MADADI Page 21 to 30

*Na ‘Dan samu sukuni nayi Typing duk da bashi da tsayi sosai Vip gruop afuwa idan baku samu da daddare ba kuyi hakuri dan Allah kuyi min adduar Allah ya bani ishashshiyar lafiya insha Allahu na warware sosai zaku samu yanda kuke so kamar yanda nayi muku al’kawari Nagode*
*Littafin na kudi ne. Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kinaso ki biya ki karanta ga yanda abin yake*
Vip Gruop #600
Normal Gruop#300
Accont: 0542382124..Binta Umar Gtbank Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan numbar….07084653262
*BINTA UMAR ABBALE*
BHRBN
*22*
Halisa na shiga d’akinta ta shiga band’aki a gurguje tayi wanka ta fito daure da alwala sallah tayi ba tare da tayi doguwar addua ba ta mike daga kan daddumar ta fito palo tana muzurai…….Naja’atu na ganinta tayi kasa da kanta dariya na nema ta kufce mata, ashe ta ganta tana ‘kunshe dariya kawai sai ta shiga cusa mata ashar dama zagi bayayiwa Halisa wahala kamar ‘yar maguzawa haka take, Tana kumfar baki gami da hayaniya tace”Mahaukaciya ni da zaki dinga yi min dariya?me kika gani na dariya a jikina? Naja’atu tace”Allah ya baki hakuri ni wallahi bake nakewa dariya ba ina hira da friend dina ne a waya! ‘Kwafa tayi ta girgiza kanta da fad’in “Zan gyara miki zama a gidan nan dan ni ba’sarki bace ballanta na ki raina ni.” Shuru palon yayi babu wanda yayi magana, Halisa cikin tsawa! da masifa ta kalli Saddiqa tace”Ina fatan kun girka abinda zakuci dan cikin ku babu wanda zanyi wa wani girki a yanzu dan na gaji.”
Saddiqa tace”Eh Mommy munyi abinci Yaya Naja’atu ce ma tayi.” Tsaki taja tace”To ku taso ku dauko wad’ancan kayan ku kaisu dakin Abbanku.” Da sauri suka mike suka shiga kwasar ledojin kayan data siyo, sai da suka gama shiga da kayan dakin sannan ta shiga ta same shi zaune a kan Sofa da Loptop a kan cinyarsa
Jikinta a sanyaye ta zauna kusa dashi, tunda taga fuskarsa a murtuke tasan har yanzu bai huce ba.
Tace”Wallahi tsautsayi ne ya ritsani dani a maimakon ka fara tambayar dalilin da yasa nayi dare kawai sai ka rufe ni da masifa a gaban maigadi da yar…….Hannu ya d’aga mata tun kafin ta karasa maganar yace.”Tunda dai ni ban isa na fad’a miki magana kiji ba to kije zan dauki mataki a kanki kin sani sarai na tsani kuje unguwa kuyi dare a waje ki fita tun safe ba zaki shigo gidanki ba sai bayan sallahr isha’i mai kikeyi a waje sai kace namiji.”
“Dan Allah kayi hakuri wallahi ba haka naso ba na fada maka tsautsayi ne ya ritsa dani a gidan bikin da naje wasu mata da ba’asan daga ina suke ba suka shigo gidan to kasan abinka da taro babu wanda ya damu dasu aka cigaba da harkoki dasu ashe ‘barayi ne, na ajiye jakata kan gadon Maijego na tafi nayi alwala kawai na dawo na tarar da zif din jakar a bude sun kwashe rabin kudin daka bani nayi wa yarinyar nan siyayya.” Cikin rawar murya ta ‘karashe maganar tana goge hawaye.
Daina duba Loptop din yayi ya tsaya kawai yana kallonta. sai ta sake fashewa da kuka ta cigaba da cewa “Wallahi sama da ‘kasa aka neme su aka rasa, sai daga sannan kowa ya farga ya fara duba jakarsa ashe bani kadai sukayi wa sata ba har da wasu amma dai tawa tafi muni.”
Shuru yayi yana nazarin maganarta jikinsa na bashi anya kuwa da gaske take? ganin yanda take kuka duk ta koma kalar tausayi yasa ya amince da maganarta yace.”To yanxu a’ina kika samu kudin da kikayi wannan siyayyar bayan kince an sace.”
Tana goge fuska tace”Ai ba duka suka kwashe ba sun bar min dubu cas’in da biyu shine bayan mun gama jajantawa junanmu na dauki Shamsiyya ta rakani muje kasuwar Dubai ta jakara na siyo mata atampa guda biyar les uku mayafai uku jaka da takalma uku sai undis da kayan make up, ajiyar zuciya ya sauke yace.”Allah ya ‘kara kiyayewa daga yanzu sai ki san da wanda zaki dinga zama a cikin taro kuma ki kiyaye ajiye jakarki a’koina.”
