MADADI 1-END

MADADI Page 21 to 30

Cikin kokarin son ta san abinda sukeyi din tace”Ni ban san me sukeyi ba kawai dai sun shiga daki tun safe shine nima hankalina ya tashi…..Yaya Ramlatu tace”To sinna suke rayawa dan haka sai ki kwantar da hankalin ki zasu fito idan sun gama……Naja’at za tayi magana sai ga Halisa ta bude kofar dakin ta fito a firgice sai wata iriyar tafiya take tana cizar le’bunanta!!! a firgice! Yaya Ramlatu ta mi’ke ta iske inda take tana tambayarta menene! Halisa hawaye suka wanke mata fuska! ta rike hannun Yaya Ramlatun tace”Muje d’aki Yaya Al’amarin yafi karfina.” Cikin tashin hankali Yaya Ramlatu ta ri’ke hannunta suka nufi dakinta Halisa sai cire ‘kafa take da kyar tana tafiya a hankali a hankali Yaya Ramlatu sai rirrike take…….Naja’atu taji dadi ganin Halisan cikin halin ciwo a fili tace “Allah shi ‘kara alhakina ne ya kama ki, murmushi tayi ta bar gurin.

 Halisa da kyar ta zauna gefen bed tana rintse idonta sai hawaye ya shiga zubo mata ita kadai tasan radadi da zugin da gabanta ke mata.

Yaya Ramlatu tace”Wai me ya faru ne ni kin sani cikin fargaba da tashin hankali….Murya na rawa Halisa tace”Ya Ramlatu dan Allah taimaka ki jona min ruwan xafi na shiga gabana kamar an tsaga da reza haka nake jinsa.”

Yaya Ramlatu ta ri’ke baki tana kallonta tace”Kamar yaya na jona miki ruwan zafi sai kace wata maijego ko amaryar da aka karbi budurcinta zakiyi ruwan zafi.” Halisa tace”Yaya Ramlatu duk wannan maganar bata taso ba tunda kikaji na fadi haka to akwai matsala.”

Ya Ramlatu tace” To Allah ya kyauta! kettle ta dauka ta shiga toilet ta jona ruwan zafi a ciki ta fito ta tsaya kan Halisan tana tamayar ta, Halisa tace”Maganin nan ne na gurin Yar Sa’adu ashe haka yake da karfi sau biyu fa kacal nasa amma tunda ya fara abu daya bai saurara ba ya kawo yafi sau biyar.” Yaya Ramlatu ta rike bakinta tana girgiza kanta tace”Aifa lallai dole kiji jiki ta’b! to ai sai ki ajiye maganin idan ya kama da cutarwa a ciki ko kuma ki dinga sa kad’an ina dalili.” Halisa ta sha’ki hanci tace”Ai gabad’aya ma maganin zubar dashi zanyi dan ba zan zauna na kashe kaina a banza ba.” Yaya Ramlatu tace”Haba ke kuwa abun zunzurutun kudi zaki zubar.” A dan hasale Halisa tace”To ko na baki kina so ne.”? Da sauri tace”Oo rabani da wannan shirme ni bashi ne a gabana ba.( Halisa ya kamata ki nutsu ki gane Yaya Ramlatu na ingizaki kina siyan abinda zai cutar dake da kudinki me yasa ita bata siya tayi amfani dashi sai ke mara hankali ki ta siyan abu baki san yanda akayi aka had’ashi ba ki dinga cusawa a matuncinki dan cutar kai) ….Tace”To kawai tunda nace zubarwa zanyi ki kyaleni ba zan kara sawa a gabana ba ballanta ‘kaninki ya kashe ni.” Yaya Ramlatu ganin Halisa ta fusata! sai ta sassauta murya tace”Allah ya kyauta to tashi kije kiyi ruwan d’umin Allah ya kiyaye gaba.”

Halisa ta mike a hankali ta nufi toilet.

Naja’atu kuwa wanka tayi a gurguje ta shirya ta fito palo ta zauna so take taga da wane ido Abba Abbas din zai kalleta dan tasan a cikin hakkinta ya shiga daki ya share awa kusan hudu yana abinda bai dace ba……Aikuwa ganinsa tayi ya fito shar dashi kamar wani matashin saurayi, Yana sanye da farin yadin piltex cotton anyi mishi aiki da bakin zare wuya da hannu! sai yayi amfani da hula mai duhu! kafafunsa na sanye da takalmi mai gidan yatsa ba’ki yayi kyau sosai yana ta kamshin turarensa…….Lafiyayyar harara ta watsa masa wacce ta dauki hankalinsa sosai ya tsira mata ido yana mamakinta, Gani yayi ta murguda bakinta ta dauke kanta tana motsa bakinta.

