MADADI Page 21 to 30

‘Yar Sa’adu tace” Aikuwa kun taki sa’a dan jiya aka kawo min kaya daga Zindar gasu nan masu kyau ne sosai sai da kudi?” Yaya Ramlatu ta d’aga wata madaidaiciyar roba wacce take cike da wani abu shi ba black ba browan ba.” ‘Yar Sa’adu tace”Wannan maganin dake hannunki sunansa sai maigida Ihu!! da kuwwa! idan kika mallaki maganin nan kin wuce takaici wallahi duk abinda kikace yayi miki sai yayi miki.”
Da sauri Halisa ta kar’bi maganin tana dubawa! dariya tasa tace “Lallai maganin nan za’aje dashi koga yanayin hoton dake jikinsa, Namiji da mace ne tsirara suna sex wani irin style mai ban mamaki! budewa tayi ta d’an dangwalo maganin a hannunta ta lasa! taji wani za’ki!! fauuu! a bakinta, tsigar jikinta sai da ta tashi ta rintse idonta.
‘Yar Sa’adu ta bawa ta kusa da ita hannu suka tafa! tana dariya tace” ‘Yar gari taji sabon abu a bakinta ai nake fad’a miki Halisa yanda kikaji za’kin maganin nan haka kema zaki dinga za’ki da dad’i mutukar kina amfani dashi, kuma amfanin maganin nada yawa dan yana ‘kara karfin sha’awa sosai idan ma mijinki baida karfi yana saurin kawowa to wallahi karfin wannan maganin sai ya mayar dashi tamkar ayu kullum yana ma’kale dake.
Halisa tace”A’a ni mijina baida wannan matsalar sai dai na siya dan biyan bukatar kaina dan haka yanzu nawa ne maganin.”?
‘Yar sa’adu ta gyara zamanta tana ‘kas-‘kas da cingum din bakinta tace”Dubu dari ne kacal amma tunda ke costomar ce ki bada dubu casa’in da biyar na cire miki dubu biyar.” Yaya Ramlatu tace”Haba dai ‘Yar Sa’adu ki sake yi mata ragi kin san fa yanda garin yake kuma kinga komai tsadar magani Halisa bata ta’ba gandar siya kuma kin san idan taji dadinsa in ya kare zata dawo ta siyi wani.”
‘Yar Sa’adu ta kalli ta kusa da ita tana ‘bata rai tace”Hajiya Mairo dan Allah nawa na siyarwa da matan da suka fita yanzu wannan maganin.”?
Hajiya Mairo tace”Dubu dari ashirin.”! ‘Yar Sa’adu ta kalli Halisa tace”Kinji dai da kunnanki dubu dari da ashirin na siyar dashi amma ke nace ki bada dubu casa’in da biyar kina neman ragi.”? Halisa tayi shuru tana nazari gabadaya kudin data fito dasu dubu dari biyu da hamsin ne har kudin kayan lefan Naja’atu kuma a ciki ta dauki dubu dari ta bawa Yaya Ramlatu dama tun kafin su fito sun gama yanke shawarar dubu dari kacal zasu kashe gurin had’awa Naja’at lefe, yanzu abinda ya rage a hannunta dubu ar’bain da takwas ne tunda sunyi kudin mota da sauran.
Ta kalli Yaya Ramlatu tace”Ina ganin kudin kayan yarinyar nan zan bada dan gaskiya bazan bari maganin nan ya wuce ni ba.”
Yaya Ramlatu tace”To kin tanadi abinda zaki fad’a masa idan kin koma gida.”? Murmushi tayi tace.”Sosai kuwa ni nasan karyar da zanyi masa. Yaya Ramlatu tace”Tom shikkenan.” Halisa ta zuge zif din jakarta ta fito da kudi ta shiga lissafawa……….
Bayan fitar masu gidan Naja’atu ta dan dauki lokaci a dakin a kwance tana tunane tunanen mafita a gareta gabadaya ta rasa wane mataki zata dauka, ta kira wayar Salim sau curin masaki yaki dagawa, sai da taci kukanta ta koshi sannan ta fito palon a lokacin da Saddiqa take kokarin shiga dakin domun ta tambayeta abunda zasu dora na abincin rana……Ganin yanda idanun antina nata sukayi fululu yasa jikinta yayi sanyi ta kalleta a sanyaye tace”Dan Allah Yaya Naja’atu ki daina kuka da damuwa ki kwantar da hankalinki wallahi Abbanmu zai kula dake ki daina damuwa.”
Dan kauda kanta tayi cikin kokarin bagarar da maganarta tace”Waye ya fada miki kuka nake bacci nayi fa shiyasa idona yayi ja.” Saddiqa dai ba yarinya bace ballanta ta dauki maganarta sai dai kawai ta bar maganar a yanda ta fada tace”To shikkenan dama shigowa nayi na tambaye ki me zai mu d’ora na abinci.”? kai tsaye tace “Muje kicin din sai muyi aikin tare.” Kai tsaye kicin din suka nufa tare.
Mussadiq ne ya shigo kicin din hannunsa rike da wayarta yana fadin “Yaya Naja’atu Abbanmu na kiran wayarki.” Goge hannunta tayi ta kar’bi wayar tana dubawa, miss call dinsa ta gani, ajiye wayar tayi ta cigaba da aikinta.
