MADADI Page 21 to 30

*Tofah!???? Ko kukan me Naja’atu take? Ita da take ikirarin bata kaunar Abbah Abbas din to meye najin haushi dan ta ga ya dad’e a dakin matarsa? Lallai akwai alamun tambaya dangane da Al’amarin……………..Akwai-Akwai_Akwai!! Rikita_Rikita anan agaba! Wai shin ya zata kaya ne a tsakanin Abbah Abbas da Amaryarsa? Shin zai samu nasarar kar’bar budurcinta ko kuwa? Salim zai kyale Naja’atu tayi rayuwar aure da Mijinta Kuwa? Wane Babban kuskure Naja’atu zata tafka anan gaba? Meye makomar Yaya Ramlatu da Halisa? akwai sauran labari anan gaba!!!! Ga duk wanda yake da ikon biyan kudin littafin nan ya biya ya karanta #300 ko #600 basu isa su biya kudin littafin nan ba???? Koda yake ai ‘KARYA ce amma dai ni nasan ‘karyar tawa tana Tasiri a wani gurin dan haka da kai da ke ina so duk ku biyo ni domin a cigaba da tafiyar daku Single #300 Vip #600 Babu tsada???? Kada ki nuna ganin ‘kyashin biyan kudi ki karanta kice bari ki bari idan an sato ki kiranta Allah ya isa! Idan anyi magana kice kema gani kikayi an turo shiyasa kika karanta, to duk wanda ya’ki sharar massalaci zaiyi ta kasuwa!????*
*Masu had’a min decoment na books daga zarar na gama bazan ce komai ba sai dai na ro’ki Allah ya tattara muku zunuban da na d’auka gurin rubuta littafin ya d’ora muku a kanku????Shikkenan sai a raba mana zunubin tare daku kun rage min nauyi.*
*Masu tambayar wai ni bana littafin free ne sai na kudi: Amsa To farkon littafina Nana Khadija Free ne zagi da ‘korafi gami da rashin hakuri irin na redars yasa na mayar dashi na kudi, tun daga haka shikkenan na daina littafin kyauta amma akwai book dina RUWAN DARE free ne book1 yana nan yana yawo a groups ga duk mai bukatar karantawa sai ya tambaya a groups insha Allah idan na gama rubuta littafin MADADI zab cigaba da typing d’insa RUWAN DARE free ne bana kudi bane! idan na gama Madadi zan cigaba da rubuta muku shi????*
*Masoya masu sahihiyar kauna Ina alfahari daku♥️*
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D’IN DA ZA’A TURA KUDIN…….0542382124…..BINTA UMAR GTBANK…..IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR……07084653262…..IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS………90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
Mdd
*21*
Halisa kuwa bayan fitar maigidan daga dakin, cikin farin ciki ta d auki wayarta ta shiga kiran Yaya Ramlatu, duk ta shaida mata abinda ke faruwa, ta fada mata cewar maigidan ya bada kud’i kimanin dubu dari biyu yace wai a siyawa amaryarsa kayan lefe masu kyau sannan yace ma idan basu isa ba ta fada masa. Yaya Ramlatu taja tsaki! tace”Ko dubu dari ba za’a kashe mata ba gurin had’o lefen komai ‘kananu za’a siya mata dan haka idan kin tashi tafiya kasuwar ki biyo ta gidana mu tafi tare.” Halisa tace”Eh to da cewa yayi wai muje tare da yarinyar ta duba abinda takeso.” Yaya Ramlatu tace”Ki san dubarar da zaki masa ki fito ke kad’ai meye wani dole sai anje da ita.” Halisa tace”Zan nuna masa yarinyar ta zauna ta kula da yara insha Allah za’a siyo mata komai mai inganci.” Yaya Ramlatu tace”To ke kuma nawa ya baki kudin naki kayan.” ? Murmushi tayi tace.”Nima dubu dari biyu ya bani kamar nata kuma yau da daddare yace zai shigo min da mukkulin sabuwar motata.” Yaya Ramlatu ta rangad’a bud’a tace”To Alhamdullhi babu shakka kwalliya ta soma biyan kudin sabulu dan haka idan zaki zo kada ki manta da al’kawarinmu dake.”
