MADADI 1-END

MADADI Page 21 to 30

Aunty Maryam jikinta yayi sanyi tace”Gaskiya Yaya Ramlatu abunda takeyi bata kyautawa, kawai da girmanta da komai ta dinga zuwa gidan k’aninta tana lalata masa zamantakewar gida, wallahi haka Halimatu tasha wahalarsu, kiyi hakuri ki koma dakinki idan Abba Magaji ya dawo zan fad’a masa abinda ke faruwa gaskiya dole ya samu abokinsa yayi masa magana.”

Tace”Anty Maryam babu inda zan koma gidan Baba malam ma zan tafi.”? Anty Maryam ta rufe baki cikin tsoro tace”Dan Allah daina wannan maganar kina so ki janyo min fada gurin mijina kenan idan kika tafi gidan baba malam zasu d’ora laifin akaina ki daiyi hakuri insha Allah komai zai daidaita…..Naja’atu shuru kawai tayi tana sauraran maganar da Anty maryam din keyi har abada bata jin zata iya zaman aure a gidan Abbah Abbas dole ta nemawa kanta mafita dan tana ji tana gani ba zata ‘kare rayuwarta cikin kunci da masifar kishiya ba.

 Aunty Maryam ta dinga rarrashinta gami da bata shawarwari masu amfani wanda idan da zata daukesu to ba karamin taimakonta zasuyi ba, amma ina! hausawa na cewa wanda yayi nisa baya jin kira dan gabadaya Naja’atu a cikin zuciyarta bata da niyyar zaman aure a gidan Abba Abbas burinta kawai ta samu damar da zata sanya ta kufce daga hannunsa……..Sai da tayi sallahar la’asar a gidan Abba Magajin sannan Aunty maryam ta lalla’bata kan ta tafi gida insha Allahu zata sanar da Abba Magaji duk abunda ke faruwa a gidan abokin nasa, Naja’atu kamar gaske tayi mata sallama ta fito daga gidan, kai tsaye sai ta mi’ki titi ta dingi tafiyar ‘kafa kofar na’isa ta nufa gidan Baba Malam dan tayi rantsuwar ba zata koma gidan ba, ta riga ta fito kenan…………Baba malam na zaune kan dadduma a dakalin gidansa ya hangota ta karyo kwanar gidan, idonsa yasa mata yana so ya tantance itace ko ba itace ba, sai da ta kusa zuwa kusa dashi sannan ya gazgata, ganin da yayi mata a firgice yasa hankalinsa ya tashi jikinsa yayi sanyi sosai! ita kuma tana zuwa sai ta zube gabansa ta bude bakinta za tayi magana kuka yaci karfinta, cikin taushin murya yace.”Tashi ki shiga ciki komai yayi tsanani maganinsa Allah.” Ta mike kamar mara lafiya ta nufi cikin gidan…..Baba Talatu na bakin rariya tana d’auraye kwanuka taji sallamarta da sauri ta juyo tana kallonta tare da amsa sallamar da tayi…..Itama ganin yanda ta shigo firgai firgai ya tashi hankalinta, sai ta mike daga inda take ta karaso kan tabarmar da Naja’atun ke zaune tana tsiyayar da hawaye…..Zama tayi kusa da ita tare da fadin “Naja’atu daga ina kike wannan zuwan naki bana alkairi bane.”! Kukanta ne ya sake tsananta ta rike hannun mahaifiyar tata tace” Baba daga gidan Abbah Abbas nake tunda kuka kaini kuka ajiye ake azabtar dani wahalar yau daban ta gobe daban, Yaya Ramlatu tazo har gidan tayi mun duka ta zageni ta tsine muku ta kira ni mayya babu irin cin mutunci da zagin da ba tayi mun ba, wannan dalilin ya sanya ni bar musu gidan dan bana so na zauna a gidan ta tunzura zuciyata na rama zagin iyayena da take ace nayi mata rashin kunya.

Baba Talatu tace”Haba Naja’atu har yaushe aka kai ki dakin mijin naki da zaki zo da wannan maganar wai shin me yasa ke baki da hakuri ne? shin ba zakiyi koyi da ‘yar uwarki ba, Halimatu har ta kwanta dama bata ta’ba zuwa gidan nan ta kawo ‘karar mijinta da ‘yan uwansa ba tana hakuri cikin ko wane hali kuma tana biyayyar aure amma ke kwana uku kacal kinzo gida shin ko dai kina so ki zubar mana da kima da mutunci ne a unguwa.

Girgiza kanta ta shigayi tace”Baba akwai cutuwa a cikin wannan auran da kuka ‘kulla domun kuwa ta kowane ‘bangare babu sassauci ni ake zalinta kwana uku kacal da nayi a gidan na fuskanci ba gidan zama bane Halisa sai abinda tace akeyi kullum cikin yi min sharri take a gurin Abbah sai yazo yayi tai min fada bani da laifi….Baba kuma kin san kowa da halinsa a gaskiya ni ba zauna wani ya dinga zagin iyayena nayi shuru ba dan iyaye ba sufi iyaye ba.”