Hawaye ta goge tana sake ‘kas’kantar da kanta kamar gaske tace”Insha Allah na kuma gode daka fahimce ni yana da kyau kuma ka duba kayan.” Yace.”Kada ki damu zan duba idan na gama abinda nake.” Yafada hankalinsa na kan loptop din cinyarsa……..Halisa ganin yana aiki yasa ta mike ta fita daga dakin zuciyarta wasai taji dadi da karyarta ta samu gurbi a zuciyarsa…..ko kunya babu ta zauna a gurun cin abinci ta cika cikinta da girkin Naja’atu mai dadi da gamsawarsa, ta mike ta nufi dakinta domin ta kira Yaya Ramlatu a waya ta fada mata yanda sukayi da maigidan.
Mussadiq ya kalli Naja’atu da hankalinta gabadaya yake kan wayarta, yace.”Yaya Naja’atu gobe ne za’a koma makaranta ko.”? A nutse ta kalleshi tace”Eh mana ai kunsha hutu sosai gobe kowa da kowa zai koma.” Mufida tace”Wallahi bana son a koma makarantar nan mutum ya tafi tun safe sai yamma akwai gajiya.”
Tana ‘yar dariya tace”Mufida in banda abinki waye kika ga ya ta’ba gajiya da neman ilimi ai kudi da ilimi mutum har ya mutu nemansu yake.” a dan sanyaye yarinyar tace”Hakane kuma anti.”
Naja’atu ta cigaba da charting d’inta tana murmushi Salim ne yake kashe mata jiki da hirarar soyayya! voice note ya turo mata, ta mike ta nufi dakinsu Saddiqa dan tana jin tsoro ta bud’e a gabansu suji tasan Mussadiq da bin’kwakw’kwafi ita kuma Saddiqa da kishin Ubanta.
Ruf da ciki ta kwanta ta bude voice note din muryasa mai kashe mata jiki taji yana cewa”My Princess ina fatan kin wuni cikin koshin lafiya kuma ina fatan baki manta da al’kawarinmu dake ba.”
Itama gyara muryar ta tayi ta amsa masa da cewar tana nan lafiya kuma al’kawarin da tayi masa yana nan insha Allahu shine zai mallaki komai nata…..Salim yaji dadi sosai da amsar data bashi kawai sai ya sake gyara kwanciya a katifarsa ya shiga sakar mata zantukan batsa! masu muni! abin ya dinga bata mamaki da kunya dan tunda suke da Salim bai ta’ba yi mata irin wannan zantukan ba sai yanzu! Duk ya kashe mata jiki tana so tace ya daina ta kasa fad’a masa, kawai idan ya turo mata voice note din sai ta bude ta saurara tana lumshe idonta! wani idan ta bude kasa hakuri take sai ta bashi amsa! haka ta dinta mutsu-mutsu a kan bed din tsigar jikinta na tashi, sai ta dinga jin wani irin Feeling na taso mata……Abubuwan da Abba Abbas yayi mata a daran jiya su ta dinga tunawa tana sake jin maganganun da Salim din keyi mata na sake tasiri a ranta da gangar jikinta.
Shigowar yaran ce tasa tayi saurin mi’kewa zaune tana dan daidaita yanayin ta, a sanyaye ta kalle Mussadiq tace”Zaka kwanta a gadon ka.”? Yaron yace.”Eh amma ki kwanta Ni sai na kwanta a kasan kafet. A sanyaye tace”Nagode Mussadiq.” Saddiqa ta kalleta tace”Yaya Naja’atu ya naganki wani iri ko baki da lafiya.”?
Da sauri ta shafa fuskarta tana kauda kanta daga kan Saddiqar tace”Me kika gani lafiya ta lau bacci ne ya fara daukana.” Saddiqa tace”Ayya. juyawa tayi ta shiga dauko kayan baccinsu. ita kuma Naja’atun ta mi’ke simi-simi ta nufi toilet, tsayawa tayi a toilet din gabanta sai faduwa yake, hakika zantukan da Salim yayi mata sun masifar tayar mata da hankali gabadaya ma ji tayi ta rasa abinda ke damunta, jikinta babu kuzari tayi wanka ta fito da kayan jikinta har yanzu tana jin feeling na damunta
Mussadiq ne ya mika mata riga da wando cotton yace.”Yaya Naja’atu gashi na dauki miki kayan baccin ki.” Kar’ba tayi ta zauna gefan gadon tana fadin “Nagode Musaadiq ku kwanta domin ku tashi da wuri.”