MADADI Page 21 to 30

Dakin su Saddiqa ta nufa koda ta shiga dakin sai ta gansu duk a kwance basu tashi ba, taji dadin hakan da sauri ta nufi toilet din dakin, ta tub’e kayan jikinta, ruwa ta hada tayi wanka kana tayi brush sai ta daura alwala ta fito…..A gurguje ta shirya ta tsaya kan Saddiqa tana tashinta, gabadayansu suka tashi tace”Ku tashi kuje kuyi alwala.”
Saddiqa ce ta fara tashi ta nufi toilet din, ita kuma ta gyara dadduma ta tayar da sallah.
Bayan ta idar da sallar kwanciya tayi kan daddumar ta takure jikinta daga zarar ta tuno da abinda ya faru a tsakaninta da Abbah Abbas sai gabanta ya yanke ya fad’i! har yanzu le’bunanta zafi suke mata idan ta tuno da yanda ya dinga shan bakinta tsigar jikinta duk sai ta mike.
Mussadiq ne yazo ya zauna kusa da ita yana gaisheta, ta mike a sanyaye tana amsawa, Saddiqa da Mufida ma suka gaisheta a nutse ta amsa musu…………’Dakin ya shigo hannunsa ri’ke da wani maidaidaicin carbi, Naja’atu tayi saurin sunkuyar da kanta ‘kasa kwata-kwata bata so ta had’a ido dashi.
Ya tsaya daga bakin kofa yana fadin “Ashe kun tashi.” Mussadiq yace.”Eh Yaya Naja’atu ce ta tashe mu.” Ya d’an kalleta da gefan idonsa, ya kauda kansa yana amsawa gaisuwar ‘yayansa, juyawa yayi zai fita yaji muryarta tana gaishe shi, ba tare da ya Juya ba ya amsa, ya bude kofar dakin ya fita.
Gabad’ayan su suka mike zasu fita tace”Ina zakuje.”? Saddiqa tace”Zamuje mu gaisa da Mommy ne.” shuru tayi tana kallonsu suka fita daga dakin..
Lokacin da suka shiga gaishe da Halisa yana tsaye a dakin suna magana, ya bisu da kallo har suka fita yana mamakin ina ita Naja’atun wato ba taji maganarsa ta jiya ba kenan? a tunaninsa zata biyo yaran suzo gaishe da Halisan tare, Inda ita kuma sam ba tayi tunanin hakaba saboda ba gaishe da Halisa ne a gabanta ba abinda ke gabanta shi ya dameta………Ya kalli Halisa a nutse yace.”To yanzu nawa kike ganin zasu isa.?
Mikewa tayi daga kan daddumar da take zaune tana kokarin cire hijabin da tayi sallah dashi tace”To ka zauna mana sai nayi maka lissafi.” Jim yayi kafin ya zauna! dan yana sane ya’ki zama a dakin saboda yasan halin da yake ciki na sha’awa baya so taja ra’ayinsa ya aikata wani abun da ita a cikin hakkin wata.
Zama tayi kusa dashi tana nanikar jikinsa, ya kalleta babu yabo babu fallasa yace.”Kiyi min bayanin nace kamar nawa ne zai isa da zaki siyo mata sutturun da suka dace.”
Fuskarsa ta shafa da hannunta ta kai bakinta kan kuncinsa ta manna masa kiss! tana me d’ora hannunta a cinyarsa, ganin irin abinda take masa ne yasa ya gane abinda take nufi! Yace.”Kin san dai ba’a cikin kwanakin ki kike ba ko.”? Marairaicewa tayi tace”Haba ai kaima kasan ba zab iya bari har sai nan da kwana shida ba wallahi, ni dai gaskiya a bukace nake.”
Kallonta ya shiga yi yana mamakin maganarta, yace.”To nima bani nake da kaina ba sai kije ki tambayi mai hakki idan ta baki aro na shikkenan.”
‘Bata rai tayi tana sake shigewa jikinsa tace”Allah ya kiyaye na tambayi yarinyar nan wani abu kaine kake da iko da kanka kuma kafi kowa sanin halin da nake shiga idan ina cikin wannan halin dan haka ni ba zan iya sauraran komai ba sai na samu biyan bukatata.” Kallonta kawai yake dan shi ya rasa ma abinda zai ce mata, yana jinta tana ta shashshafa jikinsa tana masa salo iri-iri to abinka da wanda dama yake a bukace a take ya bada kai bori ya hau, suka shiga biyawa junansu bukata…
Gabad’ayansu har ita suka fito palo suka zazzauna suna hira kar’fe takwas shuru basu ga gilmawar masu gidan ba, tara ma tayi shuru, basu fito ba, A hankali ta kalli Mussadiq tace”Ko Abbanku ya fita ne.”? Yaron ya girgiza kansa da fad’in “Wallahi ban sani ba dazu dai da muka shiga gaishe da Mommy na ganshi a dakin.”
