MADADI 1-END

MADADI Page 21 to 30

Tura masa tayi tana adduar Allah yasa ya duba ya bata amsa…….Salim shida abokinsa suna cikin mota bayan fitowarsu daga gidan kallo ya dauko wayarsa yana dubawa, ganin Kira da text din Naja’atu yasa yaja tsaki! text din ya shiga dubawa! bayan ya gama karantawa ya nunawa abokinsa, shima ya karanta, dariya yasa ya bashi hannu suka tafa yace.”Amma gaskiya yarinyar nan na sonka da yawa, yana da kyau ka fara gudanar da aikinka dan na lura dattijon nan zulamamme ne! ya samu ‘karamar yarinya sai ‘barin jiki yake kada ka barshi ya lashi zumar nan ta dad’in rai.”

Salim yayi wani murmushi yana shafa siririn sajensa yace.”Ai wallahi sai na d’and’ana masa d’aci! da bakin cikin daya jefa ni a ciki dan haka bari kaga ni.” Sai kawai ya shiga kiran wayar Naja’atun, da sauri ta dauki wayar ta kara a kunnanta.

Salim ya wani narkar da murya cikin sigar yaudara da janye hankali a kasalance yace.”My Princess bani da lafiya zuciyata ta kusa ta daina aiki yini nayi ina aman jini! soyayyarki ina tsammanin itace ajalina! na kasa daga wayarki ne saboda ni kadai nasan irin masifar da zan shiga idan naji sautin muryarki, to amma ganin wannan text din naki na yanzu ya firgitani sosai har naji sha’awar na kira ki a waya na gargade ki kan cewar komai rintsi kada ki kuskura ki mallakawa wannan tsohon jikinki kada ki bari ya kusanci inda kike my princess ni kad’ai nasan irin yanda nake jin fleengs a duk sanda na tuno zubin hallitarki hakika na jima ina kwadayin na ganni ina tsotsar bakin ki! sannan babu babban abinda yake d’aga mun hankali kamar breast dinki na jima ina mafarki gasu a hannuna ina wasa dasu ina tsotsa ina lailayasu a hannuna! dan Allah my princess kada ki bari wani yayi amfani da damata duk rintsi duk wuya kiyi min wannan alfarmar.”

Tunda yake maganar take ‘kan’kame wayar a kunnanta tana sauke ajiyar zuciya tsigar jikinta na tashi, ji tayi gabadaya jikinta ya rikice ta dinga jin sha’awar Salim din na taso mata………..Murya a dushashe tace”My prince kada ka damu zan kula maka da kaina da jikina nayi maka alkawarin babu mai mallakata sai kai kuma insha Allahu zan fito daga gidan Abba Abbas da budurcina muyi auranmu tinda shari’a bata rahamta mana ba.”

Salim ya sakeyin ‘kasa da murya yace.”Yawwa my princess nagode kwarai da soyayyarki gareni nima insha Allahu zan cigaba da yi mana kokarin dan ganin bukatarmu ta biya.” Ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin magana, taji alamun bude kofar palon……….Da sauri ta mike ta nufi dakinsu Saddiqa da wayar a kunnanta tana magana ‘kasa-‘kasa tace”Salim gashinan ya dawo zan kashe wayar yanzu.” Yace.”To shikkenan my Prince. ” Kashe wayar yayi ya kalli abokinsa dake draving sai kawai suka kwashe da dariya kamar wasu shashashai! Kamalu yace.”Gaskiya Salim ka iya tuggu! yarinyar nan fa gabadaya ta mato a kanka duk maganar daka fada mata da sauri take amsawa kamar wani ubanta.” Salim ya shafa sajensa yana dariyar mugunta yace.”Ai na fada maka dama gangar jikinta kawai ya aura, amma zuciyarta na tafin hannuna.” Yafadi maganar yana nuna hannunsa.

Abbah Abbas ya shigo hannunsa ri’ke da ledoji guda uku, kulle kofar palon yayi kai tsaye ya nufi dakinsa a hannunsa rike da ledojin dake hannunsa…………….Jim yayi yana bin dakin da kallo sai kuma ya ajiye ledojin hannunsa kasan kafet ya nufi toilet, dan kwankwasa kofar yayi yana kiran sunanta, shurun da yaji ne yasa ya dan tura kofar toilet din yana dubawa, ganin bata ciki yasa yayi saurin fita daga dakin, kai tsaye dakinsu Saddiqa ya nufa domin yasan tana can dan babu wata hanya da zata samu ta fita daga gidan tunda kafin fitarsa sai da ya rufe kofar palon da key.

