MADADI Page 21 to 30

Anty Maryam tace”Ke me yasa bakya tsawa a baki shawara ne? Halisa bata da kirki macace muguwa mai shegen kissar tsiya babbar macace ma ya ta iya da Halisa ballanta na ke! ki tsaya ki saurare ni da kyau! yanzu fushi ke ba naki bane! kamata yayi lokacin da yake fadan sai ki bashi hakuri ki fad’a masa yanda abun yake ba kiyi zuciya ba, kinga yanzu ita bukatarta ta biya ta had’aku fad’a sun ma fita unguwa tare dashi babu abinda ya dameta, to gobe ma haka zata sake miki ke kuma gaki mara wayo sai kiyi fushi ki tsaya girman kai ke ba zaki bada hakuri ba to ba haka ake zamantakewa ba.”
Tana kuka tace”Anty nayi yunkurin fad’a masa abinda ya faru ya’ki saurarata shiyasa nima na bashi guri.” Anty Maryam tace”Yanzu dai magana ta wuce kodan gaba kada ki sake aikata hakan idan wani abun ya shiga tsakaninki da Halisa yazo yana miki fada ki bari ya gama tukkuna sai ki fada masa abinda ya faru kada ki sake bar masa gurin bai dace ba.”
Cike da mamaki take kallonta tace”Anty sai na zauna kawai ya dinga yi mun fada alhalin ba laifina bane.” Anty Maryam tace”To meye yau da gobe da kansa zai gane gaskiya dan me yasa Halimatu ta ciri tuta a gurinsa nasan har ya mutu ba zai mance da ita ba saboda tayi masa ladabi da biyayya.”
Girgixa kanta ta shigayi gaskiya da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa Halimatu daban Naja’atu daban kowa da Halinsa. murya na rawa
Tace”Anty Maryam wallahi Allah shine d’aya har yanxu bana jin son mutumin nan a cikin zuciyata to ya za’ayi na iya zaman gidansa.” Anty Maryam tace”A hankali zaki ji sonsa na shiga zuciyarki ballantana Alhaji Abbas yayi duk macan da zata ganshi zata so ya zama mallakinta ke na fahimci tsufansa ne bakya so kuma ke kike abunki ‘yan mata nawa ne suke neman irinshi su aura ‘yan matan da suka fiki kyau da komai ma gasu nan suna yawo a gari amma ke kin samu kina wasa da damarki.”
Shuru tayi tana nazarin maganar anty maryam din itafa sam ba taga wani abun rubibi a gurin dattijo irin wannnan ba, kawai mace idan tana so ta more rayuwarta to ta auri dai-dai da ita amma auran tsoho a ganinta duk tauyewa rayuwa hakkine……Anty Maryam tace “Ki kirashi a waya ki fada masa bana so ya samu labarin kina zuwa gidan nan yayi miki fada kinga nima zaiga laifina da nake barin ki kina zama.
Wayar ta dauka ta nemo numbar tashi, dan dai kawai anty maryam din ta dage ne amma da wallahi ba zata fada masa ba……………Wayar tashi na hannu Salim dan haka da yaga kiran Naja’atun sai ya katse! ya’ki kai masa, Naja’atu ta sake kiran wayar a karo na biyu Salim ya’ki dagawa wayar tayi ta ringing har ta katse!! Ta kalli anty Maryam din tace” Ya’ki dagawa.” Anty Maryam tace”Watakila yana tare da mutane anjima sai ki sake kiransa.”
Dan ta’be bakinta tayi ta shiga whasap tana dubawa…..Anty Maryam mikewa tayi ta nufi kicin tana mamakin ‘kuruciyar yarinyar yanzu meye abin gudu a dangane da auran ta da Abokin mijin nata, babu shakka kuruciya ce ke damunta kuma idan Halisa ta gane akwai rashin jituwa a tsakaninsu to ita kuma tabbas ta samu hanyar da zata cigaba da shiga tsakaninsu.
Sai bayan sun fito daga sallahar azahur ne ya samu sararin ‘kar’bar wayoyinsa dake hannun Salim, ya zauna gurin zamanshi yana duba wayar, a lokacin yaga miss call din Naja’atun, da sauri ya shiga kiran wayar yana fatan Allah yasa lafiya dan baiyi tsammanin kiran wayarta ba, Lokacin da yake kiran wayar ita kuma tana bedroom din anti maryam tana sallah, Anti Maryam ta daga wayar a nutse tayi masa sallama…..Jin muryar anty maryam yasa shi mamaki yace.”Maryam ce ko.”? Tace”Eh wallahi nice ai muna tare da Naja’atu tun safe ta shigo tace kunje unguwa yara kuma sun tafi skull wai tana jin tsoron zaman gidan shine nace ta kira wayarka ta fada maka to kuma ta kira baka samu dagawa ba.”