Kimanin minti biyar da fitar Mussadiq daga kicin din wani kiran ya sake shigowa kamar bata so ta daga wayar, Yayi mata sallama ta amsa ciki-ciki Yace.”Ya gida ina fatan babu matsala.”? “Umm.” Tace Yayi shuru na minti biyu kafin yace.”Ina fatan kunci abinci.” nan ma bata bashi cikakkiyar amsa ba. Ranshi ya ‘baci yace.”Ki bude baki kiyi min magana meye wani umm! Tace”Gashi muna girkawa.” Yace.”To haka nake so ki gaishe min da yaran sai na dawo.” Shuru tayi masa yana kashe wayar ta ajiye tare da jan ‘karamin tsaki! da sauri Saddiqa ta kalleta sai kuma tayi saurin dauke kanta ta cigaba da aikin dake gabanta sam ba taji dadin tsakin da akayi wa Abbanta nata ba kawai dai tayi shuru ne dan bata da yanda za tayi.
To Halisa da Yaya Ramlatu a gidan ‘Yar Sa’adu suka lalace! sai bayan la’asar suka bar gidan kai tsaye suka nufi kasuwar dubai ta jakara, nan suka shiga katin dan jummai suka shiga siyan atampopi da lesuna masu saukin kudi suka je gurin masu undar wear suka siyi masu saukin kudi takalma da jaka guda uku ‘yan dubu daya da dari biyar sai mayafai hudu masu sharara da saurin lalacewa, kayan make up marasa kyau da ar’ha suka siya, Gabadaya basu kashe dubu saba’in ba gurin siyayyar ana shirye-shiryen kiran sallahr magariba suka fito daga kasuwar.
Abbah Abbas tun misalin shida na yamma ya dawo gida, lokacin Naja’atu da Saddiqa sun gama komai hatta da abincin dare sun shirya tsaf koda ya dawo yaga gidan nashi tsaf yaran ma tsaf tsaf sai farin ciki ya kamashi dama ko lokacin Halimatu haka d’abi’ar su take kafin ya dawo gida sun gama komai zai dawo ya ga komai cikin kyau da tsari, sai dai kuma koda ya duba Halisa yaga bata dawo ba sai ranshi ya ‘baci sosai! ya fito daga dakin nata da waya a hannunsa, lokacin ita kuma hayaniyar abubuwan hawa tasa ta kasa jin kiran da yake mata a waya…..Cikin ‘bacin rai ya shige dakinsa domin daura alwalar sallar magariba.
Har yaje massalaci ya dawo Halisa bata shigo gidan ba, fitowa yayi daga cikin gidan ya tsaya a harabar gidan yana sake kiran wayarta a rayuwarsa ya tsani matarsa tayi dare a waje…..Lokacin da yake kiran wayar a lokacin mai adaidata ya sauketa ita da kayan data siyo, ta dan bubbuga gate din gidan maigadi ya bude mata, ganinta yasa da sauri ya bude karamar kofa ta fito ya dinga daukar kayan yana shiga dasu cikin gidan, shi kuwa Abbah Abbas jin tace masa gata nan shigowa yasa ya kashe wayarsa ya tsaya a gurin yana jiran shigowarta, Halisa ganin yanda fuskarsa take a murtuke yasa gabanta ya fad’i! a take ta shiga marairace fuska! ta bude baki za tayi masa magana kawai ya rufe ta da fad’a! takaici ya cika mata zuciya a gaban maigadi yake niyyar tozarta ta kawai sai ta wuce shi ta nufi cikin gidan, aikuwa hakan ya fusata shi! ya bi bayanta ciki nan ya sake rufeta da fad’a a gaban yara! duk suka mi’ke tsaye! suna kallonsu, Halisa duk kunya ta isheta ta kalli maigadi dake ajiye ledojin kayan data siyo tace ya fita! shima da sauri ya fice yana mamaki! ashe haka ubangidan nasa yake da masifa.
Ita kuwa Naja’atu dariya ne kawai ba tayi ba ta dinga kallon Halisa tana rantse-rantse da kokarin kare kanta shi kuma ya’ki sauraranta sai da ya gama fad’ansa sannan ya bar gurin a fusace!! Halisa bayan barinsa gurin ta shiga rarraba idanunta a palon kawai sai taga yaran sun zuba mata ido har da wacce ta tsana a idonta ma sai taga kamar yarinyar dariya take…..Cikin tsawa! tace”Dan ubanku kallon me kuke min? munafukan yara kawai.”! Da sauri suka shiga fad’in “Mommy sannu da zuwa.” Ko kallonsu ba tayi ba ta watsawa Naja’atu harara! fuuuu ta wuce dakinta kamar zuciyarta zata tsage! babu shakka dole ta taka masa burki a gidan dan ba zata yarda ya dinga ci mata mutunci a gaban yara ba…..Naja’atu kuwa dariyar dake damunta ce ta su’bce mata sai tayi ‘kasa da kanta tanayi tana d’an duba wayarta ta yini cikin takaici amma wannan abun da ya faru ya wanke mata zuciyarta