Sai ya karaso inda take tsaye a nutse ya tsaya a kanta yace.”Ke lafiyarki kuwa.”? Ta kalleshi tana sake murguda baki….Sai abin ya bashi dariya yace”Da alama kina bukatar ganin likita kwa’kwalwa.” Fashewa tayi da kuka tace”Abbah a gaskiya abinda kake baya dacewa wai dama haka addini yace kuyi.” ? tafada tana me tsira masa idonta, dama tayi al’kawarin sai ta d’aga masa hankali kamar yanda ya d’aga mata…….Kallonta ya shiga yi yana mamakin maganarta, ta goge hawayen fuskarta ta cigaba da cewa” Kana shiga daki ka kulle kofa a cikin kwanakin aurena da musulunci ya bani da wane ido kake tunanin zan kalleka kaifa ba yaro bane sai ka dinga shiga hakkina.”

Ya saki baki kawai yana kallonta sosai maganganunta suka bashi mamaki!! Mikewa tsaye tayi da wayarta a hannunta tace”Dan Allah idan kasan ba za kayi adalci a tsakaninmu ba to ka sawwake min tunda dama baka d’ora min idda ba sai naje na auri wanda zai kula dani…..” Kasa cewa komai yayi kawai ya zuba mata ido yana kallonta. ita kuma ganin jikinsa yayi sanyi sai taji dadi ta ra’ba ta jikinsa zata bar gurin, turata yayi ta koma kan kujerar ta zauna! wayar hannunta ta fad’i kusa da kafafunsa, hankalinsa ne ya dauke gurin hoton dake fuskar wayar tata……Da sauri ya sunkuya ya dauka yana dubawa! ganin abinda ke wayar yasa hankalinsa yayi masifar tashi, ya nuna mata fuskar wayar da fad’in “Waye wannan.”? duk da yasan waye kawai tsintar kansa yayi da tambayarta, tace” Salim ne.”? Wani bahagon mari ya kifa mata yana tsuma! yace.”Yaushe kukayi wannan hoton.? ashe munafurtata kuke.”? tana kuka tace”Wannan hoton ya dad’e tun kafin muyi aure da kai yake.” Cikin tsawa! yace.”Karya kike wannan hoton bai jima ba ashe baki da mutunci naja’atu kina so ki zubar min da mutuncina ko.? Tace”Na fada maka wallahi hoton ya dade tunda baka yarda ba shikkenan.” A fusace ya doka wayar da bango (garu) ta fad’i kasa duk ta farfashe! tsuganawa yayi ya tsince sim card din ya karyasu ya watsar a gurin, ya kalleta da jan ido yace.” Tunda kin zama shaid’aniya to zanyi maganinki kin janyo duk wani tausayinki da nake ji na daina sai na mai dake cikakkiyar mace mai lasisi a gidan auranta zaki zauna da tsoho har karshen rayuwarki……

 Dakinsa ya nufa cikin tsananin bacin rai!! ita kuma ta had’a kai da gwiwa tana kuka sam bata dauka zai fusata hakaba gashinan garin neman gira ta rasa ido ya fasa mata waya ya karya mata sim! babban tashin hankalinta a yanzu shine ta wace hanya zata dinga saduwa da masoyinta…..Tabbas da tasan zai dauki matakin lalata mata wayarta daba ta nuna masa hoton ba……Salim ya dade da shigowa palon amma bata sani ba sai da ya kira sunanta sannan a furgice ta dago kanta tana kallonsa, ta bude baki kenan za tayi masa magana Abbah Abbas din ya fito daga dakinsa hannusa da rike da wayoyinsa, ganin Salim a tsaye a kanta ya sake tunzura masa zuciya cikin gawurtacciyae tsawa mai had’e da zazzafan kishi yace.”Kai mai kake anan.”? Gabadayansu suka firgita suka juyo suna kallonsa, Salim yace.”Kawu nazo daukar ka kamar yanda kace karfe goma sha biyu na dawo na kai kasuwa to ina shigowa sai na tarar da ita tana kuka shine nake tambayarta ko wani abune ya faru.”

Wani banzar kallo ya watsa masa kafin yace.”Malam bani key din mota ka tafi naka guri bana bukatar na sake ganinka cikin al’amurana.”

Salim yace.”Subahanallahi Kawu mai ya faru kuma idan laifi nayi maka ka gafarce ni kasan dan adam ajizi ne.”! Yace.”Ban nemi wata magana da kai ba key na mota nace ka bani ka fita ka bani guri.” Salim ya’ki bashi key din ya tsaya yana rokansa gafara! A fusace! yace.”Zan dauki mataki mai tsauri a kanka idan baka bani key ka fice min daga gida ba.” Salim ya bude bakinsa zaiyi magana Yaya Ramlatu ta fito daga dakin Halisa hankali a tashe ta ‘karaso gurin tace” Me yake faruwa ina jin anata hayaniya.” Salim ya karasa kusa da mahaifiyarsa cikin rawar baki ya shiga fada mata abinda ke faruwa. A sanyaye ta kalli dan uwan nata dake tsaye yana huci!! tace”Duk da dai ban san abinda ya had’aku ba ina rokon ka yafe masa kasan dan adam ajizi ne ba wai na hakana kayi masa hukunci ba salim kai kake da iko dashi cikin ko wane hali.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button