MADADI Page 21 to 30

Tana kwance tana juye juye yunwa duk ta isheta amma saboda tsabar cutar kai ta’ki daukar abinci taci……Su Saddiqa suka shigo dakin da niyyar kwanciya dan goma na dare tayi Abbansu yace su kashe kallon da suke suje su kwanta.
mikewa zaune tayi tana kallonsu, nan ta hangi
Mussadiq sai ‘buya yake a bayan Saddiqa ta lura tsoronta yake ji shiyasa ya kasa tunkaro gadonsa da take zaune, murmushi tayi tace”Kai Mussadiq daina ‘buya ni babu abinda zanyi maka kaje ka saka kayan baccinka kazo mu kwanta yau a gadonka zan kwanta.” Murmushi yayi yace.” Nagode Yaya Naja’atu. Saddiqa ce ta bashi kayan baccinsa yasa yazo ya dauki pillow guda daya yace.”Yaya Naja’at ke kika kwanta kan gadon ni bari na kwanta kasan kafet.” Tausayi yaron ya bata tace”Anya Mussadiq ban so kaina ba kuwa kazo ka kwanta ai gurin zai ishemu.” Girgiza kansa yayi ya kwanta kasan kafet yana fadin”Na bar miki ki dinga kwanciya har sai sanda Abbah ya kawo miki naki.” Murmushi tayi tana girgiza kanta tace”Nagode yarona Ubangiji Allah yayi maka albarka.” yaron ya amsa da amin yana jin dadin yau ya farantawa Yaya Naja’atu rai…..Ta kalli Saddiqa dake kokarin kwanciya tace”Ki kashe fitilar dakin, Saddiqa tace”Yaya Naja’at wai da gaske kike anan zaki kwana yau.”?
Harararta tayi tace”Ke wannan wace irin magana ce? da a ina nake kwana to.”? Saddiqa kamar za tayi magana sai kuma taja bakinta tayi shuru ta kwanta tare da rufe jikinta da bargo tana tunanin wani abu…..Itama kwanciya ta gyara had’e da kashe wayarta gabad’aya! yau tayi alkawarin ba zata je dakinsa ba ballanta ya samu damar latsa mata jiki bayan ya gama yi mata fada……….To shima Abbah Abbas din a nashi bangaran bai wani damu ba dan ganin bata zo dakin nasa ba, sai kawai yayi shirin kwanciya bacci kamar yanda ya saba ya fito daga dakin nasa ya nufi na Halisa ya tarar da ita tana bacci dan bayan taci abincin da ya siyo musu kwanciya tayi bacci ya dauketa ko sallahr magariba da ishai ba tayi ba, tashin ta yayi ya tambaye ta shin tasha magani? tace tasha sai yayi mata sallama ya fita daga dakin, a maimakon ta tashi taje tayi alwala tunda da akwai sauran lokaci sai kawai ta koma ta kwanta da k’udirin gobe sai ta had’a sallolin gabadaya ta rama a lokaci daya, sai kace wacce ranta yake hannunta.
Dakin yaran ya nufa! ya tarar sun kashe fitila sai ya kunna wayarsa yana haskasu, Ganinta kwance kan gadon Mussadiq tana bacci shi yana ‘kasa sai ransa ya ‘baci! wannan ai abin kunya ne ta saukar da yaro daga makwancinsa ita ta kwanta(ina fatan baku manta da mutumin naku ba a gurin son ‘ya’ya) Kasa hakuri yayi kawai ya shiga tashinta! ta mike zaune da sauri tana kallonsa! fuskarta ya haska sosai yace”Sauko ki bashi gurinsa ya kwanta.”! Ba tayi musu ba ta sauka daga gadon ta tsaya a gefe….Ya sanya hannu ya cicci’bi Yaron ya kwantar dashi a gadon, ya rufeshi da bargo ya tsaya kansa yayi masa addua duk tana tsaye tana kallonsa ya nufi gadajen sauran ‘yayansa suma yayi musu addua ya nufi kofar fita daga dakin! ta dinga jin zuciyarta na wani iri tafarfasa itama ai haifarta akayi da zai dinga nuna mata ‘ya’yansa masu daraja ne taji kamar ta fitar masa daga gida dan a rayuwarta ta tsani wulakanci da tozarci……Daf da zai fita yaga ledar take away d’inta ya tsaya yana dubawa, alamu sun nuna yanda take haka take ba’a ta’ba komai na ciki ba, domin ya gazgata yasa ya sunkuya ya dauki ledar yana dubawa, aikuwa babu abinda taci a ciki.