Ajiyar zuciya ya sauke yana hamdala a zuciyarsa yace.”Wayar bata hannuna a lokacin okey babu damuwa bayan sallahr la’asar sai kisa ta ta koma gida tunda ina tsammanin ma yanzu Halisa ta dawo dan dama asibiti na ajiyeta na wuce kasuwa….amma tunda tana son zama dake idan anyi la’asar kisa ta ta koma gida.
Anty maryam tace”To insha Allah.” Sallama sukayi anty maryam ta juyo tana kallonta tace”Kinji ashe lokacin da kika kira wayar bata hannunsa, yace babu komai idan kinyi sallah la’asar sai ki koma gidan.”
zama tayi kusa da ita ba tare da tace komai ba, anty Maryam ta mike tare da fadin “Bari na kawo mana abinci muci akwai wasu abubuwa da zan baki idan kika mayar da hankali zasu taimake ki.” kicin ta nufa, Naja’atu ta bita da kallo tana tunanin wane abubuwa ne zasu taimaketa.
Halisa kuwa bayan ta gama ganin likita gidansu ta wuce kuma sai da ya gargade ta kan lallai data gama da asibiti ta koma gida amma saboda ita mai kunnan ‘kashi ce ta tafi gidansu……Sai da tayi sallahar la’asar sannan tayi sallama da mahaifiyarta
Anty maryam ta fito daga bedroom dinta hannunta rike da bakar leda guda biyu ta zauna kusa da Naja’atun tana bud’ewa ta kalleta a nutse tace” Wannan garin magani ne na mata mai kyau nice ma na had’a abina da kaina idan kin koma gida ki d’ebi cokali biyu kisa madara da ruwa kisha haka zaki dinga yi kullam, maganin zai taimaka miki…..Wannan kuma gumba ce itama kisa mata madara ki dama sai kisha, duk da cewar ke amarya ce amma hausawa nacewa idan kana da kyau ka ‘kara da wanka, idan kinga amfanin maganin nasan zaki sake nemansu a gurina.
‘Karba tayi ba dan za tayi amfani dasu ba, ta mike tana gyara hijab dinta, tace”Nagode anty sai anjima.” Anty maryam ta mike tana sake jaddada mata yanda za tayi amdani da maganin, har bakin gate ta rakata sannan ta koma cikin gidanta.
Tana fitowa daga gidan ta watsa maganin dake hannunta a kwata, babu abinda zai sa tayi shaye-shayen maganin mata alhalin ba son auran take ba……….
Halisa ta rigata shigowa gidan koda ta duba gidan taga ba tanan jiki na rawa ta nemi wayar maigidan tana fad’a masa wai Naja’atu bata gidan tun safe! Kai tsaye yace mata ya san bata gidan ta kwantar da hankalinta.” Jikinta ne kuma yayi sanyi jin abinda yace…….Naja’atu ta shigo ta sameta zaune a kujerar palo, kallon juna sukayi babu wanda yayi wa dan uwansa magana a cikinsu, Naja’atu kai tsaye dakinsu Saddiqa ta wuce cike da damuwa gami da jin tsanar masu gidan a cikin zuciyarta…………Halisa tsaki taja mai karfi cikin takaici da tsanar yarinyar ta nufi dakinta…haka suka zauna babu wacce tayi tunanin d’ora girkin dare a cikinsu…..Karfe shida shaura yaran gidan suka dawo daga skul, Abbah Abbas kuma sai daf da magariba ya dawo ya shigo ya tarar da palon babu kowa, yaran suna cikin dakinsu tare da Naja’atu ita kuwa Halisa saboda tasan sharrin data shirya tana d’akinta a kwance a kan bed wai ita mara lafiya….
*Littafin na kudi ne….!*
Koda zaki ganshi a groups to na sata ne, idan kina so ki biya kudin karatu to ga yanda abun yake.
VIP Group #600
Normal #300
Accont:0542382124….Binta Umar gtbank….Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan numbar.
07084653262
*BINTA UMAR ABBALE*
Mdd
*25*
Ganin har an fara kiran sallahr magariba ne yasa bai saurari kowa a gidan ba ya nufi dakinsa ya daura alwala ya nufi masjid din dake daura da gidansa, bai shigo gidan ba sai bayan sallahr isha’i, har yanzu babu kowa a palon, idanunsa ne ya sauka gurin cin abinci yaga kan daning din wayam! babu komai mamaki ya kama shi,girgiza kansa yayi ya nufi dakin Halisa sai kawai ya tarar da ita a kwance a bed ta rufe jikinta sai makyarkyata takeyi.