MADADI 1-END

MADADI Page 21 to 30

Hajiya tace”Ai zamanta a gidan baida amfani tunda ka kasa ri’ke amanarta, sannan ka bawa matarka da ‘yar uwarka lasisin dukanta da zaginta gami da hanata sakat! a cikin gidan.”

Sai ya kasa gane inda maganar mahaifiyar tasa ta dosa.” Yace.”Hajiya bangane ina maganarki ta dosa ba.” Tace”Ai dama ba zaka gane ba sai na ganar da kai, to wannan yarinyar dai ‘karar ka ta kawo min kancewar kuna azabtar da ita kai da matarka sannan kuma yau Ramlatu taje har gidan ta doketa.”

Maganar ta bashi mugun mamaki! kamar shi da girmansa da shekarunsa a kawo shi ‘kara gaban iyayensa, Ya dago kansa yana kallonta sai yaga kanta na kallon wani guri sai faman zum’bura bakinta take, tunda yake da Halimatu da Halisa tsayin shekarun da sukayi a tare babu wacce ta ta’ba kawo ‘kararsa gaban iyayensa sai wannan yarinyar gaskiya ya jinjina al’amarin sosai! amma babu komai idan ma raini ne ya soma shiga tsakaninsu to dama ya dauki alkawarin yau yake so ya fitar da raini a tsakaninsa da ita.

……Hajiya ta cigaba da cewa”Wannan dalilin ne yasa nace ba zata koma gidan ba sai kazo naji ta bakin ki, shin me yasa a duk sanda Halisa zata kawo magana baka tsayawa kayi bunkice zaka hau kai ka zauna kazo kana yin abinda ya dace.”

Rashin abinda zaice ne yasa yace.”Ayi hakuri Hajiya.” 

Tace”To Dan Allah daga yau ka zama mai adalci a tsakanin matanka idan wani abu ya faru a tsakaninsu ka daina dora laifi a kan mutum daya ka dinga yin binkice tukkuna.”

Tace.”Insha Allah Hajiya to amma ni abinda ke bani mamaki anan shine har yaushe akayi auran da har za’a fara kawo ‘kara duka fa yau kwananta hud’u a gidan kuma iya bakin kokari inayi a tsakaninsu.” Hajiya tace” To nidai ga abinda tazo ta fada min kuma nasan wannan matar taka babu abinda ba zata aikata ba dan haka kaja mata kunne ita in banda abinta ai kamata yayi ta dauki naja’atu a matsayin kanwarta ba kishiyarta ba kuma itama Ramlatu zata zo ta sameni har gida, idan ta dinga zuwa gidanka tana lalata maka zamantakewar matanka to tun wuri ka taka mata burki tunda har yanzu taki tayi hankali.” Yace.”Ba zan hanata zuwa gidana ba domin suna zumunci da Halisa amma zanyi bunkice sosai kan maganar da ita Naja’atun tazo ta fad’a miki idan na tabbatar da gaske ta doke ta to ni kuma zan nuna mata rashin jin dadi na.” 

Hajiya tace”To Allah ya sa’ba halaye dama nace idan tayi sallah taci abinci sai ku tafi.” Agogon dake daure a hannunsa ya duba ya mike da fad’in “Bari na hau sama mu gaisa da Alhaji.” Kafin ma ya rufe bakinsa ya hango shi yana sakkowa daga benansa, Alhaji Sama’ila ya sauko ne d’aure da alwala da nufin zuwa massalaci, gaisawa sukayi da Abba Abbas d’in dama ita Naja’atu har dakinsa taje ta gaisheshi, ita kuwa Hajiya ‘kin fada masa abinda ke faruwa tayi saboda ba wata cikakkiyar lafiya ce dashi ba……Abbah Abbas da mahaifinsa a tare suka nufi massalaci domin gabatar da sallar magariba…

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button