Juyowa yayi yana sake haskata da hasken wayarsa yace.”Me yasa baki ci abinci ba.”? Kai tsaye tace”Bana jin yunwa.”? jimm! yayi yana nazarin maganarta yasan karya takeyi kawai tayi fushi ne saboda yayi mata fada, yace.”Sabida kinyi laifi anyi miki fada shine zakiyi wa kanki horo da yunwa.” shuru tayi ba tare da ta tanka masa ba……….Ganin ta’ki cewa komai yasa ya girgiza kanshi ya kama hanya ya fita daga dakin, yasan dai yunwa ba kanwar lasa bace lokacin da zata nemi abinci babu wanda zai sani, shi dai ya sauke nauyin dake kansa, Koda ya shiga dakin nasa bai sa key a kofar ba barinta yayi a bude wai ko zata shigo ta kwanta……gajiya yayi da jiran shigowarta dakin bacci mai nauyi ya dauke shi…
*Littafin na kudi ne….!*
Koda zaki ganshi a group’s to na sata ne idan kina so ki biya kudin karatu to ga yanda abin yake.
VIP Gruop #600
Normal gruop#300
Accont: 0542382124….Binta Umar gtbabk idan katin waya zaki turo kiyi min magana ta whasap da wannan numbar
07084653262
*BINTA UMAR ABBALE*
BHRBN
*26*
Da safe yaran suka tashi cikin walwala da farin ciki, Naja’atu kuwa kwana tayi cikin ‘kunci da takurewar zuciya kafin ma tayi bacci sai da taci kukanta ta koshi sannan………. dalilin kukan da tayi yasa ta tashi da jan ido Mussadiq yaron da ya damu da ita sosai shine ya dameta da tambayar mai ya samu idonta yayi ja, tace masa ciwo yake mata, yaron ya yarda da maganar data fad’a ita kuwa Saddiqa jinta kawai tayi da kunne ta riga ta gane kuka ne ya mayar mata da ido kamar jan gauta………..Tana cikin taimakawa Mussadiq gurin sanya takalminsa ya shigo dakin, yana sanye da jallabiya ba’ka mai yankakken hannu, as’usul hannusa da k’aramin carbi yana ja…Yaran suka shiga rige-rigen gaishe shi ya dinga amsawa cikin sakin fuska, da kulawa. Kanta a kasa ba tare data d’ago ba tace”Ina kwana.” Ya amsa lokacin da yake kokarin fita daga dakin, yaran ne suka biyo bayansa kai tsaye suka nufi dannig domin karyawa, sai dai me? babu komai a kan dannig din….Abin ya bashi mamaki sosai ya kalli Saddiqa yace.”Baku had’a break bane.”? Tace”Ai bamu tashi da wuri ba shiyasa.” shuru yayi takaici kamar yasa zuciyarsa ta buga, yace.”Yi maza kije ki dafa muku indomee kafin Salim din yazo.” Da sauri ta nufi kicin din…Dakin Halisa ya nufa, ya tarar da ita tana sallah! sai bayan da ta idar sannan yace.”Ashe bayan na fita komawa kikayi kika kwanta wai me yasa kike wasa da sallah ne.”? Ya kalli agogon hannunsa yana kallonta babu faraa a fuskarsa yace” dubi lokaci bakwai da kusan rabi kina kwance baki yi sallah ba bayan kuma kin san da cewar yara zasuje makaranta.”
Cikin ‘kosawa da maganarsa tace”bayan nasan yara zasuje makaranta to me zanyi musu ? Saddiqa ta iya komai idan ma ita Naja’atun ba za tayi ba ai Saddiqar sai ta dafa musu abinda zasu ci da wanda zasu tafi dashi tunda kasan ni ba lafiya ce dani ba.” Yace.”Duk da haka me zai hana ki ‘kokarta ki shiga kicin d’in kiyi wani abun.” Shuru tayi masa domin itafa ba zata dinga katsewa kanta bacci ba ta tashi tana wani hidimar yara….Yace.”Tunda dake da Naja’atun duk kun zama ‘yan kanku zan sa a kawo min mai aiki wacce zata dinga kulawa da yarana, ke kina ganin kyashin kulawa dasu tunda ba ke kika haifesu ba ita kuma tana fama da kuruciya da rashin hankali okey ku cigaba da abinda kuke zan dauki mataki.” Yana kare maganarsa ya fita daga dakin.
Kicin din ya nufa Allah sarki sai ya shiga taimawa Saddiqar cikin tausayinsa tace”Abba kaje ka huta zan iya komai.” Girgiza mata kai kurrum yayi ya cigaba da feraye dankali yana sawa a ruwa…..Hawaye ta goge tace”Dan Allah Abbah kaje ka huta wallahi zan iya ka bari.” Tafada tana kar’bar wukar hannunsa,