MADADI Page 21 to 30

A kanta ya tsaya yana kiran sunanta, ta dan bude ido tana kallonsa a sanyaye tace”Sannu da zuwa.” ya amsa yana dan nazarinta kafin yace.”Wai jikin ne har yanzu.”? Tace”Eh wallahi ai kana saukeni a asibiti zazzabi mai zafi ya rufe ni da kyar ma na dawo gida.” Yace.”Ina fatan likita ya dubaki sosai ina result din.”? Tace.”Bani da ciki kawai dai zazzabi da ciwon kai mai zafi ya kamani ya dai d’ora ni akan magani gasu can kan drowar dan ban fito daga asibitin ba sai da na tsaya na siya.” Yace.”Allah ya sawwa’ke sai ki mayar da hankali gurin shan maganin.” Tace.”Yanzu ma so nake nayi sallah naci abinci sai nasha maganin.” Yace.”Bana tsammanin akwai abinci dafaffe a gidan nan dole sai na sake fita yanzu.
A sanyaye tace “Kafin na kwanta sai da na had’a Naja’atu da Allah kan ta shiga kicin din ta d’ora abinci ko dan saboda yara wallahi kallo ban isheta ba, karshe ma tsaki taja ta barni a gurin…….Ranshi ya ‘baci sosai! babu shakka duk abinda akace ta aikata ba zaiyi musu ba, gidansa da abinci amma saboda tsabar rashin mutunci tana so ta tona masa asiri da girmansa da komai ya dinga yawon restaurant……Halisa na ganin ya juya zai fita da rai a ‘bace sai ta saki murmushi tana adduar Allah yasa yayiwa yarinyar hukunci mai tsauri!
Lokacin da ya shiga dakin yaran tana sallah, Yaransa suka shiga yi masa sannu da zuwa ya amsa babu cikakkiyar walwala a tare dashi, yace suje palo yanzu zai fito zasuje unguwa tare, da sauri suka fita suna murna.
Tsaye yayi bakin kofar dakin yana jiran ta idar, ita kuma tun kafin ta idar da sallahr gabanta ke faduwa, ta lura da masifa ya shigo dakin, a sanyaye tayi sallama ta kalleshi baki na rawa tace” Abbah sannu d….Hannu ya daga mata a fusace! yace.”Me ya hanaki girki a gidan nan.”?
Shuru tayi tana tunanin amsar da zata bashi, gaskiya ba zata ce ga abinda ya hanata girki ba kawai dai ta shagala tare dasu Saddiqa kuma ta dauka Halisa za tayi, Ganin tayi shuru yasa ya rufe ta da fad’a Yace.” Kin san Halisa na kwance babu lafiya me yasa ba zaki shiga kicin ke kiyi aiki ba, kuma ta fad’a min cewar tace kiyi abinci kin ja mata tsaki kin bar gurin, a gidana da abinci da komai amma saboda kina so ki tozartani ki sauke min tukunya kisa ni yawon gidan siyar da abinci….To wallahi duk ranar da haka ta sake faruwa sai na ‘bata miki rai tunda ke kin zama mara jin magana to zamu sa ‘kafar wando d’aya dake……..Kuka take ta ma kasa cewa komai, lallai a yaushe sukayi haka da Halisa? babu shakka maganar aunty maryam ta fito Halisa shaid’aniya ce, ita wallahi data san ba za tayi girkin ba da ita sai tayi, kuma da yake wannan maganar ai tunda tazo gidan itace take girki amma sabida yaje anyi masa famfo yazo yanayi mata fad’a yama ‘ki tsayawa ya saurari ta bakinta, yana fita daga dakin ta zame ta kwanta kan daddumar tana cigaba da tsiyayar da hawayen bakin ciki…….Wannan auran dashi gwara babu a gurinta ya zame mata ala’ka’kai da masifa.
Mussadiq kawai ya d’auka a cikin yaran nasa sukaje sukayi take away, ranshi duk a ‘bace! ya tsani da girmansa da komai a ganshi yana yawon gidan abinci a ganinsa hakan kamar zubewar mutumci ne…….Koda Mussadiq ya kai mata nata koro shi tayi tace ya fita da ledar bata so….Yaron ya fito da ledar take away din a hannunsa yana satar kallon Abban nasu dake zaune a kan kujera yana cin abinci…….Kusa dashi ya zauna jikinsa a sanyaye, Ya kalleshi a nutse yace.”Ya ka dawo da ledar abincin.” Murya na rawa yace.”Tace na fita dashi bata so.” Murmushi yayi yace.”Jeka ajiye mata a gabanta ka fito ka kyaleta….Yace.”Abbah tsoron masifar Yaya Naja’atu nake kada ta dokeni dan na lura tana cikin fushi mai tsanani.” Yace.”Idan ta doke ka zan rama maka.” Mussadiq yayi jim! yana nazarin maganar abban nasa, mikewa yayi ya sake nufar dakin a karo na biyu….Hankalinta na kan wayarta taga yaron ya dire mata ledar ya ruga a guje ya fita daga dakin….Tsaki taja ta ture ledar daga gabanta tayi rantsuwa sai dai ta kwana ba taci abinci ba dan ba zata ci abinda ya siyo ba……..Kwanciya tayi kan gadon Mussadiq ta bude whasap tana dubawa, voice note din Salim yafi ashirin wanda ya turo mata.
