MADADI Page 21 to 30

Ajiyar zuciya ya sauke yace.”Bana bukatar ke kisan me yayi shima kuma bana bukatar yaji abinda yayi daga bakina tunda nasan yasan abinda ya aikata min na ha’ince wannan dalilin ya sanya ni yunkurin cireshi daga cikin sabgogina saboda ya kasance maha’inci.”
Yaya Ramlatu ta fashe da kuka tana kallonsa tace”Wai shin me yayi zafi ne? dan Allah ka fada min abinda yayi maka kake jifansa da wannan mugayen maganar………Naja’atu ya kalla cikin takaici da bacin rai yace.”Yaya Ramlatu tunda nace abar maganar to a barta shine yafi amfani.”
Tace”Aikuwa ba za’a barta ba dan naga ka kalli waccar munafukar yarinyar watakila duk sharrinta ne.” Shuru yayi mata, sai kawai ta shiga zagin Naja’atun tana fad’in duk iya asiri da surkulle na ubanta to bai isa ya raba tsakanin hanta da jini ba.”
Naja’atu abu biyu ya had’e mata a duniya ta tsani taji ana zagin iyayenta ji tayi kamar ta rama sai dai tayi shiru ta sunkuyar da kanta tana ta kuka gami da yanke shawarar da zata fisheta…..Abbah Abbas ganin al’amarin na Yaya Ramlatu na nema ya wuce gona da iri sai ya dakatar da ita yace.”In dai akan ya kori Salim ne take wannan abu to ya janye maganarsa dan haka magana ta mutu.” Fadin hakan yasa ta sassauta ta nemi guri ta zauna tana haki! ita kuwa Naja’atu mikewa tayi tana kuka ta shige dakinsu Mussadiq…..Yaya Ramlatu ta bita da kallon banza da fadin “Aikin banza gayyar tsiya masu raba zumun….Daga mata hannu yayi yace.”Dan Allah ki daina wannan maganar bata dace ba ni sukayi wa laifi ita da Salim din kuma na yafe musu.” Salim baiso ya fadi hakaba yaso ayi ta tak’are a gurun, amma dai duk da haka yaji dadi da yasa masa ‘bacin rai a zuciyarsa……Sai ya karyar da kai cikin sassauta mirya yace”Kawu kayi hakuri duk da baka fada min laifina ba amma na dauka ina neman afuwarka kuma insha Allahu ba zan sake ba.”
Ba tare da ya tanka masa ba ya kama hanyar fita, sai yayi saurin rufa masa baya yana d’agawa mahaifiyar tasa hannu.
*Littafin na kudi ne….!*
Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kina so ki biya kudin karatu ga yanda abin yake.
VIP Gruop#600
normal gruop#300
Account: 0542382124… Binta Umar gtbank….idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan numbarĀ
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
Mdd
*27*
Salim da sauri ya ‘karaso bakin motar yasa hannu ya bude masa motar hade da matsawa gefe guda yana wani sunkuyar da kansa tamkar wani mutumin kirki, Abba Abbas ya shiga motar ya zauna har yanzu fuskarsa a murtuke take, da sauri salim ya rufe motar ya zagaya ya bude mazauninsa ya zauna sannan ya kunna motar suka fita daga gidan……Motar shuru tayi kowa na sa’ke-sa’ke a cikin zuciyarsa, Abbah Abbas kamar zai daure maganar azuciyarsa sai ya kasa gyaran murya yayi babu wasa cikin maganarsa yace.”Kai!! wannan hoton da nagani cikin wayar Naja’atu yaushe kukayi dauke shi.” Salim yaji gabansa ya fad’i! cikin dakiya da kokarin kare kansa yace.”Kawu wane hoto ne kake magana akansa.” ? A dan fusace! yace.”Kai bana son rainin hankali malam ya ina tambayarka kana tambayata wato matata kake bibiya ko.”? Salim yace.”Subahanallahi Kawu wannan wace irin magana ce kakeyi ina ni ina matarka Kawu ai wutsiyar ra’kumi tayi nesa da ‘kasa ni wallahi yanzu kunyarka ma nake ji idan na tuna wai na ta’ba soyayya da Naja’atu……Abbah ya daga masa hannu da fad’in “Ba cewa nayi kayi min wasu zancan banza ba ina tambayarka hoton da nagani a cikin wayar matata yaushe kukayi shi.”?
Cikin rawan murya Salim yace.” Wallahi Kawu ban fahimci inda maganarka ta dosa ba kayi min bayani yanda zan fahimta saboda nasan ni a yanzu tsakanina da Naja’atu gaisuwar mutunci ce tunda ta zama matarka ai dole na girmamata to kawu ina zan ganta ma ballanta na muyi hoto tare.