Yana shiga ya hangota kwance kusa da Mussadiq……..Ya tsaya daga bakin kofa tare da yin gyaran murya, mikewa tayi a zabure tana kallonsa, Yace.”Ya zaki zo ki takure kanki ki anan bayan kin san ko shi Mussadiq din gadon na iya yi masa kad’an.” Kasa tayi da kanta tana wasa da hannayeta, Ya juya tare da fad’in “Ki taso daga cikinsu ki dawo dakina ki kwanta ko bakiji abinda nace d’azu ba.”?

Murya na rawa tace” Abbah dan Allah ka kyaleni na kwanta a cikinsu sai nafi iya bacci. girgiza mata kansa yayi yana lumshe ido yace.”Ba zaki takurawa kowa ba ki taso kawai.”

Da sauri tace”Sai na kwanta a ‘kasan kafet babu damuwa.” Yace.”Idan baki taso ba zanzo na daukeki da kaina bana son gaddama.” Ganin yayi maganar cikin rashin wasa sai ta tsorata! da sauri ta sauko daga gadon Mussadiq ta biyo bayansa suka fita daga dakin.

Suna shiga dakinsa ya nuna mata ledojin da ya shigo dashi yace.”Ki dauki guda d’aya akwai kazar amarcinki a ciki kada nan gaba ace ana bina bashi.”

Naja’atu ta dinga kallonsa le’banta na rawa, babu shakka mutumin nan da gaske yake abinda ta fada kenan a zuciyarta……Tana kallonsa ya nufi toilet ta dinga girgiza kanta tana sake takure jikinta cikin kujera wai shin me yake shirin faruwa ne?………Ganinsa ya fito daga toilet daure da towel iya ‘kugu! faffad’an kirjinsa mai cike da yalwar gashi a waje sai yasa ‘yan hanjinta hautsinawa! cikinta ya wani murd’a mata! da mugun sauri ta sunkuyar kanta a ‘kasa! ashe haka yake da ‘kirar mazantaka gani tayi kirjinsa a cike dam! ga jikinsa a murd’e! cikinsa a shafe tamkar wanda baya cin abinci!

Karkarwa jikinta ya shiga yi gumi na yanko mata daga ko wace kusurwa ta jikinta….

*19_20*

‘Dauke kanta tayi lokacin da taga yana kokarin sanya gajeran wando, ta tsirawa ‘kasan kafet ido gabanta sai duk uku-uku yake, muryarsa taji ta dokin kunnanta inda yake cewa”Ta tashi taje tayi wanka tazo ta kwanta, ba tare da tayi kuskuran kallonsa ba ta mike salo-salo ta nufi bandakin, to koda ta shiga toilet din ma kasa yin komai tayi ta jingina jikin bango(garu) tana tunani yanzu idan Abbah Abbas yace zai kar’bi sadakinsa ya za tayi? wani irin tsoro ne ya shige ta, taji gabad’aya gwiwowinta sunyi sanyi! ita yanda ma za’ayi ta kwanta gado d’aya dashi take tunani gashi ta lura dashi sai wani abu yake yi tamkar bai damu da halin damuwar da take ciki ba…….Da kyar ta d’an sirka ruwa yayi d’umi tayi wankan, ta wanke bakinta kamar dai koda yaushe kafin ta kwanta sai tayi brush ta daura towel jikinta ya tsane tsaf sannan ta mayar da kayan jikinta ta fito, kwance ta same shi saman gado babu komai a jikinsa sai gajeran wando ga fitilar dakin a kunne! simi-simi ta nufi kan kujerar data ta bari, sunanta taji ya kira cikin ma’koshi, tsayawa tayi ba tare data juyo ba, Yace.”Ba kiyi wankan bane.”? a sanyaye tace.”Nayi.” Yace.”To cire hijabin kizo ki kwanta.” Tace.”Abbah kayi hakuri zan kwanta kan kujera.” Mikewa zaune yayi yace.”Tunda nake da Halimatu bamu ta’ba raba shimfida ba saboda haka bana so mu fara haka dake, kizo ki kwanta a makwancin ki Ni babu abinda zanyi miki.” yafada yana nuna kusa dashi.

Hawaye suka zubo mata tayi tsaye tana kallosa gami da d’umbun mamakinsa.

Ganin ta’ki zuwa yasa ya mi’ke ya nufi inda take, cikin gaggawa tayi ‘kasa da kanta dan gabadaya ji tayi ilahirin tsigar jikinta na mi’kewa sakamakon ganinsa babu kaya a jikinsa.

Yana zuwa ya ri’ke hannunta yaja ta suka nufi bed din, zaunar da ita yayi ya zauna yana kokarin cire mata hijab din jikinta, ta ri’ke hannunsa tana girgiza masa kanta bakinta sai rawa yake tana so tayi magana amma tana gudun yayi mata fad’a.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button