ya fito dake ina fatan dai lafiya.”
Murya na rawa tace”Lafiya lau Anty gidan ne shuru su Saddiqa sun tafi skull Anty Halisa da Abba sun fita a tare ni kuma tsoron gidan nake.”
Anty Maryam tace”Ayya ai sai a hankali zaki saba ina fatan maigidan ya san zaki zo nan.”
Shuru tayi tana wasa da hannunta.
Anty Maryam tace”Be sani ba kenan naga kinyi shuru.”
Tace”Ai na dauka babu wani abu dan nazo tunda koda can muna zuwa da Yaya Halimatu.” Anty Maryam tace”Eh duk da haka dai yana da kyau ya san zaki zo itama marigayi ya kafin ta fita zuwa wani guri ai tana fad’a masa ko baki san yanzu haka mala’iku na tsine miki ba.”
A sanyaye tace”Na sani anty.” Tace”To amma kin sani kika take.”! Shuru tayi dan bata da abinda zata ce, Anty Maryam tace”Yanzu ki kira wayarsa ki fada masa gaki anan gidan nasan ba zaiyi fad’a ba.” zum’bura baki tayi gaskiya ba tajin zata iya kiran wayarsa dan ba ‘karamin haushinsa take ji ba.
Anty Maryam tace”Dake nake magana fa kodai har yanzu baki saduda kin kar’bi auran ba.” Fashewa tayi da kuka tace”Dan Allah anty ki kyaleni ni bazan kira wayarsa ba saboda bashi da adalci.” Cike da mamaki antyn take kallonta tace”To ikon Allah wane iri rashin adalci yayi miki kuma.”?
Hawaye ta goge tace”Anty duk da bana sonsa da auransa ya dace ya bawa Anty Halisa ta had’a min lefe baki ga banzayen kayan data siyo min ba kuma wallahi nasan tana sane tayi haka dan ta bani haushi! sannan kuma d’azu tazo tana zagina harda dukana a baki a maimakon ya tambayi ba’asi kawai sai ya dauki laifi ya d’ora mun.”
Anty Maryam tayi shuru tana nazarin maganar, tabbas komai akace Halisa ta aikata ba zata musa ba saboda dama tasan halinta, Halimatu tasha wahala a hannunta, dalili kenan da ya sanya basa shiri da juna da ita gasu dai ma’kota kuma mazajensu abokan juna ne amma kowa sabgarsa yake a tsakaninsu babu jituwa ko ta kwabo……Cikin rarrashi tace”Kiyi hakuri da Halisa nasan dai kin san hakurin da Marigayiya tayi da ita to kema inaso ki kwatanta ko kifi nat…..”Gaskiya anty ba zan iya ba wallahi.” Ta katse tun kafin ta ‘karasa maganar.