Baba Talatu tayi shuru jikinta duk yayi sanyi da maganganun Naja’atun babu shakka duk d’a nagari ba zai so a dinga zagin iyayensa a gabansa ba…….Baba malam ne ya shigo gidan ya zauna gurin zamansa yana kallonsu sunyi jugum! ya kalli Naja’atu da fad’in “Auta kada kice min yaji kikayi kika zo gida.” Baba Talatu tace”Aikuwa dai abinda tayi kenan…..Cikin damuwa yace.”To akan me? Ashe ke ba zaki kyautata hakurin da ‘yar uwarki tayi a dakin mijinta ba.”! Baba Talatu tace”To abun ne gaskiya da akwai matsala kuma kasan kowa da halinsa ba lallai ne Naja’atu ta kauda kanta daga kan abinda Ramlatu zata zo tayi mata ba, idan baka manta ba kasan haka Halimatu ta sha fama da Ramlatu wallahi ni na rasa wace irin macace wacce kullum girma take amma tana sake lalacewa da rashin hankali.”

Baba Malam yace.”Duk wani abu da Ramlatu zata zo tayi miki a gidan mijinki idan bada mijinki kuka samu sa’bani ba to komai mai sauki ne! ban lamunce ki dinga dauko kafarki kina zuwa gida akan abinda bai kai ya kawo ba, shin dan Ramlatu ta zage ni ko ta zagi mahaifiyarki sai me? mutukar baki bude baki kin rama ba to kanta take zagi! dan haka daga yau sai yau kada Ramlatu ta sake zuwa gidan mijinki wani sa’bani ya shiga tsakaninki da ita ki d’auko ‘kafa ki zo gida, yin hakan zai janyo miki ‘bacin raina.”’!! Tayi shuru hawaye nata zirara a fuskarta dama tasan da wuya baba malam ya kyaleta ta zauna masa a gida gashi ‘kiri-‘kiri yana nema ma ya d’ora laifin a kanta…….Yace.”Tun kafin gari yayi duhu ki tashi ki koma dakin ‘ki farin cikina a duniya shine inga kin zauna lafiya tare da mijinki saboda haka kije ki cigaba da hakuri insha Allahu zaki ci riba anan gaba.

Mi’kewa tayi tana ‘kokarin zura takalminta takaicin duniya ya isheta wai iyayenta da suka haifeta sun kasa gane abinda take ji a cikin zuciyarta da anyi magana sai suce tayi hakuri idan hakuri na kisa a ganinta to da tuni ya kasheta……Koda ta fita daga gidan kai tsaye gidan Alhaji ta nufa dan yanda Yaya Ramlatu ta kuntata mata to itama sai ta janyo mata fad’an iyayenta…….Hajiya na zaune a palo tana jan carbi Naja’atun ta shiga da sallama kasa kasa a bakinta

Kallo guda Hajiya tayi mata ta fahimci akwai damuwa, Naja’atu zama tayi kujerar da take kallon hajiyan tana share hawaye…Hajiya ta ajiye carbin hannunta a nutse ta kalleta tace”Naja’atu tunda na ganki a furgice nasan babu lafiya ki fad’a min abinda ke faruwa.”? wasu sababbin hawaye ne suka zubo mata, murya na rawa ta shiga fad’a mata abinda ke faruwa da irin sharrin da halisan ke mata da kuma yanda Abbah Abbas din ke dauka yazo yayi mata fada ba tare da yabi ba’asi ba, sannan ta fada mata zagi da dukan da Ramlatu tazo har gida tayi mata.

 Hajiya shuru tayi takaici kamar ya fasa mata zuciyarta, ita kam ta rasa yaushe Ramlatu za tayi hankali wallahi da girmanta da komai ta dinga daukar kafa tana zuwa gidan yara tana shashanci to babu shakka wannan karon zata fuskanci bacin rai daga gareta…..Tace”Kiyi hakuri kinji ko Naja’atu hakika nasan anyi miki ba dai-dai ba amma na roke ki kiyi hakuri ki kwantar kuma da hankalin ki tunda dai kin kawo min ‘karar Ramlatu da Abbas to ni kuma zan hukunta miki su saboda haka yanzu ma ba zaki koma gidan ba, har sai shi Abbas din yazo a gabanki zanyi masa fadan kan abinda yake yi ba dai-dai bane.” Naja’atu taji dadi sosai da yanda Hajiya ta goya mata baya sai kawai ta gyara zamanta a palon ta zauna suna dan ta’ba hira da hajiyar……….Abbah Abbas kullum suka taso daga kasuwa kafin su nufi gidajensu shi da Abokinsa Abba Magaji sai sun shiga kofar na’isan sun gaisa da iyayensu wataran ma a can suke sallahr magariba kafin su tafi gida, to yau ma kai tsaye da suka taso daga kasuwar kai tsaye can suka nufa………….Ganinta a zaune a kusa da hajiya ya bashi mamaki sosai! ita kuma sauri tayi ta dauke kanta tana zum’bura bakinta….Hajiya ta amsa sallamarsa ya shiga palon a nutse ya zaune kan kujerar dake fuskantar hajiyar yana gaisheta, Hajiya ta amsa kadar kadahan! tunda yaga haka sai yasha jinin jikinsa…..Ya kalli Naja’atu yana tsuke fuska yace.”Ke! wa kika tambaya kan cewar zaki zo nan.”?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button