Abbah Abbas yaji zuciyarsa ta danyi sanyi saboda jin maganar da Salim din yayi, Gyara zamansa yayi yace.”Wani banzan hoto nagani kai da ita a cewar ta tun kafin aure ya shiga tsakanina da ita yake kuma saboda shashanci da rashin sanin hakkin aure ta dauki hoton ta dora a fuskar wayarta shiyasa hankalina ya tashi na d’ora zargina gabadaya a kanku kai da ita.”
Salim ya dinga girgiza kansa cikin sanyin murya yace.”Hakika munyi hotona masu yawa da naja’atu a lokacin da muna soyayya to amma daga lokacin dana tabbatar da cewar tafi karfina sai duk nagoge hotonanta dake cikin wayata Kawu ka yarda dani wallahi bazan ta’ba cutar da kai ba.”
Ajiyar zuciya ya sauke! yanzy yaji sanyi cikin ransa domin kalaman Salim din sunsa ya gazgata maganarsa kan cewar tsakani da Allah yake zaune dashi kuma a tsakaninsu babu cuta babu cutarwa…………..Yaya Ramlatu kuwa tana ganin maigidan ya fita sai ta mike tabi Naja’atu dakin ta dinga zazzaga mata masifa tana zagin iyayenta da fad’in “Insha Allahu sai Allah ya tona musu asiri kuma duk asirin da Baba malam yakewa zuriarsu da yardar Allah kansu zai koma.
Naja’atu kasa hakura tayi tace” Yaya Ramlatu mu bama asiri muna zama da mutum da zuciya daya duk wanda kikaji yana maganar anyi masa asiri to bai yarda da kansa ba Amma ni da iyayena da Allah muka dogara kuma shine zai shige mana gaba……..Yaya Ramlatu tace”Eh lallai wuyanki ya isa yanka yarinyar nan to dan ubanki Malam Sani!!! Halimatu ma bata iya karawa dani ba ballantana ke karan kad’a miya da har nake magana kina mayar min da martani to ni sai na sabauta miki rayuwa wallahi……Tana kuka tace”Dan Allah kiyi hakuri na fada miki abinda yake zuciyata ne kuma ni ba rashin kunya nayi miki ba.” Yaya Ramlatu ta gaura mata mari a zafafe tace”Dan uwarki kin tsaya gaba da gaba dani kina fada min maganar da ranki yake so amma kice ba rashin kunya kike min ba to Ubanki kike min kome.”?
Halisa ta turo kofar dakin ta shiga tana dan ya mutsa fuska tace”Wai me faruwa ne? tun dazu nake jin hayaniya…..Yaya Ramlatu ta shiga wassafa mata abinda ya faru.
Tsaki taja ta kalli Naja’atun tace”Yaya Ramlatu sharrin yarinyar nan yafi kala d’ari komai akace tayi ba zanyi mamaki ba nima nema suke su rabani da ‘yata mufida, tunda tazo gidan nan Mufida ta daina zuwa inda nake sai na kwana na yini bansa ta a idona ba tana nane dasu sun lashe mata kurwa.”
Yaya Ramlatu tace”Ai sai kiyi gaggawar dauke yarinyar ki dan kada su koya mata mugun hali na gado.” Naja’atu na tsaye tana jinsu suna ta zaginta iyayenta da kakaninta, sai da suka gaji dan kansu suka fita daga dakin.
Cikin kuka da tashin hankali ta nemi hijabinta tasa ta kama hanya ta fita daga gidan tana kuka kamar ranta zai fita……Aunty Maryam taga ta fad’o mata gida tana kuka, a gigice ta mike ta tare ta tana tambayarta abinda ke faruwa, Naja’atu rungumeta tayi tana kuka tace”Aunty Maryam kun kassara min rayuwata kun cutar dani ba zan iya wannan rayuwar ba, gidan Abbah Abbas yafi karfina dan haka wallahi tallahi zan yankewa kaina hukunci da ba zaiyi wa kowa dad’i ba.” Aunty Maryam tace”Innalilihi wa’ina ilahi raji’un! Naja’atu nutse ki fada min abinda ke faruwa ashe duk kin manta shawarwarin da na baki jiya.”
Tace”Aunty Maryam wane shawarwari zanyi amfani dasu kullum a gidan a cikin laifi nake Halisa tayi ta yi min sharri a gurinsa sai ya dauki maganarta ba zaiyi binkice ba yazo yay tayi min fad’a! Yanzu haka Yaya Ramlatu na gidan kafin na fito ta zage ni ta mare ni yafi sau uku me nayi mata zata dinga dukana nima fa ba’ason raina akayi auran nan ba da zasu dinga takurawa rayuwata.”