Da sauri ta bud’e tana saurara! murmushi ta dinga yi tana lumshe idonta gabadaya jikinta ya mutu domin zantukan da Salim yake mata na yau sun sha bambam dana jiya! gabadaya ma mantawa tayi da ‘bacin ran da take ciki shauki da sha’awa duk sun dame ta
Gani tayi ya turo mata hoto da sauri ta bude, gabanta ya yanke ya fadi ganin hotonsu a cikin mota lokacin da take masa kiss a fuska, da sauri ta tambaye shi ya akayi ya dauki hoton bata sani ba? rokonsa ta shigayi akan ya goge kada ya bari Abbah Abbas ya gani……Yace” Ba zai goge ba itama ya turo mata ne dan sabida yana so ta d’ora shi a fuskar wayarta saboda yana so Abbah Abbas din ya gani…Tace My prince idan Abbah yaga hoton nan dani da kai asirinmu zai tonu dan Allah kada ka bari yaga hoton nan ni zan fika shiga tashin hankali kuma duniya za tayi tur damu.
Yace.”My Princess kece kike tsoron ya gani! ni ko d’ar! ba nayi wai dan yaga hoton nan dan saboda na tanadi amsar da zan bashi koda zai kalubance ni, ke kuma munufar d’ora hoton nan a fuskar wayarki shine nasan idan ya gani jikinsa zaiyi sanyi zai gane cewar bafa kya sonsa zuciyarki tana tare dani, hakan zai sa yaji sha’awar auran ya fita daga ransa tunda na fahimci shi mutum ne mai kishi idan bukatarmu ta biya ta dalilin hakan kinga sai ya sawwake miki ki fito muyi auranmu.” Shuru tayi tana nazarin maganganunsa! Eh ta amince da wannan shawarar ta Salim zata sa hoton a fuskar wayarta har Allah yasa wanda akayi dominsa ya gani! tasan duk ranar da yaga hoton kamar yanda Salim din ya fada jikinsa zaiyi sanyi, sannan zai shiga cikin kunci da damuwa kasancewarsa mutum mai kishin kansa, to sai dai bata da amasar da zata bashi idan ya turketa da tambayar akan me yasa tana matsayin matarsa ta d’ora hotonta da wani akan wayarta…..Sai Tace”Salim ina jin tsoro yaga hotonmu ni da kai idan kai kana da amsar da zaka bashi ni bani da amsar da zan bashi.”
Salim yayi murmushi yace.”Idan yazo yana miki magana kice masa ai hoton ya dad’e tun kafin a daura muku aure dashi yake, idan yace to me yasa kika sa a wayarki sai kice kin kasa cirewa shiyasa kika barshi.
Mirmushi tayi tace”Wannan shawarar tayi wallahi aikuwa yanzu zan sa hoton a wayata Allah yasa ma idan ya gani yayi zuciya ya sakeni.” Salim yace.”Ameen ya Allah.” zan kashe data yanzu zamuje gurin kallon boll da abokina kada kiyi bacci da wuri idan na dawo inaso muyi hirar dare wacce tafi ta yanzu dadi.”
Murmushi tayi tace”To sai ka dawo idan kuma nayi bacci sai gobe mu had’u! Yace.”To shikkenan ki kula da kanki sosai kada ki barshi yayi gangancin ta’ba min wani ‘bangare daga jikin ki.” Tace”Kada ka damu my lov ni takace har abada.” Salim yayi murmushi jin dadi bukatarsa na biya ta kowane fanni yana sake siye zuciyar yarinyar da salon soyayyarsa. Yace.”Okey kiss me please. ” Dariya tasa tace ya za’ayi nayi maka kiss ta waya. Yace idan kinyi zanji a kunnena da gangar jikina.” Murmushi tayi tace”Kai dai ka fiye zolaya wallahi! sai anjima.” ta fada tare da kashe wayar tana murmushi, gaskiya Soyayyar da Salim keyi mata na burgeta sosai shiyasa kullum take kara kaunarsa, shi kuwa Abbah Abbas babu abinda ya iya sai fad’a komai fad’a da rashin uziri ga mutum! ai ba tajin zata ta’ba iya zama dashi tunda shi ya zama mijin tace komai Halisa ta fad’a masa dai-dai ne a gurinsa babu binkice zai hau kai ya zauna yazo yayi tayi mata tsawa!