Halisa na dariya tace”Haba Yaya Ramlatu ai ‘Yar halak ce ni insha Allah zan kawo miki.” Cikin farin ciki Yaya Ramlatu tace”To Allah ya ‘kara mallaka miki mijinki a hannuki.” Halisa ta amsa da amin tana cike da farin ciki ganin ta kowane ‘bangare tana samun biyan bukata……..Cikin shararriyar kwalliya ta fito palon ta samu yaran suna zaune a palo suna kallo, ba tare da tace musu komai ba ta nufi dakin maigidan, shima lokacin yana kokarin fitowa cikin shirin fita, ganin uwar kwalliyar da taci tana kamshin turare sai ya ‘bata fuska yace.”Keda zaki shiga kasuwa kuma meye nayin kwalliya harda shafa turare.” Tayi fari da ido kamar yanda ta saba idan za tayi masa magana tace”Wallahi shaf na manta ban fad’a maka ba yau ne bikin sunan ‘Yar yayata data haihu a unguwar Gaida to inaso in fara zuwa can kafin naje kasuwar.” Yace.”Anya kuwa sai dai ki za’bi d’aya dan idan kin tafi suna da zuwa kasuwa lokaci zai ‘kure baki dawo gida ba.” Da sauri tace”Shine ai nace mai zai hana ita Naja’atun ta zauna ta kula da yaran tunda amarya ce bai kamata ace daga zuwanta ta fara yawo ba insha Allah zamuje tare dasu Shamsiyya zan siyo mata komai mai kyau wanda ake yayi.” Yana gyara zaman hularsa a kansa yace.”Wannan shawarar taki tayi kyau dan gabadaya banyi tunanin hakan ba okey muje sai na ajiye ki a gidan bikin.”
Farin ciki ya cika mata zuciya, ta juya tana wata irin tafiya irin ta manyan mata.
Tsakiyar palon ya tsaya yana kallonsu, ya kalli Mussadiq da fadin”Ina Yaya Naja’atu.”? Yaron yace.”Tund’azu data shiga daki bata fito ba mybe bacci take.” Ba tare da yace komai ba ya nufi dakin yaran.
Ruf da ciki ya sameta bayan ta gama kukanta bacci ne ya dauketa a haka. Ya tsaya kanta yana k’are mata kallo………..Halin da ya shiga lokacin da yake kiss d’inta jiya kawai yake tunowa yarinyar nada wani sirri na mussaman a tare da ita. Hannu yasa ya dan shafi gefan fuskarta yana kiran sunanta
Ta bud’e idonta wanda kuka da bacci ya mai dasu wani iri! shi kuwa ai ji yayi tsigar jikinsa ta tashi ganin yanda idanunta suka jirkice kamar wacce take ciki sha’awa.
Gyaran murya yayi kamar yanda ya saba ya sake kiran sunanta.
Mikewa zaune tayi tana goge fuskarsa had’e da d’an zum’bura baki ta’ki kallon inda yake tsaye. Yace.”Za mu fita tare da Halisa zaki zauna tare da yara kafin ta dawo da nace zakuje tare domin ki duba abinda kike so sai kuma yanzu take ce min zata je bikin suna ina ganin ke sai ki zauna tare da yaran a gida kafin Allah yasa ta dawo.” Fuskarta ta goge tana kallon kasan gadon da take zaune tace”Nifa Abba daka bar kudinka bana son wani lefe kayan da nake dasu ma sun isheni.”
Cikin d’an mamaki yace.”Saboda me? ai hakkinki ne dole nayi miki tunda inada iko.” Kamar ta fad’a masa mara dad’i sai dai tayi shuru tana d’auke kanta, tayi al’kawarin ko an siyo kayan ba za tayi amfani dasu ba.
Agogon dake daure a hannunsa ya dan kalla sha biyu shaura na rana ya nufi kofar fita yana fad’in “Sai mun dawo ki kula da kanki da yara.” Wani irin kallo ta bishi dashi har ya fita daga dakin taja tsaki mai karfi ta koma ta kwanta.
Halisa a bakin titi tasa ya ajiyeta tace ya sauketa zata shiga da ‘kafa, nan ya ‘kara jaddada mata cewar kada ta kai dare tayi ta gama duk abinda za tayi ta koma gida da wuri. ta amsa masa kamar gaske tana d’aga masa hannu
Tana ganin motarsa ta wuce ta tari a daidaita sahu ta shiga kai tsaye unguwar gwangwanxo ta nufa, dama tun kafin taje ta shaidawa Ramlatu gata nan a kan hanya dan haka a shirye ta tarar da ita ba kuma tare da ‘bata lokaci ba suka dauki hanyar gidan ‘Yar Sa’adu! koda suka isa gidan cike yake da manyan mata masuji da kansu, kamar dai koda yaushe ‘Yar sa’adu na zaune kan kujerarta mata sun kewaye ta suna ta d’aga magungunan mata suna dubawa ita kuma tana musu ‘karin bayani a kan maganin, ‘Yar Sa’adu na ganin su Halisa ta rangwada guda ta gyara zamanta tana dariya ta kalli Halisa da fad’in “Kaga Uwargidan Alhaji Abbas Lallai tunda naga kina kyallin goshi akwai magana ai dama nace sai kin dawo da kafafunki.” Halisa ta bata hannu suka tafa suna kyalkyala dariya! suka zazzauna suna gaisawa da juna.