Shuru tayi tana nazarin maganar yaron, ta kalleshi cikin sanyin jiki tace”Kana jin yunwa ko.”? Kai ya d’aga mata, mi’kewa tayi ta kalli Saddiqa da Mufida tace”Kuzo ku nuna min kicin din na had’a muku break fast.” Suka mike da sauri suna murna, tare suka shiga kicin din nan suka shiga aiki kowanne ta bashi abinda zai taimaka mata dashi…………..Halisa ta samu abinda take so sosai ta ri’ke wuta ta’ki barinsa ya huta shi kuma jinta zam-zam! ya dinga d’imautar dashi ya kasa hakura da ita suka dinga abu daya kamar jaraba koda yake dama can sun saba tunda jajayen sawun su……Sai kusan goma da rabi ya fito daga dakin, lokacin su har sunyi break dinsu suna zaune dai a palon suna hira wanda take saka musu baki jefi-jefi……Ido suka had’a ita dashi lokacin da ya fito daga dakin Halisan duk sai ya diririce! lokaci guda ta gane rashin gaskiyarsa kuma ta gane abinda suka dade sunayi a dakin, wace irin magana ce za’ace an shiga daki sama da awa uku anayi ai da akwai alamun tambaya………’Dauke kanta tayi sam bata wani ji ciwo ba dan ba wai sonsa take ba ballanta taji haushin abinda sukayi mata, cigaba tayi da dan dudduba wayarta dake hannunta, Shi kuma da sauri yake kokarin shiga dakinsa…..Mussadiq yace.”Yawwa Yaya Naja’atu ga Abban namu ya fito dama nace miki bai futa ba.”
Da sauri ta kalli yaron tana d’an hararasa! Shi kuma Abbah Abbas din tsayawa yayi yana kallon Mussadiq din yace.”Waye yazo nema na.”? Shuru tayi, Mussadiq yayi karaf yace.” ‘Dazu ne Yaya Naja’atu take tambaya ta wai ko ka fita saboda munji shuru bamu ga ka fito daga dakin ka ba shine nace mata kana dakin Mommy.”
Naja’atu taji kamar ta kwad’awa yaron mari! kada fa Ya d’auka ko sonsa take shiyasa take tambayarsa
Shi kuwa Abbah Abbas murmushi yayi yana dan shafa gemunsa ya kalleta a nutse yace.”Ina tare da Halisa muna tattauna magana mai muhimanci insha Allah anjima zakuje tare dake da ita ki za’bi irin kayan da kike so domin ita na wakilta ta had’a miki lefe.” Tsakaninsa da Allah ya fad’i maganar dan shi yana ganin meye a ciki dan Halisa ta had’a mata lefe ai duk a zaman d’aya!
Ita kuwa Naja’atu maganar ce ta girmi tunanin ta wannan ma ai rainin hankali ne da zaice Halisa ta had’a mata lefe kuma har ya iya fad’a mata da bakinsa, zuciyarta tace mata “To ke meye abin damuwa ai ba sonsa kike ballanta na dan yace Halisa ta had’a miki lefe kiji haushi!!! ” Eh duk da ba sonsa nake ba amma ai hakan bai dace ba abin kamar yazo da cin fuska a ciki, to idan ya kasance tana sonsa kuma haka zai dinga d’ora kishiyarta kan al’amuranta abinda ba zata iya jurewa ba kenan don ita ba Yaya Halimatu bace………..Dauk’e kanta tayi ba tare da tace masa komai ba, shi kuma yanayin yanda yaga ta nuna sai yaji wani farin ciki ya lullu’beshi yana addua Allah yasa yarinyar ta soma sonsa……Yana shiga daki, Ita kuma ta shiga fad’a da zuciyarta ganin kamar tana so ta takura mata gurin ganin kamar anyi mata rashin adalci a gidan zuciyarta sai ingizata take akan ta dauki mataki ta bishi daki ta tambaye shi me tsaya yayi a dakin Halisa har tsayin awa uku alhalin yasan a cikin kwanakin auranta yake, sannan kuma tace ita bata yarda Halisa ta had’a mata lefe ba!…..Allah mai iko! abinda zuciyarta keta sa’ka mata kenan duk ta kasa samun nutsuwa a gurin sai kallon kofar dakin nasa take tana tununin taje ko kada taje? Mikewa tayi ba tare da dogon nazari ba ta nufi dakin nasa har tasa hannu zata bude kofar sai kuma ta fasa, ta juya cikin sanyi jiki ta nufi dakinsu Saddiqa kwanciya tayi ruf da ciki kawai ta tsinci kanta da fashewa da kuka.